Iran : ‘’Falasdinu Ta Al’ummar Falasdinu ce” Jagora
Published: 6th, February 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa : Gabadayen Falastinu tun daga kogi har zuwa teku ta al’ummar Falasdinawa ce.
Jagoran ya jaddada goyon bayan Iran ne ga gwagwarmayar Falasdinawa kan kasarsu mai dimbin tarihi, tun daga kogin Jordan zuwa tekun Bahar Rum, kamar shafin offishin jagoran ya sanar.
Kallaman Jagoran na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da wata shawara mai cike da cece-kuce na kaurar da Falasdinawa daga zirin Gaza da kuma sanya Amurka ta karbe yankin da yaki ya lalata.
Ta hanyar yada wannan sako a cikin harsuna da dama, Iran ta nanata kudurinta na tabbatar da Falasdinu.
Shugaba Trump na Amurka ya tsaya kai da fata cewa “kowa na kaunar” shirinsa na Amurka ta kwace zirin Gaza.
Ya fadi hakan duk da irin watsi da suka da bayyana shirin nasa da al’ummar Falasdinawa da shugabannin Gabas ta Tsakiya da gwamnatocin kasashen duniya suka yi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Yana Son Ganin Bayan Shugaban Kasar Ukraine Volodimir Zelezky Daga Kujerar Shugabancin Kasarsa
A dai-dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana a fili kan cewa baya son nganin tokwaransa na kasar Ukraine Volodimir Zelesky kan kujerar shugabancin kasarsa. Al-amura suna kara tabarbarewa a Kiev.
Jaridar Economist ta kasar Burtaniya ta bayyana cewa al-amarin ya bayyana kiri-kiri ne a lokacinda shugaban kasar Amurka ya zanta ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimi Putin. Sannan aka gudanar da taro na farko tsakanin Amurka da Rasha a birnin riyad na kasar Saudiya ba tare da an gayyaci Zelesky ba haka ma, babu wani Jami’in tarayyar Turai da aka gayyata.
Jaridar ta nakalto wani babban jami’in gwamnati a Kiev yana cewa tun lokacinda suka fahinci cewa Trump baya son a ci gaba da yaki a Ukraine, sannan baya son shugaba Zeleski sun san haka zai faru.
Banda haka, Trump ya bayyana cewa Amurka ta kashe dalar Amurka miliyon 360 kan yakin da ta tabbatar da cewa Ukrain ba zata sami nasara ba. Banda wannan ya ji ta bakin Zeleski kansa kan cewa an sace rabin kudaden da Amurka ta bata. A halin yanzu dai Trump ya bukaci a gudanar da zabe a kasar Ukraine, don ya tabbatar da cewa Zelesky bai da magoya baya da yawa. A cikin watan Fabrairun da mukr ciki ne yaki tsakanin Ukraine da Rasha yake cika shekaru 3 da fara shi.