Kasar Iran Ta Yi Kakkausar Suka Kan Sabbin Takunkumin Da Amurka Ta Kakabawa Kasarta
Published: 7th, February 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran ya sabawa ka’idojin dokokin kasa da kasa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai da sabbin takunkuman da Amurka ta kakabawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa sun sabawa ka’idojin dokokin kasa da kasa.
Baqa’i ya yi nuni da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na kakaba takunkumi kan wasu kungiyoyi da cibiyoyi masu gudanar da ayyuka na dabi’a da al’adu na kasa Iran bisa zarginsu da hannu wajen sayar da danyen man fetur na Iran, a matsayin mummunan matakin da bai dace ba, kuma ya jaddada cewa hakan ya sabawa ka’idojin kasa da kasa.
Ya kara da cewa: Matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na matsin lamba ga al’ummar Iran ta hanyar hana kasuwanci da abokan huldarta na tattalin arziki shima haramtacciyar hanyar ka’idojin kasa da kasa ne.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta cire tukuicin wanda ya bayar da bayani kan mataimakin shugaban Taliban
Kungiyar Taliban ta ce Amurka ta cire tallafin dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan Sirajuddin Haqqani, mataimakin shugaban kungiyar kuma ministan harkokin cikin gida.
A cewar Abdul Mateen Qani, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan Taliban, an janye tukuicin da aka bayar a baya a karkashin shirin bayar da lada na ma’aikatar harkokin wajen Amurka, tare da bayyana Haqqani a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.
Kawo yanzu dai babu wani martani daga ma’aikatar harkokin wajen Amurka dangane da matakin.
Haqqani shi ne shugaban kungiyar Haqqani, wata kungiya mai karfi a cikin kungiyar Taliban wacce ta shahara wajen ayyukanta da makamai.
Duk da ayyana shi a baya a matsayin “dan ta’adda na duniya” da Amurka ta yi, Haqqani ya rike babban matsayi a cikin gwamnatin Taliban, inda aka dora masa alhakin kula da tsaron cikin gida na Afghanistan.
Kasancewar sa a cikin gwamnatin ya kasance wani batu ne da ake ta takun saka tsakanin ‘yan Taliban da gwamnatocin kasashen yammacin duniya, wadanda ke ci gaba da kakaba takunkumi tare da kin amincewa da mulkin kungiyar a hukumance.
Zargin cire ladan ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar Taliban ke kokarin ganin ta samu halacci a fagen kasa da kasa, a yayin da take kokarin kulla huldar diflomasiyya, da sakin kadarorin babban bankin Afganistan da Washington ta rike, da kuma rage takunkumin hana tafiye-tafiye a kan jami’ansu.