HausaTv:
2025-03-25@17:25:35 GMT

Limamin Tehran:Trump Ba Zai Taba Cimma Manufofin Da Ya Bayyana Ba

Published: 7th, February 2025 GMT

 Wanda ya jagoranci sallar juma’a a yau anan birnin Tehran, Hajjatul-Islam Kazim Saddiki, ya bayyana cewa: Trump yana yin baraza da tsoratarwa da cewa zai rage karfin da Iran take da shi a fagen fasahar Nukiliya da kuma matsayin da take da shi a cikin wannan yankin na yammacin Asiya, sai dai kuma ya kamata ya fahimci cewa kamar yadda shugaban da ya gabace shi ya yi kuskuren lissafi, to shi ma haka yake yi.

Limamin na Tehran ya kuma ce,Kamar yadda shugaban Amurka da ya gabaci Trump bai sami nasara akan Iran ba, shi ma haka ba zai cimma manufarsa ba.

Hajjtul-Islam Siddiki ya kuma kara da cewa; Bai kamata ace muna  kallon cewa ta hanyar abubuwa na zahiri ne kadai za a iya warware matsaloli ba,domin wannan shi ne koyawar tauhidi a cikin alkur’ani mai girma. Haka nan kuma ya yi kira da kar a biye da mika kai ga sha’awace-sha’awace na duniya ba, maimakon haka mu mika kai da yin biyayya ga dokokin Allah domin mu sami haskakawa akan hanyar da muke tafiya a kanta.

 Da yake magana akan kwanaki 10 na cin nasarar juyin juya halin musulunci a Iran, Limamin na Tehran ta ce, abinda ya  faru yana cike da darussa da al’umma za ta dauki darussa daga ciki har adaba. Kuma gagarumin sauyin da ya faru a cikin al’ummar Iran yana daga cikin manufar da juyi ya cimmawa a karkashin jagorancin Imam Khumaini (r.a).

Haka nan kuma ya bayyana cewa;siffa mafi girma da take tattare da juyin shi ne kasantuwarsa ta musulunci, kuma a lokaci daya akan tsarin jamhuriya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Fiye Da Dalibai 4,200 Suka Amfana Da Tallafin Ilimi Na Sanata Solomon Adeola

Ya kara bayanin cewa an dauki matakin ne inda har abin ya shafi daliban da suke mazabun majalisar Dattawa biyu na Jihar Osun.

Ya nuna jin dadinsa inda ya furta ce wa“Wani abin farinciki ne gare ni dana samu yawan daliban da suka samu damar yin rajista daga mazaba ta da kuma saiuran mazabun na majalisar Dattawa, wadanda su basu samu damar rubuta jarabawar da zata basu damar zuwa manyan makarantu ba a fadin tarayyar Nijeriya.

“Ilimi shi ne wani babban abinda ya kamata kowane dan/ ‘yar kasa su kasance sun samu damar yin haka ta samun sa, don haka lamarain kudi bai dace ace ya hana su damar samun hakan ba musamman ma ga matasa wadanda sune manyan gobe kamar yadda Sanatan ya bayyana”.

Daga karshe ya yi karin bayani ne na shit sarin bada fom domin cikawa saboda rubuta JAMB wata dama ce ita ma tayi kama ko daya take da damar bada guraben karatu zuwa manyan makarantu, na dalibai 500 za a cimma burin yin haka cikin makonni masu zuwa na gaba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [17]
  •  Syria: Isra’ila Ta Kai Hari A Kan Sansanin Soja A Yankin Dar’a
  •  Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon Ya Yi Gargadi Akan Masu Tunanin Kulla Alakar Kasar Da HKI
  •  Arakci: Babu Wanda Zai Yi Tunanin Kawo Wa Iran Hari
  • UNICEF: Yara a Gaza suna fama da matsalar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba
  • Fiye Da Dalibai 4,200 Suka Amfana Da Tallafin Ilimi Na Sanata Solomon Adeola
  • Moscow : Dole ne Rasha da China su shiga tattaunawar nukiliya da Iran
  • Kao Kim Hourn: Ba Ta Hanyar ‘Siddabaru’ Kasar Sin Ta Cimma Nasarori A Fannin Ci Gaba Ba Sai Dai Ta Hanyar Aiki Tukuru Kuma Mai Dorewa
  •  Haaretz: Sojojin Isra’ila Suna Kan Shirya Kai Wa Gaza Hari Ta Kasa
  •  Amurka: Turmp Yana Son Yin Yarjejeniya Ne Da Iran Ba Yaki Ba!