Kasar Sin ta yi watsi tare da nuna kin amincewarta da tsegumin da aka yi mata daga bangaren Amurka, inda sakataren harkokin wajen Amurkar, Marco Rubio ya yi wasu zarge-zarge marasa tushe balle makama a kan kasar ta Sin, yayin da yake ziyara a yankin Latin Amurka da Caribbean.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana hakan a yau Juma’a, inda ya kara da cewa, kalaman marasa tushe daga bangaren Amurka, wadanda suka karkata zuwa tunanin yakin cacar-baka da nuna son zuciya, zarge-zarge ne kawai na yamadidi a kan kasar Sin da aka kitsa da nufin haifar da sabani tsakaninta da kasashen da abin ya shafa na Latin Amurka da Caribbean, wanda kuma hakan tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar Sin, da kuma gurgunta hakkoki da moriyar kasar Sin ta halaliya da kuma muradunta.

Game da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da yankin na LAC kuwa, mai magana da yawun ma’aikatar ya ce, kasar Sin ta kuduri aniyar karfafa abokantaka da hadin gwiwa tare da kasashen na LAC bisa tsarin mutunta juna, da daidaito, da cin moriyar juna, da bude kofa, da hada kai, da sauran harkokin hadin gwiwar samun nasara ga ko wane bangare. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya godewa ministan harkokin wajen kasar Omman

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Bagaei ya godeawa ministan harkokin wajen kasar Omman kan yadda ya shirya ya kuma gabatar da tattaunawa tsakanin JMI da Amurka a birnin Mascat da kuma kai kawon da yayi a  tsakanin bangarorin biyu.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Bagaei yana bayyana haka a wani sakon da ya aika a cikin shafinsa na X  a jiya Asabar, ya kuma aika da sakon ne a dai dai lokacinda ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana kan hanyarsa ta dawowa Tehran, bayan tattaunawar. Ya kuma kara da cewa yana fatan Badr bin Hamad Al Busaidi zai ci gaba da wannan kokarin a ranar Asabar mai zuwa inda bangarorin biyu zasu sake haduwa, sannan har zuwa karshen tattaunawar. Bayan kammala tattaunawar dai,  shugaban tawagar JKI a tattaunawar kuma ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana a shafinsa na X kan cewa, tattaunawar ta yi armashi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Yi Watsi Da Matsawa Sauran Kasashe Lamba
  • Iran, Iraki Sun Karfafa Dangantakar Makamashi
  • Rigima: Mawaƙi Portable ya kwana a hannun ’yan sanda
  • Xi Da Prabowo Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 75 Da Kulla Huldar Diplomasiyya Tsakanin Sin Da Indonesiya
  • Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya godewa ministan harkokin wajen kasar Omman
  • Sharhi: Tattaunawa Zagaye Na Farko Tsakanin Iran Da Amurka A Oman
  • Sin Da Sifaniya Sun Daga Matsayin Hadin Gwiwa A Fannin Shirya Fina-finai
  • Iran da Amurka zasu ci gaba da tattaunawa a mako mai zuwa
  •  A Yau Asabar Ne Ake Bude Tattaunawa A Kasar Oman Akan Shirin Makamashin Nukiliyar Iran
  • Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro