‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Tsohon Darakta Janar Na Hukumar NYSC
Published: 6th, February 2025 GMT
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina inda suka yi garkuwa da tsohon Darakta Janar na Hukumar Kula da Matasa masu yi wa kasa hidima NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da wasu mutum takwas.
Majiya mai tushe ta bayyana hakan ga gidan rediyon Najeriya a wata hira da manema labarai, yayin da ‘yan sanda ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.
Wani shaidan gani da ido ya bayyana yadda gungun ‘yan bindigan suka afkawa al’ummar a kan babura da misalin karfe sha biyu na dare.
“Da misalin karfe 12 na dare ne ‘yan bindigar suka shigo garin na tsiga a bisa babura, inda suka rika harbi a sararin samaniya, sannan suka nufi gidajen da suka kai hari.”
“Kimanin mutum goma daga cikin ‘yan bindigar ne suka kai farmaki gidan Birgediya Janar Maharazu Tsiga, yayin da ssauran suka bazama wasu gidajen, inda suka tasa keyar mutum takwas.” inji shi.
Wakilinmu ya ruwaito cewa ‘yan bindiga sun sha kai wa al’ummar Tsiga hari a cikin shekaru bakwai da suka wuce.
Daga Isma’il Adamu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Dubban Falasdinawa Sun Kauracewa Gidajensu A Dai-Dai Lokacinta Sojojin HKI Suke Fafatawa Da Dakarun Falasdinawa
Dubban Falasdinawa ne suka kauracewa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan. Tun ranar 21 ga watan Jeneru na wannan shekara ta 2025, wato kwanaki biyu kacal da tsaida wuta a Gaza, sojojin HKI suka fadawa sansanin yan gudun hijira na Jenen inda suka fara fafatawa da dakarun Falasdinawa a yankin. Da nufin korarsu.
Dagan nan ne dubban Falasdinawa suka fara kauracewa gidajensu a yankin. Wasu suka dauki dukkan iyalansu su a mota su tafi inda ba’a tashin hankali. Wasu kuma sukan taka da kafafuwansu zuwa nesa daga inda ake fada da tashin hankali.
Wani dan agaji a yankin ya bayyana wa Jaridar ‘Arabsnews’ cewa bai taba ganin irin wannan kaurar da Falasdinawa suke yi ba, sai wanda aka yi a yakin 1967 inda falasdinawa 300,000 suka kauracewa gidajensu, sai kuma kafin haka a shekara ta 1948 falasdinawa 700,000 ne, sojojin yahudawan suka tilastawa falasdinawa kauracewa yankunansu a kasarsu da aka mamaye.