An Fara Binciken Badaƙalar Haɗa NIN-SIM Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Published: 7th, February 2025 GMT
Majalisar wakilai ta umarci kwamitocin sadarwa da harkokin cikin gida da su binciki haɗa lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) da layukan waya ba tare da izini ba da kamfanonin sadarwa ke yi.
Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da ‘yan majalisa Patrick Umoh da Julius Ihonvbere suka gabatar, inda aka buƙaci hukumar NCC ta ɗauki mataki kan duk wani kamfanin sadarwa da aka samu da laifi, tare da NIMC ta tabbatar da sahihancin haɗa bayanan NIN.
Umoh ya ce wannan mataki na iya haifar da damuwa ga ‘yan ƙasa, tare da jefa su cikin hatsarin satar bayanai, da damfara, da wasu laifukan intanet. Kwamitin binciken na da makonni huɗu domin kammala aikinsa.
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Tinubu ya taimaka wa ’yata ta samu aiki NUPRC — Buba Galadima
Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu, ya taimaki ’yarsa ta samu aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC).
Galadima, ya bayyana haka ne yayin wani shiri a gidan talabijin na AIT.
Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur zuwa N865 Yadda masu safarar ɗan Adam ke yaudarar mutane ta intanetYa ce duk da yana yawan sukar gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki, har yanzu shi da Shugaba Tinubu abokai ne.
Ya ce: “Abokai ne mu kuma za mu ci gaba da zama abokai. Idan ina buƙatar wani abu daga gare shi, zan iya tambayarsa.
“Bari na faɗi gaskiya a idon duniya. ’Yata ce ta yi amfani da wayata ta kira Shugaban Ƙasa, shi kuma ya yi zaton ni ne. Sai suka ce ’ya’yana ne, suka sanar da shi al’amura sun yi tsanani.”
Ya ƙara cewa: “Sun faɗa wa Tinubu cewa ‘mahaifinmu ba zai iya wannan ba, amma ya faɗa mana kai abokinsa ne.’
“Ɗaya daga cikinsu ta ce ta kammala NYSC amma ba ta samu aiki a NUPRC wacce Gbenga Komolafe ke jagoranta.
“Tinubu ya ‘kira Komolafe, ya ce ku bai wa ’yar abokina aiki.’ Shi ya sa ta ke son zuwa Makkah don yi wa Allah da Shugaban Ƙasa godiya.”
Galadima ya kuma bayyana cewa ’yarsa ta yi aiki a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na tsawon shekara huɗu ba tare da an taɓa biyanta albashi ba.
Ya ce: “’Yata ta yi aiki da shi (Buhari) har na tsawon shekara huɗu, kuma ya bayar da umarnin kada a biya ta albashi.
“Sai dai duk wata a kawo takardar da ke nuna an biya ta. Ta yi aiki da Buhari shekara huɗu a ofishin Osinbajo ba tare da ta karɓi ko sisin kwabo ba,” in ji shi.
Galadima, ya kuma ce shi kansa ya yi aiki tare da Buhari na tsawon shekara goma sha uku.
Wannan kalamai sun bai wa mutane da dama mamaki, musamman ganin cewa Galadima ya shahara wajen sukar gwamnatin APC a fili.