Kwara ta kammala horar da kwararrun ma’aikatan gona 1,000
Published: 7th, February 2025 GMT
Akalla manoma da ma’aikatan gona 1,000 ne gwamnatin jihar Kwara ta horas da su akan aikin gona da sarrafa ragowar amfanin gona don inganta amfanin gonakin da makiyaya ke amfani da su.
Da yake jawabi a karshen horon, a Ilorin, wanda Synergy Impact Limited ya shirya, tare da tallafin gwamnatin tarayya, bankin duniya da kuma shirin gwamnatin jihar Kwara akan kiyo da noma (L-PRES) kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Yakubu Danladi ya bayyana cewa shirin yana da karfin inganta ayyukan noma a jihar.
Kakakin majalisar wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin noma na majalisar, Issa Gideon, ya bayyana cewa shirin ya kara wa dimbin matasa kwarin gwiwa da jami’an noma da manoma wajen samar da kananan manaoma da sarrafa abincin dabbobi.
Ya godewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin jihar bisa bullo da shirin na L-PRES cewa aikin ya kara habaka noma a jihar.
Danladi, ya ce mahalarta taron, wadanda suka fito daga dukkan kananan hukumomin jihar 16, za su inganta harkar noma da kiwo a jihar da ma kasa baki daya.
Ya kuma bukaci mahalarta taron da su yi amfani da ilimin da aka samu a lokacin shirin, inda ya ce mutane na bukatar amfanin gona da kiwo a matsayin tushen arziki.
Dan majalisar ya ce samar da kananan dabbobin da matasa ke yi zai iya zama tushen gina tattalin arzikin kasar.
Ya kuma shawarci mahalarta taron da su kirkiro kayan aikin noma da injuna da aka samar musu a lokacin shirin horaswa a yankunansu daban-daban.
A nasa bangaren, shirin na jihar, Soji Oyawoye, ya bayyana fatansa cewa ilimi, kwarewa da kwarin gwiwa da mahalarta taron suka samu zai taimaka musu wajen aiwatar da ayyukan noma a yankunansu.
Ya kuma bukaci wadanda aka horas da su ma su horasda wasu akan wannan fasahar da suka samu ga manoma abokan aiki.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara mahalarta taron
এছাড়াও পড়ুন:
Ban bai wa majalisa haƙuri ba — Natasha
Sanata mai wakilatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta musanta batun da ake yaɗawa cewa ta bai wa Majalisar Dattawa haƙuri.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Natasha ta ce tana na kan batunta, kuma ba za ta taɓa bai wa majalisar haƙuri a kan gaskiyarta ba.
Fursunoni 12 sun tsere bayan fasa gidan yari a Kogi Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — ZulumIdan za a tuna dai majalisar ta dakatar da Natasha tsawon watanni shida tare da dakatar da albashi da alawus-alawus ɗinta ne bisa saɓa wa dokokin majalisar da kwamitin ƙorafi da ladabtarwa ya tabbatar.
Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kuma Sanata Natasha take ci gaba da zargin shugaban majalisar, Godswil Akpabio, da cin zarafinta.
Daga bisani kuma Natasha ta shigar da koken nata a Majalisar Ɗinkin Duniya.
“Zan ci gaba da yaƙi domin ƙwato ‘yancin matan Najeriya har sai ranar da aka fara sauraronmu. Yunƙurin da ake yi domin rufe bakina ba na wasa ba ne, amma ko a jikina.
“Gaskiyar wasan kwaikwayon da ake yi akan idon ‘yan Najeriya za ta bayyana watarana, sannan duk ‘yan rashawar da suka mamaye gwamnatin za su yi bayani dalla-dalla,” in ji Natasha.
“Don haka ina kira gare ku, da ku yi watsi da da duk wani rahoto da kuka ci karo da shi cewa na bai wa majalisa haƙuri, domin ba gaskiya ba ne.
“Ina na kan batuna, kuma zan ci gaba da yaƙi a kan gaskiyata duk rintsi duk wuya.
To sai dai Natasha na wannan maganar ne a daidai lokacin da hukumar zaɓe ta kasa ke bayyana cewa ta samu takardar neman yi wa ‘yar majalisar kiranye daga mazabarta.
Sakatariyar hukumar Rose Oriarana-Anthony ce ta bayyana hakan inda ta ce takardar ta iske ta ne a ranar Litinin.