Tinubu ya sauke shugabar Jami’ar Abuja, ya yi sauye-sauye a jami’o’in Najeriya
Published: 6th, February 2025 GMT
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauke Aisha Maikudi daga muƙaminta na Shugabar Jami’ar Abuja, wadda yanzu ake kira da Jami’ar Yakubu Gowon.
Sanarwar sauke Maikudi ta fito ne jim kaɗan bayan ta jagoranci bikin maraba da sabbin ɗalibai a jami’ar.
Uwa ta fusata ta jefa ’yarta cikin kogi a Bayelsa HOTUNA: Yadda gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a KanoTun farko, naɗinta ya jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu malaman jami’ar suka ce ba ta cancanta ta riƙe wannan matsayi bisa doka.
Tinubu ya naɗa Farfesa Lar Patricia Manko a matsayin Muƙaddashiyar Shugabar Jami’ar na tsawon watanni shida.
Sai dai ba za ta iya neman kujerar dindindin ba idan aka buɗe damar neman muƙamin.
Cikakken bayani na tafe…
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jami ar Abuja Jami ar Yakubu Gowon Kora
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Tinubu Ya Yaba Da Gudunmawar Da IBB Ya Bayar Yayin Mulkinsa
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) bisa irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban Najeriya.
Shugaban kasar a bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da tallafin, tarihin rayuwar Janar Babangida da gwagwarmayarsa yayin aiki, wanda aka gudanar a Abuja.
A yayin da yake jawabi a matsayin babban bako na musamman, Tinubu ya bayyana ga irin jagoranci Babangida a yayin mulkinsa, wanda ya ce ya abin koyi ne ga kowa.
Ya kuma yaba da rawar da IBB ya taka wajen kafa sabbin bankuna na zamani, wanda ya kawo kyakkyawa sauyi a fannin hada-hadar kudi na Najeriya.
Tinubu ya kuma yabawa manufofin Babangida da salon shugabancinsa da suka yi tasiri a nasa salon siyasar, inda ya jaddada kokarin Babangida wajen inganta dimokuradiyya da kawo sauyi a tattalin arziki.
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, wanda ya gabatar da jawabi mai ma’ana, ya yabawa Babangida bisa rubuta tarihin rayuwarsa da irin gudunmawar da ya bayar a tarihin Najeriya.
Obasanjo ya jaddada mahimmancin adana bayanan tarihi don taimakawa al’umma masu zuwa, domin gano kura-kurai da suka gabata, da yadda za a gyara, da kuma taimako wajen gina kasa.
A wani muhimmin jawabi, tsohon shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya yaba da shugabancin Babangida a Najeriya, inda ya jinjina gudunmawar da ya bayar wajen tabbatar da dimokuradiyya a yammacin Afirka.
Kazalika shi ma tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya tuna irin jajircewa da Babangida ya nuna a lokacin da yake aikin soja.
Ya lura da biyayyar Babangida da kokarin daidaita gwamnatin Najeriya a lokacin yunkurin juyin mulki da sauran kalubalen siyasa.
A nasa jawabin, tsohon mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi nazari mai zurfi game da littafin, inda ya yaba da abin da ya kunsa, da kuma yadda Babangida ya karrama wadanda suka yi aiki tare da shi.
A nasa jawabin, Babangida ya bayyana godiya ga dukkan wadanda suka halarci taron da suka hada da gwamnoni, da sanatoci, da sarakunan gargajiya, da wakilan kamfanoni masu zaman kansu.
Ya yi waiwaye kan kalubale da sadaukarwar da aka yi a lokacin gwamnatinsa, ya kuma bayyana irin matsalolin da al’ummar Najeriya ke fuskanta.
Babangida ya fito karara ya yi magana kan soke zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 12 ga watan Yunin 1993, inda ya dauki cikakken alhakin wannan mataki.
Ya bayyana cewa an dauki dukkan matakan ne da domin gujewa tashin hankali, da kuma tabbatar da zaman lafiyar Najeriya.
Duk da cece-kucen da ake yi, Babangida ya jaddada cewa tsarin dimokuradiyya ya ci gaba da wanzuwa, wanda ya sa Najeriya ta samu ci gaba a dimokuradiyya.
An kammala taron ne da kaddamar da dakin karatu na Ibrahim Badamasi Babangida na fadar shugaban kasa, inda baki da dama suka bayar da gudunmawa domin tallafawa aikin.
Daga Bello Wakili