Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kara kudirin kasafin kudin shekarar 2025 daga naira tiriliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2, yayin da majalisar dokokin kasar ke kokarin ganin an zartar da shi kafin karshen wata.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da karin kasafin ta hanyar wasiku daban-daban da shugaba Tinubu ya aikewa majalisar dattawa da ta wakilai.

A cikin wasikar da aka karanta yayin zaman majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya ce an sami  karin kudin ne sakamakon karin kudaden shigar da hukumar tara haraji ta kasa FIRS ta samu na Naira tiriliyan 1.4, yayin da hukumar hana fasakwabri  ta kasa ta tara Naira tiriliyan 1.2, da kuma Naira tiriliyan 1.8 da wasu hukumomin gwamnati suka tara.

A don haka shugaban majalisar ya mika bukatar ga kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa domin tantancewa cikin gaggawa, inda ya tabbatar da cewa za a kammala nazarin kasafin kudin kafin karshen wata.

Daga Bashir Meyere

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Naira tiriliyan

এছাড়াও পড়ুন:

‘Tell Your Papa’: NBC ta haramta amfani da waƙar da ke sukar Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta haramta amfani da wata sabuwar waƙar da ke sukar Shugaba Bola Tinubu a dukkanin kafofin labarai na rediyo da talabijin a faɗin ƙasar.

Waƙar da mawaƙi Eedris Abdulkareem ya fitar a baya-bayan nan mai suna“ Tell Your Papa”, ta soki yadda Shugaba Tinubu ke gudanar da tattalin arzikin Nijeriyar.

An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da mayaƙa 100 a Katsina An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano

The lyrics are addressed to Tinubu’s son, calling on him to let his father know “people are dying” from economic hardship as well as continued insecurity from armed groups.

Baitocin waƙar da ke ɗauke da kira ga ɗan shugaban ƙasar, Seyi Tinubu, sun buƙaci ya isar wa mahaifinsa saƙon cewa ’yan Nijeriya na fama da matsanancin ƙunci na tattalin arziki da kuma matsalar tsaro.

Sai dai Hukumar Kula da Kafafen Watsa Labarai a Najeriya NBC, ta shaida wa kafofin labaran ƙasar cewa waƙar ta saɓa ƙa’ida da ma taɓa “mutuncin gwamnati.”

Tuni dai mawaƙi, Eedris Abdulkarim, ya mayar da martani, inda ya buƙaci magoya bayansa su saurari waƙar ta hanyoyin da kafar Intanet ta bayar da dama.

Abdulkareem ya wallafa a shafinsa na zumunta cewa, faɗa wa gwamnati gaskiya ko sukar gyara kayanka a kullum laifi ne a Nijeriya.

Shekaru biyu na mulkin Bola Tinubu a ƙasar dai sun gamu da zanga-zanga musamman kan tsadar rayuwa da man fetur.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ci Gaba Da Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Tinubu ya kaddamar da aikin sake gyaran titin Abuja zuwa Kano
  • Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya
  • Badaƙalar Miyagun Ƙwayoyi: Kotun Amurka ta ba da umarnin fitar da bayanai kan binciken Tinubu
  • ’Yan adawa sun zama kyanwar Lami duk da rinjayensu a Majalisa
  • Isra’ila ta yi barazanar fadada hare-hare Gaza yayin da ta yanke Rafah daga birnin Khan Yunis
  • ‘Tell Your Papa’: NBC ta haramta amfani da waƙar da ke sukar Tinubu
  • Sin Ta Yi Allah-wadai Da Karin Harajin Amurka Ta Kuma Jaddada Goyon Bayanta Ga Ka’idojin WTO 
  • Sin Za Ta Kara Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar Zuwa 125%
  • Basukan Da Nijeriya Ke Biya Sun Karu Zuwa Naira Tiriliyan 13