Aminiya:
2025-04-16@09:14:55 GMT

’Yan bindiga sun mamaye masallaci sun yi awon gaba da masallata a Sakkwato

Published: 7th, February 2025 GMT

Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu masallata a wani masallaci a unguwar Bushe da ke Ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.

Waɗanda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki masallacin ne da asubahin ranar Alhamis a yayin da masu ibada ke yin Sallar Subhi da asuba.

Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Yadda bom din Boko Haram ya kashe mutane a hanyar kasuwa a Adamawa

Aƙalla masallata 10 da suka haɗa da Limamin ne aka ce an yi awan gaba da su a yayin harin.

Jaridar Punch ta ruwaito DSP Ahmed Rufa’i, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a.

Rufa’i ya ce, rundunar ’yan sandan tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro, suna aiki tuƙuru don ganin an sako dukkan waɗanda lamarin ya shafa cikin gaggawa.

Ya ce: “Na tabbatar da faruwar lamarin ne daga bakin babban jami’in ofishin ’yan sanda DPO na unguwar lokacin da na zanta da shi ta wayar tarho.

“Ina so in tabbatar muku cewa, rundunar ’yan sandan Nijeriya tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro suna aiki tuƙuru don ganin an sako dukkan waɗanda aka yi garkuwa cikin gaggawa.”

Shima Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato mai wakiltar yankin Sa’idu Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Sakkwato yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Ta Bukaci Jami’an Tsaro Mata Su Rika Sanya Hijabi Yayin Aiki

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da amfani da Hijabi ga jami’an tsaro mata a fadin jihar.

Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa da aka gudanar a fadar gwamnatin  jihar da ke Dutse.

A cewarsa, majalisar ta bayar da umarni ga kamfanonin tsaro guda uku da ke aiki a jihar, su bai wa jami’an tsaro mata daga cikin matasa 9,969 da aka dauka aiki, damar sanya Hijabi yayin aiki, a matsayin girmamawa ga addini da al’adu.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, wannan matsaya ta biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar kan tsaron makarantu, asibitoci da kotuna ya gabatar, kuma aka sake jaddada kudurin gwamnatin na tabbatar da tsarin aiki mai cike da mutuntaka, da daidaito.

Ya ce, majalisar zartarwar ta kuma amince da kaddamar da makon kirkira da kere-kere na jihar (JISCIW) daga shekarar 2025.

Ya jaddada cewa, wannan tsari na nuna jajircewar gwamnatin wajen bunkasa basira da hazakar matasa, da kuma inganta kirkire-kirkire da tunani mai zurfi a fadin jihar.

Sagir ya bayyana cewa, JISCIW zai kara zaburar da matasa a fannoni daban-daban kamar fasaha, zane, kasuwanci da kuma harkokin fasaha.

Ya kara da cewa, majalisar ta amince da fitar da sama da Naira miliyan 516 domin sayen tikitin jirgi ga daliban jihar Jigawa 185 da ke karatu a fannin likitanci da kimiyyar kiwon lafiya a Jami’ar Near East dake kasar Cyprus, domin shirye-shiryen zangon karatu na shekarar 2024/2025.

Kwamishinan ya kara da cewa, wannan tallafi ya nuna yadda gwamnatin ke ci gaba da daukar nauyin ilimi da jin dadin daliban da ke karatu a kasashen waje, musamman a muhimman fannoni kamar likitanci da kiwon lafiya.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 7 A Wani Sabon Hari A Benuwe
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bukaci Jami’an Tsaro Mata Su Rika Sanya Hijabi Yayin Aiki
  • EFCC ta gaza tabbatar da tuhumar Murja kan zargin wulaƙanta takardar Naira
  • Bello Turji ya kashe manoma 11 a Sakkwato
  • Mutum 45 Sun Rasa Rayukansu A Wani Sabon Hari A Filato 
  • ‘Yansanda Sun Kama Wasu Da Ake Zargin Ɓarayin Wayar Wutar Lantarki Ne A Yobe
  • ’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato
  • ‘Yansanda Sun Gano Haramtaccen Wurin Hada Makamai A Kano
  • An kama kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
  • An kama miyagun kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano