HausaTv:
2025-03-25@17:53:18 GMT

Babban Kwamandan IRGC Ya ce ‘Bama Sunkuyawa Ko Ga Duk Wata Barazana Ga Kasa’

Published: 7th, February 2025 GMT

Babban kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran Burgediya Janar  Hussain Salami ya bayyana cewa a dai dai lokacinda manya-manyan kasashen duniya suke amfani da takunkuman tattalin arziki, mafi muni a kan wasu kasashe, a lokacin ne kuma, dakarun IRGC  suke yunkuri don kare kammu daga makiya. Sannan samar da ci gaban da muke bukata don kawukammiu daga cikin gida.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Salami yana fadar haka a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa, JMI ta na samun ci gaba duk tare da matsin lambar da ta take ciki. Kuma zata kara karfin sojojinta, don kare kanta daga duk wata kasa wacce teka barazana ga cibiyoyon Nukliyar kasar ko kuma tana son ta maida kasar mu baya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

 Jam’iyyar “Turkish National Party” Ta Tsaid Imam Uglu A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa

Jami’iyyar adawa ta “Turkish National Party” ta bayyana cewa dan takararta a zaben shugaban kasa na 2028 shi ne magajin garin Istanbul Akram Imam Ugulu wanda a halin yanzu yake a gidan kurkuku.

Imam Uglu dan shekara 53 shi ne muhimmin dan takarar shugaban kasa a tsakanin ‘yan hamayya da ake hasashen cewa  zai iya bugawa da shugaba Rajab Tayyib Urdugan a zabe mai zuwa.

‘Yan jam’iyyar ta adawa sun kada kuri’ar tsayar da Imam Ugulu a matsayin dan takararsu a zabe mai zuwa, inda ya sami kuri’u miliyan 1.6 a tsakanin miliyan 1.7.

Shugaban jam’iyyar ta “National Party” Uzgur Uzil wanda ya sanar da hakan, ya kuma bayyana cewa an yi zabe na gwaji da miliyoyin mutane su ka zabi Imam a matsayin shugaban kasa.

Kasar Turkiya ta fada cikin dambaruwar siyasa ne bayan da aka kama ‘yan hamayyar siyasa kusan 100 da aka zarga da cin hanci da rashawa, da kuma taimakawa ta’addanci. Daga cikin wadanda aka kama da akwai Akram Imam Uglu wanda shi ne magajin garin Istanbul.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Ceto ‘Yan Nijeriya Sama Da 950 Daga Gidajen Yari A Libya – Gwamnati
  • Za mu ɗauko hayar sojojin ƙetare domin horas da dakarun Nijeriya — Badaru
  • An Ɗauko Sojoji Daga Waje Don Horas Da Dakarun Nijeriya 
  • An Ɗauko Sojoji Daga Wajen Don Horas Da Dakarun Nijeriya 
  •  Jam’iyyar “Turkish National Party” Ta Tsaid Imam Uglu A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa
  • Wajibcin Gina Al’ummar Duniya Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya
  • Iran ta yi gargadin cewa keta hurumin Lebanon da Isra’ila ke yi barazana ne ga zaman lafiyar duniya
  • Wata mata ta haifi jaririn da ba nata ba
  • Iran ta yi Allah-wadai da harin ta’addanci da aka kai a wani masallaci a kudu maso yammacin Nijar
  • Sudan: Sojoji na ci gaba karbe mahimman gine-gine a birnin Khartoum