Jordan Ta Gargadi Amurka Cewa: Tada Hargitsi A Kasarta Zata Shafi Dukkan Yankin Gabas Ta Tsakiya
Published: 8th, February 2025 GMT
Manyan jami’an kasar Jordan sun gargadi Amurka cewa: Idan ta janyo hargitsi a Jordan, to zai mamaye dukkan kasashen yankin gaba daya
Shugaban majalisar dattijan kasar Jordan Faisal Al-Fayez ya jaddada a ranar Juma’a cewa: Ana daukar kasarsa a matsayin ginshikin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai cewa; Duk wani hargitsin da zai iya faruwa a kasar, zai shafi kasashen yankin baki daya, yana mai jaddada cewa: Kasashen yamma, musamman Amurka, suna da cikakkiyar masaniya game da wannan lamari.
Al-Fayez ya bayyana cewa, a cikin hirarsa da tashar talabijin ta masarautar Jordan kan manyan kalubale da kasarsa ta fuskanta a baya, amma ta yi galaba a kansu da karfi da kuma tsayin daka, tare da dogaro da muhimman abubuwa, wadanda mafi muhimmancinsu su ne tsaro da zaman lafiyarta, yana mai cewa, diflomasiyyar kasar Jordan tana da babban karfin wajen samar da daidaito, kamar yadda sarkin Jordan Abdallah na biyu ya yi nasara a fagen gudanar da kyakkyawar alakar kasarsa da kasashen yanki da na kasa da kasa wajen nisanta hatsarori da dama.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
MDD Ta CE Sake Tada Komatsar Tattalin Arzikin Kasar Siriya Zau Dauki Shekaru 50 Nan Gaba
MDD ta bada sanarwan cewa tattalin arzikin kasar Siriya na bukatar shekaru 50 nan gaba kafin ta koma kamar yadda take kafin yakin basasa a kasar.
Tashar talabijan ta Presstv ta nakalato shugaban hukumar UNDP Achim Steiner yana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa hukumar ta ta gudanar da bincike kuma ta gano cewa, rikici da yakin basasa da kuma mamayar kasar da sojojin kasashen yamma suka yiwa kasar, ya sa al-amura sun lalace a kasar, ta yadda idan tana bukatar komawa matsayinta kafin shekara ta 2011 tana bukatar rabin karni kafin hakan ya samu. Wato kasar Siriya ba zata koma kamar yadda take a shekara ta 2011 ba sai nan da shekara 2080.
Tace Siriya tana bukatar zuba jari mai yawa a ko wace shekara kafin ta sami wannan ci gaban. A halin yanzu dai kasha 90% na mutanen kasar Siriya suna rayuwan talaka. Sannan kasha 50% daga cikinsu basa da aikin yi. Sannan tattalin arzikin kasar GDP na kasar yana rabin matsayinsa a shekara ta 2011. Banda tallafi daga kasashen waje kasar Siriya tana bukatar zuba jari mai yawa don komawa kamar yadda take.