’Yan sanda sun sa dokar hana yawon dare a Gombe
Published: 7th, February 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta haramta yawon dare, ta hanyar takaita zirga-zirga daga kare 12 na dare zuwa 5 na asubahi.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya sanar a ranar Alhamis cewa dokar za ta fara aiki ranar Juma’a, 7 ga Fabrairu, 2025.
Ya bayyana cewa an kafa dokar takaita zirga-zirgar ne bayan samun rahotannin barazanar tsaro.
Sanarwar ta ce, “takaita zirga-zirgar na da nasaba da karuwar barazanar tsaro da ke fuskantar al’ummar Gombe,” kuma a shirye rundunar take ta shawo kansu.
NAJERIYA A YAU: Dalilin Faɗuwar Farashin Tumatur A Kasuwa Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya Mutuwar Almajirai: Tinubu ya buƙaci a samar da matakan kare ɗalibaiDSP Buhari ya kara da cewa rundunar za ta kara ba da muhimmanci ga tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma domin jihar Gombe ta kasance cikin aminci.
Ya bukaci jama’a su ba da hadin kai, yana mai kira ga iyaye da su gargadi ’ya’yansu su guji saba dokar domin duk mai kunnen kashin da aka kama zai yaba wa aya zaki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Sudan Sun Killace Fadar Shugaban Kasa Da Take A Hannun ‘Yan Tawayen A Birnin Khartum
Rundunar sojan kasar Sudan ta sanar da kwace iko da hanyoyin da suke isa al-Fasha, kamar kuma yadda su ka killace fadar shugaban kasa dake birnin Khartum.
Sanarwar sojojin na Sudan ta kuma tabbatar da cewa, killace wannan hanyar da su ka yi, ya yanke duk wata dama da dakarun “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” suke da ita, ta samu dauki.
Birnin al-Fasha dai shi ne babbar birnin jahar Arewacin Darfur, kuma sojojin na Sudan sun ce, suna ci gaba da kutsawa a cikin jahar.
A gefe daya, wani jami’in sojan Sudan Yasir Adha, ya sanar da cewa; Babu yadda yaki zai tsaya har sai an ‘yanto da kowane taku daya na kasar Sudan daga hannun ‘yan tawaye.
Adha ya bayyana hakan ne dai a gaban sojoji a birnin Dabbah dake jahar Arewacin kasar.
A nashi gefen gwamnan jahar Darfur, Muna Minawi ya ce, sojojin na kasar Sudan suna ci gaba da ‘yanto da garuruwan kasar har zuwa birnin Janinah da shi ne babban birnin jahar Darfur ta yamma.
Haka nan kuma ya yi kira ga dukkanin masu goyon bayan “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” a wannan yankin da su daina.
A cikin birnin Khartum kuwa sojojin Sudan sun katse duk wata hanyar kai musu dauki zuwa kusa da fadar shugaban kasa. A halin yanzu dai an killace “Dakarun Kai Daukin Gaggawa” dake cikin kusa da fadar ta shugaban kasa.