Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Cewa Kasarsa Bata Neman Yaki Sannan Bata Nemam Mallakar Makaman Nukliya.
Published: 7th, February 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa juyin juya halin musulunci a nan Iran ya zo ne da sakon zaman lafiya ga dukkan kasashen duniuya, don haka ne ta haramtawa kanta mallakan makaman nukliya wanda yake kissan kare dangi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Alhamis a taron da jakadun kasashen waje da manya-manya baki suka halatta a gidan shugaban kasa a nan Tehran.
Sannan ya ce JMI bata amince da samuwar yan ta’adda a ko ina ba, kuma kasar Iran tana daga cikin kasashe wadanda suka fi cutuwa da ayyukan ta’addanci a duniya.
Sannan daga karshen shugaban ya kammala da cewa tsarin harkokin wajen kasar Iran ya tafi ne a kan abota zaman lafiya da kuma mu’amala da juna cikin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Al-Huthi Ya Ce Kawo Wani Jirgin Ruwa Mai Daukar Jiragen Saman Yaki Gazawa Ce Ga Amurka
Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin halin da ake ciki a yakin da sojojin kasarsa suke fafatawa da gwamnatin kasar Amurka. Ya kuma kara da cewa jiragen yakin ruwa na kasar Amurka sun zama matsala ga gwamnatin Amurka maimakon su taimaka mata.
Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata aiko da jirgin ruwan yaki mai suna USS Carl Vession zuwa tekun Maliya don karfafa USS Harry Truman a yakin da take fafatawa da sojojin kasar Yemen.
Shugaban kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa sojojin kasar Yemen zasu ci gaba da abinda suka sa a gaba na maida martini kan jiragen yakin Amurka a tekun Red Sea da kuma dukkan jiragen HKI ko wadanda suke zuwa can don tallafawa mutanen Gaza.
Shugaban kasar Amurka donal Trump dai ya sha alwashin shefe kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen daga Doron kasa.