Sojojin Kenya 100 sun isa Haiti domin yaƙi da ƴandaba
Published: 7th, February 2025 GMT
Sama da sojojin Kenya 100 ne suka isa ƙasar Haiti, domin karfafa jami’an tsaron Haiti da kuma aikin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, a yaƙin da suke yi da gungun ƴandaba da suka addabi ƙasar.
Sai dai ana nuna damuwa kan yadda har yanzu dakarun suka gaza tabbatar da doka a babban birnin ƙasar, Porto Prince.
An yi ta raɗe-raɗin ayyukan dakarun sun zo ƙarshe, amma kwamandan rundunar, Godfrey Otunge ya ce lamarin ba haka yake ba.
Ya ce lokacin da yake magana da jakadun yana yi ne domin kawar da shakkun da ake yi na aikinsu, ya kuma shaida cewa ƙawancen na nan daram.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kenya
এছাড়াও পড়ুন:
An Ɗauko Sojoji Daga Waje Don Horas Da Dakarun Nijeriya
A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka.
Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar.
Ana sa ran wannan shiri zai ƙara inganta ƙoƙarin jami’an tsaro, domin daƙile hare-haren da ake yawan kai wa a yankin Arewa da wasu sassan Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp