Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta ce ta mikawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON kudaden aikin hajjin maniyyatan jihar  na shekarar 2025 kimanin naira biliyan 4.5.

Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar.

Ya ce hukumar ta aika wa NAHCON Naira Biliyan Huda da Miliyan Dari Biyar da Ashirin (4.

520), a yayin da take sa ran za ta kara biyan wasu kudaden kafin cikar wa’adin da NAHCON din ta bayar.

Ya bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta baiwa jihar kujeru 1,809.

A cewarsa, tuni hukumar ta raba kashi 40 cikin 100 ga kananan hukumomin jihar domin gudanar da aikin hajjin bana.

Don haka Labbo ya bukaci Maniyyatan jihar da su gaggauta kammala biyan kudinsu kafin wa’adin da NAHCON ta bayyana, saboda rashin yin haka na iya sa su rasa kujerunsu.

Ya kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba hukumar za ta fara gudanar da taron bita ga maniyyata a cibiyoyin da wasu Malamai suka kebe domin alhazan jihar.

Yayin da yake tsokaci kan masaukin Alhazai, Labbo ya ce  hukumar ta samar da masauki na alfarma kusa da Masallacin Harami da ke birnin Makkah, domin alhazan jihar su sami damar gudanar da ayyukansu cikin sauki.

Don haka ya bukaci maniyyatan  da su ci gaba da bai wa hukumar hadin kai domin cimma burin da ake so.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, tun ffarko da hukumar ta sanar da sama da miliyan 8.4 a matsayin kudin aikin Hajjin shekarar 2025 ga maniyyatan jihar.

Shugaban hukumar ya bayyana cewar sun yi taro da jami’an hukumar na shiyoyi, wanda  aka gudanar a dakin taro na hukumar da ke Dutse.

Ya yaba da irin goyon baya da kuma kyakkyawar alakar aiki da ake samu a tsakanin mahukuntan hukumar da ko’odinetocin, inda ya yi addu’ar samun dauwamammen hadin gwiwa domin amfanin kowa da kowa da kuma ci gaban jihar.

Ya kuma  bayyana cewar sun yi taro da jami’an hukumar na shiyoyi, wanda  aka gudanar a dakin taro na hukumar da ke Dutse.

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Hukumar Alhazai Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara

Hukumar da take kula da hakkin bil’adama ta MDD ta bayyana cewa; Mafi yawancin wadanda yaki ya rutsa da su a Gaza mata ne da kananan yara.

Mai Magana da yawun hukumar ta kare hakkin bil’adama ta MDD Rafina Shamdsani ce ta bayyana hakan a wurin taron hukumar da aka yi a birnin Geneva tana mai kara da cewa; Atsakanin watan Maris zuwa Aprilu na wannan shekara ta 20205 da ake ciki kadan, Isra’ila ta kai hare-hare har sau 224 akan gidajen mutane da kuma hemomin da ‘yan hijira suke ciki.

Har ila yau, hukumar ta kara da cewa; suna ci gaba gudanar da bincike akan wasu hare-hare 36 da sojojin Isra’ilan su ka kai da aka tabbatar da ya ci rayukan mutane da dama da su ka hada mata da kananan yara.

A nata gefen, kungiyar agaji ta “Red- Cross” ta yi gargadin cewa, kayan aikin da ake da su a cikin asibitocin da ake da su a cikin yankin sun kusa karewa.

Haka nan kuma kungiyar ta ce; ” A cikin yankuna da dama na Gaza, ba a iya samun ruwan sha, babu abinci, kuma babu wutar lantarki.

Ita kuwa ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza, ta yi kiran gaggawa domin a shigar da kayan aiki a cikin asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya. Haka nan kuma ta kara da cewa, da akwai masu fama da ciwon suga 80,000 sai masu hawan jini 110,000 ba su samun kula yadda ya dace.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babban Daraktan Hukumar IAEA, Zai Ziyarci Iran ranar Laraba
  • Hukumar OCHA Ta Bayyana Cewa Yahudawan Sahyoniyya Sun Ninninka Ayyukan Korar Falasdinawa A Yamma Da Kogin Jordan
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Siyo Tan Tan 360 Ga Manoma
  • An kama kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
  • An kama miyagun kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
  • Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
  • Za A Samar Da Ababen Hawa Ga Malaman Sakandare A Jigawa
  • MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
  • Shugaban Hukumar Makamashin Nukliya Ta Kasar Iran Ya Ce Dukka Ayyukan Makamashin Nukliya A Cikin Gida Suna Tafiya Da Karfinsu
  • Basukan Da Nijeriya Ke Biya Sun Karu Zuwa Naira Tiriliyan 13