Sojojin Sudan Suna Samun Nasarar ‘Yantar Da Garuruwan Kasar Daga Mamayar ‘Yan Tawaye
Published: 7th, February 2025 GMT
Majiyoyin sojin Sudan sun sanar da cewa: Sun sake samun nasarar kwace iko da babban birnin kasar Khartoum
Majiyoyin sojin Sundan sun sanar da cewa: Cikin dan gajeren lokaci sun samu nasarar sake kwace iko da birnin Khartoum fadar mulkin kasar daga mamayar dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, bayan da suka yi birnin kawanya daga bangarori hudu.
A nata bangaren, Ma’aikatar yada labaran Sudan ta zargi bangarorin waje da jagorantar gudanar da fadace-fadacen da ‘yan tawayen dakarun kai daukin gaggawa ke yi don samun damar cin gajiyar albarkatun kasar, idan ‘yan tawaye suka yi nasara.
Rayuwa ta fara inganta a birnin Omdurman kuma kasuwanni sun fara farfadowa, inda jama’a suke komawa ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ciki har da garuruwan Kassala da Port Sudan tare da tafiye-tafiye zuwa birnin Khartoum fadar mulkin kasar, tare da cewa an fara aikin sake gina kasar ayankunan da aka samu kwanciyar hankali, amma har yanzu ana cikin damuwa da fargaba a birnin Khartoum sakamakon hare-haren bama-bamai da dakarun kai daukin gaggawa ke kai wa ta sama musamman kan asibitoci da kasuwanni.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta sake kai hare-hare Yemen
Rahotanni daga Yemen na cewa sojojin Amurka sun kai hari a filin tashi da saukar jiragen sama na Hudayda a wani sabon hari kan kasar Yemen tun bayan da Washington ta sanar da kai munanan hare-hare kan kasar dake adawa da hare-haren da Isra’ila ke kai wa al’ummar Gaza.
Tashar talabijin ta al-Masirah ta kasar Yemen ta ce an kai hare-hare ta sama har sau uku a filin jirgin saman da ke gabar tekun Bahar Maliya a daren Asabar.
Kafafan yada labaran Yaman sun kuma bayar da rahoton cewa, an kai hari da jiragen yakin Amurka a tashar jiragen ruwa ta Salif da ke lardin Hudaidah.
Jiragen yakin Amurka sun kara kai hare-hare biyar a gundumar Majzar da ke lardin Ma’rib da ke tsakiyar kasar Yemen.
A wani labarin kuma a lardin Sa’ada dake arewa maso yammacin kasar, sojojin Amurka sun kaddamar da hare-hare ta sama a yankunan Sahar da Kitaf wa al-Boqe’e.
A ranar 15 ga watan Maris ma Amurka ta sanar da kai wani hari ta sama wanda jami’an Yemen suka ce ya kashe mutane 53.
Hare-haren, wanda shi ne na farko tun bayan da Shugaba Donald Trump ya koma kan karagar mulki, ya zo ne bayan da sojojin Yaman suka yi alkawarin sabunta ayyukansu na hana duk wata safarar jiragen ruwa na Isra’ila ko kuma wadanda ke da alaka da Tel Aviv, domin nuna goyan baya ga al’ummar Falasdinu.