Xi Jinping Zai Halarci Bikin Kaddamar Da Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Lokacin Hunturu Ta Kasashen Asiya Karo Na 9 A Harbin
Published: 6th, February 2025 GMT
Xi Jinping Zai Halarci Bikin Kaddamar Da Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Lokacin Hunturu Ta Kasashen Asiya Karo Na 9 A Harbin.
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi : Ya kamata Duniyar Musulmi ta dauki mataki mai karfi kan Isra’ila
Ministan harkokin wajen kasar Iran, Abbas Araghchi, ya yi kakkausar suka kan zaluncin da gwamnatin Isra’ila ke yi kan al’ummar Falasdinu da ba su da kariya a yankin Zirin Gaza, yana mai jaddada bukatar hadin kai da daukar matakin gaggawa na kasashen musulmi domin dakile wadannan laifuka.
Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan a ranar Asabar, inda ya bukaci kasashen musulmi a duk fadin duniya da su dauki kwararen matakai da hadin kai don tunkarar ta’addancin Isra’ila.
Araghchi ya yi nuni da yadda gwamnatin Isra’ila ta sake dawo da yakin da take yi na kisan kare dangi a kan Gaza tun ranar Talatar data gabata wanda ya keta yarjejeniyar tsagaita bude wutar da aka cimma a zirin.
Sabon farmakin Isra’ila ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 1,000, akasari mata da yara, baya ga kusan mutane 48,000 da sojojin suka yi wa kisan kare dangi tun da farko.
A wani bangare na jawabin nasa, Araghchi ya yi tir da hare-haren wuce gona da iri da Amurka da Birtaniya ke yi kan kasar Yemen, inda ya bayyana irin asarar da aka yi a tsakanin mata da kananan yara da ba su ji ba ba su gani ba, da kuma lalata kayayyakin more rayuwa na kasar.
Ya jaddada nauyin daya rataya a wuyan al’ummar musulmin duniya na tallafa wa ‘yan uwansu a wannan kasa ta Larabawa mai fama da tashe-tashen hankula da talauci.
A nasa bangaren, Yarima Farhan ya nanata matsayar Riyadh na yin Allah wadai da mummunan zaluncin gwamnatin Isra’ila, Ya kuma jaddada wajabcin hada kai da hadin gwiwa a tsakanin kasashen yankin don hana barkewar rikicin.