Yadda Jami’an Tsaro Suka Fara Gyara Wa ‘Yan Jari Bola Zama A Abuja…
Published: 7th, February 2025 GMT
Obuah ya ce, makasudin yin bayanin shi ne don tabbatar da cewa masu aiki da doka ne kawai ke aiki a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma yaki da matsalar masu varna a yankin.
Ya ci gaba da cewa, wani samame da ‘yansanda suka kai a wasu kasuwannin Pantaker a baya-bayan nan ya yi nasarar kwato dukiyar al’umma da aka sace da suka kai sama da Naira biliyan daya.
“Saboda haka, Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, tare da jami’an tsaro, ta bayar da umarnin cewa duk wani ma’aikacin pantaker dole ne a yi rajista da kuma bayyana sunansa. Wannan zai ba mu damar gano masu aiki na gaske kuma mu fahimci ayyukan kasuwancinsu.
“Haka zalika za a bukaci masu gudanar da aikin su rike rajistar masu saye da masu kaya. Muna bukatar mu san su wanene masu samar muku da kaya kuma wa kuke sayarwa. Samun wannan bayanin zai taimaka a kokarinmu na tsaro,” Obuah ya kara da cewa.
Ya shawarci masu sana’ar pantaker da su guji yin mu’amala da wasu mutane ba bisa ka’ida ba ko sayen kayan sata, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da irin wannan kayan zai fuskanci kamawa tare da gurfanar da shi gaban kuliya.
Obuah ya kuma kara karfafa gwiwar ma’aikatan da su hada kai a karkashin wata kungiya domin samar da ingantaccen hadin gwiwa da gwamnati da hukumomin tsaro.
Daraktan Sashen Tsaro na Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, Adamu Gwary, ya jaddada cewa masu sana’ar sayar Jari Bola ne kawai da aka sani za a yi musu bayani kuma a ba su izinin sake bude kasuwancinsu.
Ya umurci duk ma’aikatan da ba su yi rijista ba da su bi tsarin tantancewa kafin su ci gaba da aiki.
Da yake mayar da martani, Shugaban Masu Sana’ar Pantaker Operators na Kasa, Alhaji Abbas Bello, ya bayyana kudirin ma’aikatan na tallafa wa kokarin da suke yi na inganta sana’o’insu.
Ya yarda cewa akwai masu aikata laifuka a cikinsu kuma ya yi maraba da shirin a matsayin hanyar kawar da su.
Sakataren Kungiyar Malam Salisu Abubakar ya tabbatar da shirinsu na hada kai da jami’an tsaro domin yakar wannan varna a Babban Birnin Tarayya Abuja
কীওয়ার্ড: Tsaro Babban Birnin Tarayya Abuja
এছাড়াও পড়ুন:
Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia
A ranar Juma’a aka rantsar da sabuwar shugabar ƙasar Namibia, Netumbo Nandi-Ndaitwah domin jagorantar ƙasar wadda aka ruwaito na fuskantar ƙalubale na rashin aikin yi da talauci.
Kasancewar Netumbo Nandi-Ndaitwah mace ta biyu da aka taɓa zaɓa a matsayin shugabar ƙasa a nahiyar Afirka, kuma ta farko a Namibia na iya fuskantar ƙalubale.
Bam ya kashe mutum 4 da jikkata wasu a Borno Gobara ta kashe ɗan shekara 7 a sansanin ’yan gudun hijira“Idan komai ya tafi daidai, wannan zai zama kyakkyawan misali,” kamar yadda Netumbo Nandi Ndaitwah ta shaida wa shirin Podcast na BBC Africa. “Amma idan wani abu ya faru, kamar yadda zai iya faruwa ga kowace gwamnati ko da a ƙarƙashin namiji ne, akwai waɗanda za su ce: ‘saboda ni mace ce!'”
Sabuwar shugabar, mai shekara 72 a duniya ta lashe zaɓen qasar ne a watan Nuwamba inda ta lashe kashi 58% na ƙuri’un da aka kaɗa.
Nandi-Ndaitwah ta kasance daɗaɗɗiyar ƴar jam’iyyar South West Africa People’s Organisation (Swapo) – wadda take kan mulki tun lokacin da ƙasar ta samu ƴancin kai a shekarar 1990, bayan kwashe tsawon lokaci tana fafutukar ƙwatar kanta daga Afirka ta Kudu mai fama da mulkin wariya.