Amurka ta dakatar da bai wa Afirka ta Kudu tallafi
Published: 8th, February 2025 GMT
Gwamnatin Amurka ta sanar da janye tallafin da take bai wa Afirka ta Kudu yayin da alaƙa tsakanin ƙasashen biyu ta lalace a dalilin dokar karɓe gonakin fararen fata da Shugaba Cyril Ramaphosa ya amince da ita.
Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta katse duk wani tallafin da take ba wa Afirka ta Kudu ciki har da na kuɗi a wani mataki na nuna adawa da dokar kwace filayen noma da Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar ya rattabawa hannu.
Shugaba Trump ya ce Amurka ba za ta taimaka wa gwamnatin Pretoria ba, duba da yadda take ci gaba da take haƙƙin ɗan Adam, da kuma yi wa siyasar Amurka ta ƙetare karan tsaye, inda ya soki zargin Isra’ila da aikata laififukan yaƙin da Afirka ta Kudun ta yi a baya, da ma hulɗarta da Iran a wani ƙudirin da ya sakawa hannu a ranar Juma’a.
Sai dai tun a gabanin matakin na shugaban Trump ya soma aiki, a wani jawabinsa, Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudun ya ce kasarsa ba za ta kawar da ido ga duk wata barazana ba.
Tun farkon wannan wata na Fabrairu ne Donald Trump ya ce zai yanke duk wasu kuɗaɗe da Amurka ke bai wa Afirka ta Kudu har sai an kammala cikakken bincike kan matakin gwamnatin ƙasar na ƙwace filaye mallakar fararen fata ba bisa ƙa’ida ba.
Barazanar na zuwa ne yayin da a ƙarshen watan Janairun da ya gabata Shugaba Ramaphosa ya ƙaddamar da dokar da ta bai wa gwamnati damar ƙwace wasu filaye galibi mallakin fararen fata ba tare da biyan diyya ba a wani mataki na samar da daidaito da kuma adalci ga ’yan kasar.
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta bayyana matakin a matsayin wani yunƙuri na gyaran kura-kurai na rashin daidaito da ƙasar ta gada daga Turawan mulkin mallakar na Birtaniya.
Sai dai wannan mataki ya gamu da suka daga masu ra’ayin mazan jiya ciki har da attajirin nan Elon Musk ɗan asalin Afrika ta Kudu wanda ke da kusanci da shugaba Donald Trump.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: wa Afirka ta Kudu
এছাড়াও পড়ুন:
Rigima: Mawaƙi Portable ya kwana a hannun ’yan sanda
’Yan sanda sun kama shahararren mawaƙin zamani a Najeriya Habeeb Okikiola Badmus, wanda aka fi sani da Portable, bayan ƙazancewar rikicinsa da fitaccen ƙwararren mawakin Fuji, Okunola Saheed “Osupa.”
A ranar Lahadi da dare ne ’yan sanda daga Jihar Kwara suka yi takakkiya suka kamo Portable mai waƙar “Zazu Zeh” a garin Abeokuta, Jihar Ogun
Kakakin ’yan sanda na Jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ya ce an kama Portable bayan samun takardar ƙorafin da Osupa ya aike ɗauke da jerin manyan zarge-zarge da yake yi wa mawakin na “Zazu Zeh,” na ɓata suna, barazanar kisa, tunzura jama’a, zubar da da mutum da gangan, neman tayar da fitina, da kuma amfani da zagi da munanan kalamai.
“Saboda girman waɗannan zarge-zarge da kuma ingantattun shaidun da aka gabatar, rundunar ta samu sammacin kame daga Kotun Majiatare da ke zamanta a Ilorin, inda jami’anmu suka je Abeokuta, suka kamo wanda ake zargin suka kawo shi Ilorin domin ci gaba da bincike.”
Jami’in ya ce da kawo Portable jihar Kwara, nan take aka fara yi masa Portable tambayoyi da ɗaukar bayanansa a gaban lauyoyi daga bangarorin biyu.
Ya tabbatar da cewa Portable zai ci gaba da kasancewa a tsare kuma nan ba da komawa ba za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Rigimar mai zafi, tsakanin Portable da Osupa, ta samo asali ne daga rashin jituwa kan keta haƙƙin mallakar waƙa. Wannan rashin jituwa ta ɓarke ne a bainar jama’a lokacin da Portable ya yi amfani da zagi ga fitaccen mawakin na Fuji mai shekaru 55 a wani bidiyo da ya yaɗu, wanda ya jawo caccaka a kafafen sada zumunta.
A cikin bidiyo, Portable ya bayyana cewa, “Kuɗi ne ya jawo faɗan!” yana ƙoƙarin bayyana ɓacin ransa. Ya ce “Raina ya ɓaci ne saboda ina so a ba ni kuɗina, kuma na ji suna ƙoƙarin sauke waƙar.”
Bayan shan caccaka daga bisani ya saki wani bidiyo yana neman afuwar Osupa cikin girmamawa. Ya ce, “Sarki Saheed Osupa, babana, don Allah kada ka yi fushi. Ka ɗauke ni kamar ɗanka ka horar da ni.”
A wani yanayi mai ban mamaki kuma, Portable ya nuna cewa rigimar tasu wani salon neman magoya baya ne, har ma ya nemi a ba shi damar gudanar da wasanni. “Dukkanmu muna tallata kanmu… don Allah a ba ni aiki.”
Sai dai, Saheed Osupa ya yi watsi da neman afuwar a matsayin wanda bai isa ba, yana mai cewa dole Portable ya samu sakamakon abin da ya aikata.
Ƙi amincewar tasa ba ta yi wa Portable daɗi ba, har ya ƙi janyewa, inda a ƙarshe ya kai ga matakin da Osupa ya ɗauka na shigar da ƙara ga hukumar ’yan sanda.
Yanzu, duniyar nishaɗi ta zura ido tana kallon yadda za a ƙare a wannan rikici manyan mawaka da ya tashi daga kafafen sada zumunta zuwa zauren kotu.
Shin Portable zai fuskanci cikakken hukuncin doka bisa ga zarge-zargen da ake yi masa, ko kuwa za a samu sasanci ne?