HausaTv:
2025-03-24@00:49:05 GMT

 Kasar Venezuela Ta Yi Allawadai Da Kwace Mata Jirgin Sama Da Amurka Ta Yi

Published: 7th, February 2025 GMT

MA’aikatar harkokin wajen kasar Venezue ta sanar da cewa; Abinda Amurkan ta yi sata ce a tsakar ranar Allah da ta yi wa dukiyar al’ummar Venezueal, tare da cewa za ta dauki dukkanin matakan da su ka dace domin sake dawo da jirgin saman nata.”

Sanarwar ta kuma zargin ministan harkokin wajen Amurka Marco Robio da cewa shi ne ya bayar da umarnin kwace jirgin na Venezuela.

Haka nan kuma ta kara da cewa; Kiyayyar da Robio yake yi wa kasar Venezuela ce ta sa shi kwace jirgin, da hakan ya mayar da shi zama barawon jiragen,alhali a baya, ba shi da wani aiki sai cusa kiyayya da gaba.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Venezuela ta bukaci ganin an dawo ma ta da jrigin samanta da gaggawa.

Amurka dai ta kwace jirgin saman kasar Venezuela ne da ya sauka a kasar Dominican, bisa zargin yana da alaka da kamfanin man fetur na kasar. Tun a 2019 ne dai Donald Trump ya rattaba hannu akan dokar haramta haramta mu’amala da kamfanin man fetur din na  kasar Venezueal (PDVSA)

Wannan dai ba shi ne karon farko da Amurkan take kwace dukiyar kasar Venezuela ba, domin a shekarar da ta gabata ma ta kwace wata matatar mai mallakin Venezuela dake cikin kasar ta Amurka.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar Venezuela

এছাড়াও পড়ুন:

Wang Yi: Kasar Sin Na Da Kwarin Gwiwa Kan Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu  

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a jiya cewa, kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da kasashen Japan da Koriya ta Kudu, kuma tana da kwarin gwiwa kan hakan.

Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar taron firaministan kasar Japan Shigeru Ishiba a birnin Tokyo tare da ministocin harkokin wajen kasashen Japan da Koriya ta Kudu. Yana mai cewa, an fara hadin gwiwa tsakanin Sin da Japan da Koriya ta Kudu da wuri, inda aka samu sakamako da dama, kuma tana da babban tasiri, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta fahimtar juna da hadin gwiwar moriyar juna a tsakaninsu.

Wakilin Musamman Na Xi Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugabar Namibiya Fadin Yankin Da Ke Fama Da Zaizayar Kasa Na Kasar Sin Ya Ragu A 2024 

Kazalika, dangantakar Sin da Japan da Koriya ta Kudu tana kara bunkasa, za a kara tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Bugu da kari, hadin gwiwarsu na kara zurfafa, kasashen yankin za su kara kaimi wajen tunkarar kalubale daban daban daga waje.

Wang ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Japan da Koriya ta Kudu, wajen kafa sahihiyar ra’ayi game da tarihin yakin duniya na biyu, da kiyaye tsarin bangarori daban daban, da kiyaye muhimmiyar rawar da MDD ke takawa a tsarin kasa da kasa, da ci gaba da inganta hadin gwiwa, da ba da gudummawa ga samun zaman lafiya da wadata a shiyyar da duniya baki daya. (Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al-Huthi Ya Ce Kawo Wani Jirgin Ruwa Mai Daukar Jiragen Saman Yaki Gazawa Ce Ga Amurka
  • Amurka ta sake kai hare-hare Yemen
  • Amurka ta cire tukuicin wanda ya bayar da bayani kan mataimakin shugaban Taliban
  • Wang Yi: Kasar Sin Na Da Kwarin Gwiwa Kan Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu  
  • Kwana Daya Bayan Kwace Fadar Shugaban Kasa, Sojojin Sudan Sun Kwace Babban Bankin Kasar
  • Ranar Mata Ta Duniya: NPA Ta Mayar Da Hankali Wajen Kare ‘Yancin Mata –Dantsoho
  • Wike Ya Kwace Filaye 4,794 A Abuja Saboda Rashin Biyan Kudin Ka’ida
  • Saree: Filin jirgin saman Ben Gurion ba shi da aminci har sai an kawo karshen yakin Isra’ila a Gaza
  • Sojojin Sudan Sun Kwace Iko Da Fadar Shugaban Kasa A Birnin Khartum
  • Dubban Mutane Sun Fito Zanga-Zangar Yin Allawadai Da Kama Magajin Garin Istambul