HausaTv:
2025-04-15@23:22:21 GMT

Kudin Ajiyar Najeriya Na Kasashen Waje Sun Ragu Da Dalar Amurka Biliya 1.79

Published: 7th, February 2025 GMT

Bayanin da babban bankin kasar ta Najeriya ya fitar, ya bayyana cewa an sami wannan koma bayan ne a cikin makwanni uku da su ka gabata.

Bayanin na babban bankin na Najeriya ya ci gaba da cewa, kudaden ajiyar Najeriya na waje da a cikin watan Disamba sun kai dala biliya 40,887, sun ragu, sun zama dala biliyan $39.

723 daga ranar 31 ga watan Janairu 2025.

An bayyana koma bayan ne a kudaden waje na ajiya da babban bankin kasar yake da su, da ya kamata ace a ranar 4 ga watan Febrairu ne za a fitar da kididdiga akan halin da kudaden wajen suke ciki,amma ba a yi ba.

Bugu da kari  wannanbayanin  ya fito ne daga kamfanin dake kula da  kai da komawar kudaden Waje  Bismack Rewane da yake hasashen samun raguwar kudaden ajiyar na Najeriya a tsakanin shekarar 2025-2026 sai sami koma baya da kaso 11.47,wato zuwa dala biliyan 36.21, yayin a a cikin shekarar 2026 zai zama dala biliyan 37.65,alhali a 2024 ya kasance dala biliyan 40.9.

Farashin Naira idan aka kwatanta ta da Dala, a  3 ga watan nan  na Febrairu shi ne ; Naira 1,500.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: dala biliyan

এছাড়াও পড়ুন:

Hauhawar Farashi ya ƙaru a watan Maris — NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce hauhawar farashi ya ƙaru a ƙasar zuwa kashi 24.23 cikin 100 a watan Maris.

Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna an samu ƙarin kashi 1.05 daga kashi 23.18 cikin ɗari da aka samu a watan Fabrairu.

EFCC ta gaza tabbatar da tuhumar Murja kan zargin wulaƙanta takardun kuɗi ’Yan Najeriya sun koka kan rashin ingancin shinkafar Gwamantin Tarayya

Wannan ne karon farko da aka samu ƙarin hauhawar farashin tun bayan da hukumar ta NBS ta soma fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi a farkon shekarar nan.

Sai dai bayan soma amfanin da sabon tsarin fitar da ƙididdigar a watan jiya, NBS ta ce da wuya a iya gane haƙiƙanin raguwa ko hauhawa a yanzu.

A wani jawabi da ya yi manema labarai tun a watan da ya gabata, shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya bayyana cewa sun sauya tsarin ne saboda “daidaita shi da irin na sauran ƙasashen duniya.”

Ya ce karo na ƙarshe da Nijeriya ta sauya tsarin ƙididdigar shi ne a shekarar 2009, inda ake ƙididdige farashin kayan da aka fi amfani da su a wannan tsakanin.

Hakan na nufin yanzu za a riƙa kwatanta farashin kayayyakin da aka ƙididdige daga shekarar 2024, maimakon 2009 da aka riƙa amfani da ita a baya.

A sabbin alƙaluman da NBS ta fitar, ta alaƙanta hauhawar farashin da tashin kayayyaki irinsu citta, garin rogo, shinkafa, zuma, dankali, barkono da sauransu.

Aminiya ta ruwaito cewa, Hukumar NBS ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma kashi 24.48 daga 34.8 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hauhawar Farashi ya ƙaru a watan Maris — NBS
  • Duk da samun koma baya: Najeriya ce kasa mafi arzikin danyen mai a Afirka —OPEC
  • Noman rake: Najeriya da China sun kulla yarjejeniyar kasuwancin $1bn
  • Kamata Ya Yi Amurka Ta Kara Kokarin Gyara Kuskurenta 
  • Guguwar Kudin Fito Na Gwamnatin Trump: Dabara Ko Hauka?
  • Cinikin Waje Na Sin Ya Karu Da Kashi 1.3 A Rubu’in Farkon Bana
  • Kasashen Turai na E3 sun goyi bayan tattaunawar Iran da Amurka
  • Iran Ta Ce Za’a Gudanar Da Zagaye Na Gaba Tsakaninta Da Amurka Ne A Birnin Roma Na Kasar Italiya
  • Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
  • Ukraine na Fuskantar Wata Barazana, Dangane Da Bukatar Amurka Na Kwace Iko Da Cibiyar Gas Na Rasha  A cikin Kasar