Rikicin Uba Sani Da El-Rufa’i Ya Dauki Sabon Salo
Published: 7th, February 2025 GMT
Gwamna Sani ya bayyana zargin da kungiyar ta yi a matsayin maras tushe, yana mai jaddada cewa “Mafi yawan ‘yan siyasar da ke irin wadannan kalamai na iya zama suna magana da kansu ne kawai,” in ji shi. “Mun kasance a cikin jam’iyya daya a wani lokaci, kuma dole ne in ce na yi mamakin abin da suka yi.
Ya kara da cewa kawancen ba shi da wata hujjoji ta gaskiya kan ikirarin nasu.
“Fito da zarge-zarge ba tare da hujja ba, wani yunkuri ne kawai na kawar da hankulan ‘yan Nijeriya,” in ji gwamnan.
“Yawancin wadannan ‘yan siyasa sun rike mukamai a gwamnati kasa da shekaru biyu da suka gabata. Me suka yi a lokacin da suke kan mulki?”
Ya nuna shakku kan sahihancinsu, yana mai nuni da cewa yakinsu sun yi ne kawai a lokacin suna kan mulki.
“Yan Najeriya suna fa fahimta, kuma sun riga sun san wadannan ’yan siyasa ba wai suna fada da Tinubu ba ne saboda sun fi shi sanin abin da ya fi dacewa da su, a’a sun samu dama a baya amma me suka yi?
Gwamna Sani ya kara da cewa a kwanakin baya wasu ‘yan siyasa sun yaba wa Shugaba Tinubu amma sun canja ra’ayinsu bayan barin gwamnati.
“Mafi yawansu suna zaune a teburi daya da mu, suna yakar Tinubu saboda mun yi imanin cewa shi ne mutumin da ya fi dacewa ya ciyar da kasar nan gaba,” in ji shi. “Mene ne shaidar dimokuradiyya, idan zan iya tambaya? Me suka yi domin ciyar da dimokuradiyya gaba a Nijeriya?” Ya tambaya.
A martanin da El-Rufai ya mayar a shafinsa na D, ya caccaki gwamnan, yana mai cewa, “Mutanen Jihar Kaduna za su yi hukunci.”
El-Rufai, a cikin shafinsa na D mai taken “Kaduna Update,” ya ce gwamnan yana “borin kunya ne da rudani” a kowace rana.
“Ina mamakin dalili, ko da yake na tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ‘ramawa’ kura aniyarta, ya bai wa Kaduna tallafin da ya haura Naira biliyan 150, a cikin watanni 18 da suka gabata, yanzu ya bayyana komai.”
“Ta kowane hali suke kare Asiwaju don samun kudi bisa sharadi. Asiwaju ya amfana da ku. Al’ummar Jihar Kaduna za su yi hukunci a daidai lokacin da ya dace, kamar yadda ya rubuta.
A wani labarin kuma, El-Rufai ya ruwaito cewa, tsohon firaministan kasar Birtaniya Tony Blair na cewa a wani lokaci da ya gabata: “ Cikin kasashe masu tasowa, inda mutane ke gwagwarmayar sanya abin da za su sa a bakinsu, zuwa makaranta, samun ilimin kiwon lafiya na yau da kullum, samar da rayuwa ba sana’a ba, (ayyukan zamantakewa) bayarwa na iya zama bambanci tsakanin rayuwa da mutuwa; ko akalla bambanci tsakanin rayuwa mai cike da bege da wacce ta sava da hakan.
“Su (‘yan kasa) suna son a magance matsalolin da ke shafar rayuwarsu ko a rage su. Suna son ingantacciyar rayuwa, ingantaccen kiwon lafiya, ilimi da tsaro.
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Sama
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dokta Danjuma Adamu Ismaila a matsayin shugaban kwalejin koyon tukin jiragen sama ta Najeriya (NCAT) da ke Zariya.
Sanarwar da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce Dakta Ismaila, kwararre kan harkokin sufurin jiragen sama, da manufofin tattalin arziki, ya kammala karatunsa na digiri a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu digiri a fannin kimiyyar lissafi a shekarar 1989.
Ya kuma yi babbar Difloma ta a fannin Sufuri sannan ya halarci kwasa-kwasan da dama, da tarukan karawa juna sani.
Hakazalika memba ne na kungiyar masana harkar sufurin jiragen sama ta Birtaniya, wato Aeronautical Society, UK, da Ƙungiyar Binciken Sufurin Jiragen Sama, da sauransu.
Kafin nadin nasa, Dr. Danjuma Adamu Ismail malami ne a jami’ar sufuri ta tarayya dake Daura.
Daga Bello Wakili