Tunisiya: An Daure Rashid Alganushi Shekaru 20 A Gidan Kurkuku
Published: 7th, February 2025 GMT
Kotun manyan laifuka a kasar Tunisiya ta daure Shugaban kungiyar al-Nahdha ta masu kishin musulunci Rashid al-Ganushi, zaman kurkuku na tsawon shekaru 20.
Haka nan kuma an daure wata ‘yar Jarida Shahrizad Ukkasha wacce take wajen kasar, zaman kurkuku na tsawon shekaru 22.
Wata ‘yar jaridar da ita ma ta sami hukuncin dauri, ita ce Shuza Bilhaj, wacce za ta yi zaman kurkuku na tsawon shekaru5.
Shi kuwa tsohon minista Lutfi Zaitun an yanke masa hukuncin zaman kurkuku na shekaru 35, sai kuwa mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gida Muhammad Ali al-Aruri, shekaru 13 a gidan kaso. Yayin da tsohon shugaban gwamnatin kasar Hisham al-Mashishi zai yi zaman shekaru 35 a gidan kurkuku.
Tun a watan Disamba na 2021 ne aka bude sharia akan wadannan ‘yan siyasar, wacce ake wa kallon cewa ba ta da wani tushe na doka da ya wuce yi wa ‘yan siyasa bita da kulli.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
A Kasar Gabon Brice Oligui Nguema Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya lashe zabe da kawo 90.35% kamar yadda sanarwar ma’aikatar cikin gida ta sanar.
Brice Nguema ne dai ya jagoranci juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Ali Bango a watan Ogusta na shekarar 2023, ya kuma shiga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar a wannan zaben.
Dan takara na biyu da yake binsa a baya, shi ne Alain Claude Bilie Bie Nze da ya sami kaso 3.02% na jumillar kuri’un da aka kada.
An sami halartar kaso 70.4% na jumillar wadanda su ka cancanci kada kuri’a da ya zama mai muhimmanci da zai kawo karshen mulkin rikon kwarya na soja.
Zaben na wannan lokacin shi ne irinsa na farko tun 2023.
Yawan masu kada kuri’ar dai sun kai 920,000, sai kuma masu sa idanu daga kasashen waje da sun kai 28,000.
Adadin mutanen kasar Gabon ya kai miliyan 2.3 da mafi yawancinsu suke rayuwar talauci duk da cewa Allah ya huwace wa kasar arzikin man fetur.
Masu Sanya idanu akan zaben sun ce, a kalla san sami kula da dukkanin ka’idojin zabe a cikin kaso 94.8 na mazabun kasar, kuma an baje komai a faifai ba tare da kumbaya-kumbiya ba da kaso 98.6%. Gabanin yin juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin iyalan Bango na shekaru 50, Oligui Nguema ya kasance shugaban rundunar da take tsaron fadar shugaban kasa na kusan shekaru biyu.