Shugabannin Kasashen SADC Da EAC Na Ganawa Kan Rikicin Gabashin DR Congo
Published: 8th, February 2025 GMT
Yau Asabar shugabannin kasashen raya tattalin arzikin kasashen Gabashi da Kudancin Afrika EAC da SADC za su gana a birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniya domin tattauna rikicin gabashin DRC.
Shugaban kasar Kenya, William Ruto, dake jagorantar kungiyar EAC, ya sanar da halartar takwarorinsa na Congo da Rwanda.
Tun da farko a ranar Juma’a, ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun gana domin samun nasarar wannan tattaunawar, inda fadar shugaban kasar ta Kwango ta gabatar da bukatunta da suka hada da : tsagaita bude wuta nan take, janyewar dakarun M23 da na Rwanda daga yankin Congo, da sake bude filin jirgin saman Goma, da mayar da birnin ga hannun halastattun hukumomi.
A ranar Juma’a, a wani taro a Malabo, Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Tsakiya “ta yi Allah wadai da kungiyar M23 da kawarta Ruwanda.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kwana Daya Bayan Kwace Fadar Shugaban Kasa, Sojojin Sudan Sun Kwace Babban Bankin Kasar
A ci gaba da shimfida ikonsu da suke yi a cikin birnin Khartum, sojojin Sudan sun kwace iko da babban bankin kasar, kwana daya bayan da su ka kori dakarun kai daukin gaggawa daga fadar shugaban kasa.
Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya nakalto majiyar sojojin Sudan tana cewa; A yau Asabar sun yi nasarar kwace iko da babban bankin kasar, tare kuma da shimfida ikonsu a cikin wasu yankunan na birnin Khartum.
Kakakin sojan kasar Sudan Nabil Abdullah, ya bayyana cewa; Mun rusa sojoji da kayan aikin abokan gaba. Haka nan kuma Abdullah ya sanar da kwace wasu ma’aikatu da suke a tsakiyar birnin Beirut da su ka kasace a karkashin ikon dakarun kai daukin gaggawa.
Ana zargin rundunar kai daukin gaggawa da tafka laifukan yaki a cikin yankunan da a baya su ka shimfida ikonsu a ciki, har da babban birnin kasar Khartum.