ICC Na Neman Shaidu Kan Ta’asar Da Aka Aikata A Gabashin DR Congo
Published: 6th, February 2025 GMT
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya na neman shaidu kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Matakin zai shafi irin ta’asar da aka aikata daga ranar 1 ga watan Janairun 2022 zuwa yau, bisa la’akari da tashe-tashen hankula da aka yi a makonnin baya-bayan nan musamman a birnin Goma – babban birnin lardin Kivu ta Arewa.
Kotun ta ICC ta ce an jikkata dubban mutane tare da kashe daruruwan mutane a birnin Goma da kewaye.
Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su har da fararen hula da dakarun wanzar da zaman lafiya, bayan shafe tsawon watanni ana gwabza fada tsakanin sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da kungiyar M23 da kawayenta.
Ofishin mai gabatar da kara ya yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, da shaidu, da kungiyoyin kasa da kasa, kungiyoyin farar hula, da su bayar da duk wata shaida da ke hannunsu, dangane da zargin laifukan da dukkan bangarorin suka aikata.
A nata bangaren, DRC tana shirin gabatar da kudiri ga kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya a wannan Juma’a a birnin Geneva na kasar Switzerland, na neman a gudanar da bincike kan abin da ta kira “gaggarumin take hakkin dan Adam” a birnin Goma.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Malaysia: An Bude Kiran Yanke Sayen Kere-kere Kamfanin “Tesla” Na Elon Musk
A kasar Malaysia an bude yin kira da a yanke kere-keren kamfanin Elon Musk saboda goyon bayan da yake nuna wa Donald Trump da siyasarsa ta son korar Falasdinawa daga Gaza.
Mutanen kasar ta Malaysia ne suke amfani da kafofin sadarwa na al’umma wajen yin kira da a yanke mu’amala da motocin da kamfanin na Telsa take kerawa saboda kusancinsa da shugaban kasar Amurka Donlad Trump wanda yake son ya tilastawa Falasdinawa daga Gaza zuwa wasu kasashe na daban.