Aminiya:
2025-02-22@06:41:24 GMT

Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya

Published: 6th, February 2025 GMT

Kwamitin Sake Duba Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na Majalisar Wakilai, ya bayar da shawarar ƙirƙiro sabbin jihohi 31 domin ƙara yawan jihohin ƙasar nan daga 36 zuwa 67.

Shugaban kwamitin, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Benjamin Okezie Kalu ne, ya bayyana hakan yayin zaman majalisar da ya jagoranta a ranar Alhamis.

Malamai sun fara yajin aiki a Ebonyi  Tinubu ya yi sauye-sauye a Jami’ar Abuja

Daga cikin sabbin jihohin da aka bayar da shawarar ƙirƙirar su, akwai Benue Ala, Okun, Okura, Confluence, Apa-Agba, Apa da Abuja, waɗanda za a samar daga jihohin Benuwe da Kogi, tare da babban Birnin Tarayya.

A Arewa Maso Gabas, an bayar da shawarar ƙirƙiro jihohin Amana daga Jihar Adamawa, Katagum daga Bauchi, Savannah daga Borno, da Muri daga Taraba.

A Arewa Maso Yamma, akwai jihohin New Kaduna da Gurara daga Kaduna, Tiga da Ghari daga Kano, da kuma Kainji daga Kebbi.

A Kudu Maso Gabas kuwa, akwai jihohin Etiti, Urashi, Orlu, Aba da Adada, waɗanda za su fito daga yankin gaba ɗaya.

A yankin Kudu Maso Kudu, ana son ƙirƙiro jihohin Ogoja daga Kuros Riba, Warri daga Delta, Bori daga Ribas, da Obolo daga Ribas da Akwa Ibom.

A Kudu Maso Yamma, an tsara sabbin jihohin Toru-Ebe daga Delta, Edo da Ondo, Ibadan daga Oyo, Lagoon daga Legas, Ijebu daga Ogun, Oke-Ogun daga Ogun, Oyo da Osun, da Ife-Ijesha daga Ogun, Oyo da Osun.

Idan wannan shawara ta samu amincewa, Najeriya za ta ƙara yawan jihohinta daga 36 zuwa 67.

Ana kyautata zaton lamarin zai kawo sauyi mafi girma a tsarin gudanarwar Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Adamawa Ghari Majalisar Wakilan Najeriya Taraba

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Gombe ta horar da makiyaya kan sabbin hanyoyin kiwo

Gwamnatin Jihar Gombe ta horar da makiyaya 684, ciki har da nakasassu, mata, matasa, da tsofaffin ma’aikata, kan sabbin dabarun kiwon awaki da kasuwancinsu.

Wannan horo ya gudana ne ƙarƙashin shirin Livestock Productivity and Resilience Support (L-PRES).

Rigima ta sake kaurewa tsakanin PDP da APC a Zamfara Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno

Kwamishinan Aikin Gona, Kiwo, da Hada-hadar Ƙungiyoyi na Jihar Gombe, Dokta Barnabas Malle ne, ya jagoranci ƙaddamar da horon a Gombe.

Yayin da yake jawabi, ya jaddada ƙudirin gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na inganta kiwon dabbobi da tallafa wa al’umma.

Ya ce: “Shirin ya dace da manufofin gwamnati na bai wa kowa damar cin gajiyar shirye-shiryen da ake gudanarwa.”

Shugaban shirin L-PRES na Gombe, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya bayyana cewa horon zai taimaka wa makiyaya wajen ƙara ƙwarewa da haɓaka kiwon awaki.

Ya ce: “Mun mayar da hankali kan makiyaya saboda muhimmiyar rawar da suke takawa wajen samar da awaki a tsakanin al’ummarmu.

“Manufarmu ita ce ƙara musu ƙwarin gwiwa da ƙwarewa don su inganta rayuwarsu.”

Farfesa Abubakar, ya ƙara da cewa buƙatar naman awaki a duniya na ƙaruwa, don haka Gombe na da shirin kafa cibiyar kiwon awaki ta zamani da kuma babbar kasuwa ta yanka dabbobi a Najeriya.

A yayin horon, an koyar da mahalarta yadda ake:

Zabar nau’in awaki masu inganci Ciyarwa mai kyau Rigakafin cututtuka Inganta muhalli don kiwo

Dabarun kasuwanci da sarrafa kayayyakin da ake samu daga awaki

Shugaban Ƙungiyar Masu Nakasassu ta Jihar Gombe, Ja’o Sarkin Aiki, ya yaba wa gwamnatin bisa wannan horo

“Wannan horo zai taimaka mana wajen bunƙasa kiwonmu da kuma dogaro da kanmu don samun ingantacciyar rayuwa.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Dauki Nauyin Dalibai 80 Da Ke Manyan Makarantu
  • Tsarin Fansho Na Jihar Jigawa Ya Yi Wa Sauran Jihohi Zarra- Premium Pension
  • Jami’an Diblomasiyya Daga Kungiyar G20 Da Dama Sun Isa Afrika Ta Kudu
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa
  • NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC
  • Majalisa ta fara bincike kan zargin USAID na tallafa wa Boko Haram
  • IRGC Ta Kaddamar Da Sabbin Makamai A Atisayen Da Take Yi A Halin Yanzu
  • NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano
  • Gwamnatin Gombe ta horar da makiyaya kan sabbin hanyoyin kiwo
  • Gwamnatin Niger Ta Hana Yan Najeriya Dauke Da Passpor Ta Na ECOWAS Shiga Kasar