Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dakta Ajuji Ahmed, ya tabbatar da shugabancinsa, inda ya yi watsi da ikirarin wani bangare na jam’iyyar, inda ya bayyana cewa shi ne wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta amince da shi. Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja ranar Juma’a, Ahmed ya tabbatar da cewa, jam’iyyar na nan a karkashin shugabancinsa da kuma kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da aka kaddamar a shekarar 2022.

Sin Ta Yi Watsi Da Tsegumin Da Marco Rubio Ya Yi Kan Hadin Gwiwarta Da Latin Amurka ‘Yansanda Sun Kama Mutum Uku Da Kokon Kan Mutum A Imo Dakta Ahmed ya jaddada cewa, INEC jam’iyyar NNPP daya ta sani, mai tambarin launin ja, fari, da jajayen kalamai, da littafi, da kuma hular ilimi mai taken, ilimi ga kowa, “Education for All”. Ya bukaci ‘yan Nijeriya da masu yada labarai da su tabbatar da ikirarinsa da ke shafin hukumar ta INEC. Da yake martani kan taron da wani bangare na jam’iyya NNPP ya gudanar a Legas kwanan nan, Dr. Ahmed ya yi watsi da taron, a matsayin taron da ya sabawa doka. Ya bayyana cewa, jam’iyyar bata gudanar da wani taro a wajen hedikwatarta da ke Abuja ba, ya kuma musanta ikirarin kaddamar da sabon kwamitin gudanarwa a wasu wurare sabanin na Abuja.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

APC Ta Tafka Asara, Wani Jigo Ya Fice A Enugu 

Tsohon shugaban jam’iyyar APC a Jihar Enugu, Dr. Ben Nwoye, ya ajiye muƙaminsa daga jam’iyyar. Nwoye, wanda ya sanar da haka a wani taron manema labarai ranar Alhamis, ya ce wannan shawara ta biyo bayan rushewar jagorancin jam’iyyar a jihar.

Kafin yanke wannan shawara, Nwoye ya ce ya tattauna da magoya bayansa da sauran masu ruwa da tsaki, amma bai bayyana wacce sabuwar jam’iyyar da yake shirin shiga ba.

Masu Gida Sun Yi Ruwan Kwallaye A Enugu Mutane Da Dama Sun Rasu Sakamakon Bindigar Tankar Mai A Enugu

Nwoye ya bayyana cewa jagorancin APC a Kudu maso Gabas sun koma siyasar keta haƙƙoƙin juna, inda ya ce ba su da sha’awar ƙara wata jiha a cikin jihohin da jam’iyyar ke mulki a wannan yanki.

Nwoye ya kuma zargi jagorancin jam’iyyar APC na ƙasa da cewa suna jin daɗin mulkin su, inda suka kasance a ƙarƙashin jam’iyyar da ta haifar da shugaban Najeriya da yawancin ‘yan majalisar dokoki. Ya ƙara da cewa, “Jagorancin APC na ƙasa yana da hargitsi, sannan suna barin rikici yayi ƙamari sosai har ya halaka jam’iyyar a Jihar Enugu.” Ya bayyana cewa ya tattauna sosai da magoya bayansa na ƙasa, kuma ya yanke shawarar cewa lokaci ya yi da zai fice daga APC.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike
  • Dole Kwankwaso Ya Nemi Afuwarmu Kafin Ya Komo APC
  • APC Ta Gaza Gudanar Da Taron NEC Cikin Shekaru Biyu – PDP Ta Zarge Su
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Makasudin Rubuta Sakon Jagora Ga Shugaban Kasar Rasha
  • APC Ta Tafka Asara, Wani Jigo Ya Fice A Enugu 
  • Majalisar Kasa Ta Rasha Ta Amince Da Yarjeniyar Dangantaka Ta Musamman Tsakanin Iran Da Kasar
  • Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin Kidayar Jama’a Na Kasa
  • An Kashe Mutane 7 A Yayin Da ‘Yan Ta’adda Suka Ƙaddamar Da Wani Sabon Hari A Adamawa
  • Ina Da Ƙwarewar Da Zan Iya Zama Shugaban Ƙasar Nijeriya – Makinde
  • An Gudanar Da Taron Kasa da Kasa Don Tallafawa Yan Gudun Hijirar A Sudan