Haɓaka Adabin Rubutu Da Zaƙulo Haziƙan Ɗalibai Ne Muradinmu A 2025 – TYBLI
Published: 7th, February 2025 GMT
Gidauniyar ‘TY Buratai Literary Initiative (TYBLI)’ ta kaddamar da shirye-shiryen tallafinta na 2025 wanda ta kudiri aniyar bunkasa ilimi da tsarin koyo a tsakanin daliban Nijeriya. Shirin wanda gidauniyar Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) ta kirkiro kuma ta dauki nauyin wannan shiri na da nufin kwadaitar da koyon Adabin rubutu da kuma bai wa daliban da suka fi hazaka tukuici a fadin kasar nan.
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Lafiya Ya Yi Alƙawarin Inganta Tallafi Ga Likitoci A Hajjin 2025
“Duba da yanayin kiwon lafiya a duniya tun bayan ɓullar cututtuka kamar sanƙarau da Shan Inna, wajibi ne mu bi ƙa’idojin kiwon lafiya na Saudiyya.
“Dole ne mu tabbatar da cewa dukkanin alhazai sun samu takardun rigakafi da katin shaidar lafiya,” in ji shi.
Ministan, tare da rakiyar wasu manyan jami’an ma’aikatar lafiya, sun duba motocin ɗaukar marasa lafiya na NAHCON, kayan magani, da shirye-shiryen kiwon lafiya a asibitocin Nijeriya da ke Saudiyya.
Sun gano muhimman wuraren da ake buƙatar ingantawa, ciki har da wadatar magunguna, alluran rigakafi, na’urorin likitanci, da motocin ɗaukar marasa lafiya.
Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yaba da shirin Ministan, inda ya ce: “Ziyararku ta ƙara mana ƙwarin gwiwa a ƙoƙarin da muke yi na inganta kiwon lafiyar alhazai.”
A duk shekara, kimanin ‘yan Nijeriya 70,000 ne ke halartar aikin Hajji, kuma Ministan Pate ya bayyana damuwarsa kan matsalolin da ke tattare da yanayin zafi mai tsanani da ake tsammanin fuskanta a Hajjin 2025.
Ya ce an ɗauki matakan kariya don tabbatar da lafiyar alhazai da jin daɗinsu.
Wannan shiri na haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Lafiya da NAHCON zai tabbatar da cewa mahajjatan Nijeriya sun samu ingantacciyar kulawa.
NAHCON ta kuma tabbatar da ƙudirinta na ci gaba da samar da ingantattun ayyuka ga alhazai.
Waɗanda suka halarci wannan ziyarar sun haɗa da Minista Pate, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, Kwamishinan Ayyuka Prince Anofi’u Olanrewaju Elegusi, Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal, Prince Abdul-Razak Aliyu, Dokta Sa’edu Ahmad Dumbulwa da sauran manyan jami’ai na NAHCON da Ma’aikatar Lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp