Layin Dogo Na Habasha-Djibouti Na Kara Karfin Jigilar Kayayyaki Zuwa Kasashen Waje
Published: 8th, February 2025 GMT
Babban jami’in gudanarwa na kamfanin EDR Takale Uma, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kamfanin layin dogo na Ethio-Djibouti (EDR), yana samun ci gaba mai kyau, tare da kara karfinsa na jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje. Uma ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Tare da karin kan jiragen kasa da taragu, yanzu mun samu damar baiwa karin wurare hidima, mun fadada zirga-zirga daga Indode da Adama zuwa Mojo, Dire Dawa, da kuma wurin ajiye kaya na Sabata.
Uma ya kara da cewa, EDR yana maye gurbin tsoffin kayayyakin aiki da sabbi, da kuma gyara wadanda suka lalace, kana ya kara yawan jiragensa daga jiragen kasa takwas zuwa 21 da taragu 892 zuwa 935. Yana mai cewa “Jajicewar da muka yi wajen habaka aikin wurin ajiye kaya da jiragen kasa yana nufin karin inganci da rage tsadar gudanar da ayyuka, kuma yana taimakawa wajen biyan bukatun al’ummar kasar wajen yin zirga-zirga.”
Tun lokacin da aka kaddamar da shi a shekarar 2018, layin dogon wanda kasar Sin ta gina ya ci gaba da bunkasa kasuwar dakon kayayyaki da kuma fadada ayyukansa na hidima, ciki har da ayyuka masu inganci kamar sufurin kayayyakin sanyi, da jiragen kasa masu jigilar mazauna kauyuka, da jiragen kasa na musamman don jigilar motoci. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
কীওয়ার্ড: jiragen kasa
এছাড়াও পড়ুন:
Jagora: Siyasar Kasar Iran Ta Ginu Ne Akan Kyautata Alaka Da Kasashen Makwabta
Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da sarkin Katar a jiya Laraba ya bayyana cewa; Siyasar Iran ta ginu ne akan kyautata alaka da kasashen makwabta, kuma tuni an cimma sabbin matakai a wannan fagen.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma fada wa sarkin na Katar Tamim Bin Hamad ali-Sani cewa, ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yana fadi tashi a wannan fagen na kyautata alaka da kasashen makwabta, tare da yin kira da cewa yarjeniyoyin da aka kulla su zama masu kare maslahar kasashen biyu.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana kasar Katar a matsayin kasa abokiya, kuma ‘yar’uwa ta Iran, duk da cewa har yanzu da akwai wasu batutuwa da ba a kai ga warware sub a,kamar dawo da kudaden Iran da aka zuba a Bankunan kasar daga Korea Ta Kudu.
A nashi gefen sarkin Katar ya jinjinawa matakan da Iran din take dauka na taimakawa raunana a duniya, da kuma al’ummar Falasdinu, kuma yadda ta kasance a tare da Falasdinawa wani abu ne da ba za taba mancewa da shi ba har abada.