Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa
Published: 6th, February 2025 GMT
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci nan na Jihar Kaduna, Sheikh Ishaq Yunus Almadany, ya rasu bayan fama da rashin lafiya.
Ya rasu a ranar Alhamis a Asibitin 44 Army Reference da ke Kaduna.
An tsinci gawar Ɗan Majalisar da aka yi garkuwa a jajibirin Kirsimeti Tinubu ya sauke shugabar Jami’ar Abuja, ya yi sauye-sauye a jami’o’in NajeriyaJami’in hulɗa da jama’a na na kafafen sada zumunta na ƙungiyar Izalatul Bidia Waikamatus Sunnah (JIBWIS), Ibrahim Shehu Giwa ne, ya tabbatar da rasuwar.
Shugaban JIBWIS reshen Jihar Kaduna, Alhaji Adamu Ibrahim, ya bayyana alhininsa, tare da yin addu’ar Allah Ya gafarta masa Ya kuma Aljanna makomarsa.
Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, shi ma ya sanar da rasuwar malamin a shafinsu na Facebook, inda suka yi addu’ar Allah Ya jiƙansa.
Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5 na yamma a filin idi na Sultan Bello, da ke Kaduna.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Rashin lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Kwamandan IRGC Ya Bayyana Cewa: Amurka Da Isra’ila Ba Su Yi Nasara A Yakin Gaza Ba
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Amurka da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ba su yi nasara a yakin da suka kaddamar kan ‘yan gwagwarmaya a Gaza ba
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta samu wanzuwa idan babu Amurka, yana mai cewa, ita kanta Amurka ta kama hanyar rugujewa. Ya kara da cewa: Wadannan al’amura suna faruwa ne a kasa kuma wani bangare ne na makomar al’umma, don haka wajibi ne al’umma su dogara ga Allah kuma su yi duk abin da za su iya.
A yayin ganawarsa da Ziyad al-Nakhala babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami, Manjo Janar Salami ya yi nuni da irin nasarorin da dakarun gwagwarmayar Falastinawa da al’ummar Gaza suka samu a kan yahudawan sahyoniya ‘yan mamaya, yana mai bayyana wannan nasara a matsayin nasara da take a fili kuma nasara ce bayyananniya ta Ubangiji” wacce ta kawo abin alfahari ga duniyar Musulunci, yayin da Allah ya girmama Falastinawa da nasara bayan tsawon shekaru ana killace da su saboda matakan zalunci.
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa: Zafin zalunci da wahalhalun da al’ummar Falastinu suke sha yana damun kowa a cikin zukata duk jurewa hakan yana da wahala da wuya, amma al’umma tana godiya ga Allah kasancewa wadannan al’amura sun kare da nasarar da jarumai a Gaza suka samu.