’Yan fashin teku sun sace jirgin fasinja mutum 11 sun ɓace a Ribas
Published: 7th, February 2025 GMT
Wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun yi awon gaba da wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji 20 a hanyar ruwan daga Bonny zuwa Okrika a Jihar Ribas.
Sai dai jami’ai a ƙaramar hukumar Bonny ta ce ta kuɓutar da tara daga cikin fasinjojin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don ceto sauran.
Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace Magungunan Jabu: ’Yan majalisa sun nemi yin hukuncin ɗaurin rai da raiShugaban Ƙaramar hukumar Bonny, Hon Anengi Barasua Claude-Wilcox ya ce, an ceto mutanen tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro.
Claude-Wilcox a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Boma Waribor ya fitar a ranar Juma’a, ya ce direban jirgin fasinja ya saɓa wa ƙa’idar wucewa ta kilomita 10, wanda haramtacciyar hanya ce ga direbobin kwale-kwalen fasinja.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Tattaunawar tsaro da shugaban ƙaramar hukumar Bonny, Anengi Barasua Claude-Wilcox ya yi, ya nuna cewa an yi fashin wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji 20 da ke kan hanyarsa ta zuwa Bonny da yammacin ranar Alhamis a yankin Isaka da ke Ƙaramar Hukumar Okrika.
“Duk da haka, ya kamata a lura da cewa an gano mutane tara aka dawo da su Fatakwal ta hanyar sa hannun jami’an tsaro na gwamnati a kan lokaci, waɗanda a halin yanzu suka ƙara ƙaimi wajen ceto sauran fasinjoji 11.
“Ya kamata a lura cewa binciken farko ya nuna cewa, direban jirgin ya bijirewa ƙa’idar hanyar kuma ya wuce kilomita 10, hanyar ruwan da aka haramta ga direbobin Jirgin ruwan fasinjoji.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fashin jirgin ruwa Fatakwal
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗansanda Ya Kashe Matar Abokin Aikinsa, Ya Jikata Wasu Biyu A Ribas
Wani Sufeto Dansandan da ke aiki a Jihar Kuros Ribas, ya harbe matar abokin aikinsa har lahira tare da jikkata wasu mutane biyu a harbe-harben da ya yi a ranar Lahadi.
Mai magana da yawun rundunar, SP Irene Ugbo, ta tabbatar da faruwar lamarin ga Labarai a birnin Kalaba, inda ta bayyana cewa jami’an Dansandan ya nuna halayyar da ba ta dace ba kafin ya fara harbe-harben.
Ba Na Goyon Bayan Dakatar Da Gwamnan Jihar Ribas – Ndume Bututun Iskar Gas Ya Sake Fashewa A RibasUgbo, ta ƙara da cewa jami’in, naaiki ne a Cibiyar ‘Yansanda ta Atakpa, ya dawo daga aikin dare a wani bankin ‘Microfinance’ kafin afkuwar lamarin. Ta kuma bayyana cewa tuni an kama wanda ake zargi, inda su kuma waɗanda suka jikkata ke samun kulawar likitoci a asibiti.
Bincike ya nuna cewa ɗansandan ya fara nuna alamun taɓun hankali tun bayan dawowarsa daga aikin dare, inda ya rufe ƙofar shiga ofishin ‘yansandan tare da hana kowa fita ko shigowa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp