An Kammala Taron Bitar Dabarun Yaki Da ‘Yan Bindiga A Sakkwato
Published: 7th, February 2025 GMT
Rundunar sojin Najeriya ta ce tana aiki kan hanyoyin da za su yaki ‘yan bindiga da sauran masu tada kayar baya ta hanyar amfani da darussan da aka koya a wajen wani bada horo da ya gudana a Sakkwato.
Babban Hafsan Sojojin Najeriya Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya bayyana haka a Sokoto a wajen wani taron karawa juna sani da nufin tattauna sabbin dabarun murkushe ‘yan bindiga da sauran ayyukan tada kayar baya a yankin Arewa maso Yamma, wanda aka gudanar a Runduna ta 8 ta Sojojin Najeriya dake Sokoto.
Wanda ya samu wakilcin babban hafsa Manjo Janar Olusegun Samson Abai, ya ce ziyarar wayar da kan ta taso ne domin inganta aikin da ake yi ta hanyar amfani da darasin da aka koyo na sojojin Najeriya.
Ya jaddada cewa taron karawa juna sani na daya daga cikin matakai da dama da aka dauka domin dakile kalubalen da sojojin ke fuskanta a yayin da suke gudanar da ayyukansu cikin yanayi mai sarkakiya da rashin tabbas.
Babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Olufemi, Oluyede, ya ci gaba da cewa, sojojin Najeriya na ci gaba da duba dabarunsu da hanyoyin da suke bi domin fito da dabarun shawo kan wannan kalubale.
Ya lura cewa dole ne kwamandoji a kowane mataki su ci gaba da samar da sabbin dabaru don inganta hanyoyinsu.
Ya bayyana cewa matakin ya yi daidai da Falsafar sa a wani yunkuri na karfafa sauye-sauyen da sojojin Najeriya ke yi domin ba da darasin da ya dace da kuma shirin rundunar na sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya tanada a cikin hadin gwiwa da hukumomi da dama.
Rediyon Najeriya dake Sokoto ya rawaito cewa an shirya taron karawa juna sani ga kananan hafsoshi da matsakaitan shugabannin sojojin Najeriya.
NASIR MALALI
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Sakkwato Taro sojojin Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Syria: Isra’ila Ta Kai Hari A Kan Sansanin Soja A Yankin Dar’a
Sojojin HKI sun kai wasu hare-hare akan sansanin sojan Sanamain dake gundumar Dara’a a kudancin kasar Syria.
Tashar talabijin din da “ Akhbariyyah” ta Syria ta sanar a yau Litinin cewa; sojojin Isra’ila sun kai hari akan sansanin soja na “Sanamain” wanda yake a gundumar Dar’a, kuma an ga jiragen sama na ‘yan mamaya masu yawa suna shawagi a samaniyar yankin.
Wata majiyar ta Syria ta kuma ambaci cewa; sojojin na HKI sun kursa cikin garin Mu’arrah, tare da yin kutse cikin gidaje masu yawa a ciki da gudanar da bincike a cikinsu.
A yankin Kunaidhara ma an ga sojojin na mamaya suna yin kutse, haka nan kuma sun kai hari akan filin saukar jiragen sama na Tpor, da kuma wani filin saukar jiragen sama na soja a Tadammur.
Tun bayan da gwamnatin Basshar Assad ta fadi ne dai HKI ta bude kai wa makamai da cibiyoyin sojan kasar hare-hare babu kakkautawa. A cikin kwanakin farko na faduwar gwamnatin Asad, sojojin HKI sun sanar da cewa sun rusa tsakanin kaso 70% zuwa 80% na jumillar makaman da Syria take da su, na sama, kasa da na ruwa.