HausaTv:
2025-03-24@00:35:19 GMT

Kasashe 79 Sun Yi Watsi Da Matakin Trump Na Kakabawa Kotun ICC Takunkumi

Published: 8th, February 2025 GMT

Kasashe 79 na duniya sun yi watsi da matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na kakabawa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC takunkumi, suna masu cewa matakin na raunana tsarin dokokin kasa da kasa.

Wadannan kasashen  da suka hada da Canada, Jamus, Faransa, Afirka ta Kudu da kuma Mexico, a wata sanarwar hadin gwiwa na cewa irin wadannan matakan na kara barazanar rashin hukunta masu manyan laifuka.

Har ila yau a cikin sanarwar, kasashen 79 sun jaddada cewa takunkumin da Amurka ta kakabawa kotun ta ICC na iya yin illa ga sirrin bayanan da suka shafi wadanda abin ya shafa, da shaidu da kuma jami’an shari’a, wadanda ‘yan asalin wadannan kasashe ne.

Sanarwar ta zo ne sa’o’i bayan da Trump ya sanya hannu kan wani umarni na zartarwa na sanya takunkumi na kudi da hana biza ga ma’aikatan ICC da iyalansu.

A sanarwar hadin gwiwa da kasashen sun nuna yin nadamar duk wani yunkuri na kawo cikas ga ‘yancin cin gashin kan kotun.

Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Alhamis ya ba da izinin kakaba takunkumin tattalin arziki da tafiye-tafiye kan mutanen da ke aiki kan binciken kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ya shafi ‘yan kasar Amurka ko kawayenta irinsu Isra’ila.

Matakin dai ya zo daidai da ziyarar da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu wanda kotun ICC ke nema ruwa a jallo dangane kan aikata laifukan yaki a zirin Gaza, ke ziyara a Amurka, saidai kotun ta yi ICC, ta ce wannan matakin ba zai katse mata hamzari ba wajen gudanar da aikinta.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Araghchi : Iran za ta mayar da amsa ga wasikar Trump cikin kwanaki masu zuwa

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa ta hanyoyin da suka dace.

Araghchi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kai tsaye a gidan talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB) jiya Alhamis.

Araghchi ya kuma lura cewa a wannan karon, ci gaban ya zo tare da wani yunkuri na diflomasiyya daga Amurkawa, ciki har da wasika da bukatar yin shawarwari.

Ya kuma bayyana cewa manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a bayyane take. “Ba za mu shiga tattaunawa kai tsaye karkashin matsin lamba, barazana, ko karin takunkumi.”

A cewar Araghchi, tilas ne a gudanar da shawarwari bisa daidaito da kuma kyakkyawan yanayi.

Ministan harkokin wajen kasar ya kuma bayyana cewa wasikar “mafi yawan barazana ce,” amma kuma akwai damamaki a ciki.

“Mun yi nazari sosai kan dukkan bangarorin wasikar, tare da yin la’akari da kowane daki-daki sosai,” in ji shi.

A farkon watan Maris ne Trump ya bayyana cewa ya rubuta wasika zuwa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

A karshen watan Fabrairu, Ayatullah Khamenei, a wata ganawa da jami’an sojin sama a Tehran, ya bayyana cewa bai ga amfanin tattaunawa da Amurka saboda ba zata warware matsaloli ba.

Kalaman nasa sun zo ne sa’o’i bayan da gwamnatin ta Trump ta kakaba wa Iran takunkumai da Trump ya bayayana  da “mafi girman matsin lamba” kan Iran.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wakilin Sin Ya Yi Bayani Game Da Tunanin Sin Kan Kare Hakkin Dan Adam Da Kin Amincewa Da Siyasantar Da Hakkin Dan Adam
  •  Haaretz: Sojojin Isra’ila Suna Kan Shirya Kai Wa Gaza Hari Ta Kasa
  •  Amurka: Turmp Yana Son Yin Yarjejeniya Ne Da Iran Ba Yaki Ba!
  • Trump Ya Bayyana Dalilin Rufe Gidan Rediyon Muryar Amurka
  • Najeriya: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Zargin Kisan Kiristoci A Kasar
  • Kotun Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha
  • Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP
  • Araghchi : Iran za ta mayar da amsa ga wasikar Trump cikin kwanaki masu zuwa
  • Zargin Kisan Kiristoci A Nijeriya: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Rahoton Amurka
  • Kwankwaso ya yi Allah-wadai da ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas