Hukuma mai kula da samar da magungunan HIV/AIDS ko (UNAISD) ta MDD ta bada sanarwan cewa mai yuwa mutane kimani miliyon 6 ne zasu mutu a duk fadin duniya a cikin shekaru 4 masu zuwa saboda rashin samun tallafin Amurka a cikin shirin.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayyana cewa, a ranarsa ta farko na kama aiki a matsayin shugaban kasan Amurka, ya dakatar da dukkan tallafin da Amurka take bayarwa a duniya na tsawon kwanaki 90.

Labarin ya nakalto shugaban shirin samar da magunguna HIV/AIDS Christine Stegling tana cewa, duk tare da cewa Amurka ta ci gaba da tallafawa HIV/AIDS na wucin gadi, amma suna ganin cewa da wuya hakan ya ci gaba don tun yanzu wasu al-amura sun fara tsayawa. Mai yuwa kome zai lalace nan gaba.

Stegling ta ce idan gwamnatin Amurka bata ci gaba da bada tallafi ga bangaren PEPFAR tsakanin shekara 2025-29 ba to kuwa yawan mace-mace saboda cutar Aids da HIV zai karu da kashi 400%. Wanda ya nuna cewa mutane kimani miliyon 6.3 ne zasu mutu a cikin wannan lokaci. Banda haka duk wani dakatarwa na tallafin sai ya shafi shirin gaba daya a duniya.

Ta ce a kwai mutane kimani 5000 suna aiki wa hukumar UNAIDS a kasar Habasha kadai, dakatar da tallafin yana nufin sun rasa ayyukansu. Sannan hukumar da aiki a kasashe 80 a duniya tare da tallafin daga kasashen duniya amma rabon Amurka ya fi yawa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran da UAE sun kirayi Isra’ila da Amurka da su kawo karshen hare-harensu a Gaza da Yemen

Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bayyana matukar damuwarsu kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sake dawo da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza da kuma hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen.

A wata tattaunawa ta wayar tarho a wannan Juma’a, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na UAE  Abdullah bin Zayed Al Nahyan, sun tattauna batutuwan da suka shafi yankin, musamman ma ayyukan wuce gona da iri na Isra’ila a Gaza da kuma hare-haren Amurka a Yemen.

Araghchi ya yi kakkausar suka kan kisan gillar da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi wa daruruwan Falasdinawa  da ba su ji ba ba su gani ba tun daga ranar Talata, yana mai jaddada cewa yin hakan saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ne da aka rattaba hannu a kansa.

Ya kuma yi Allah wadai da hare-haren da sojojin Amurka ke ci gaba da kai wa kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mata da kananan yara da dama, tare da lalata muhimman ababen more rayuwa na yankin, da kuma jefa mutane cikin kangin talauci da yunwa.

Araghchi ya kara da cewa, laifuffukan da gwamnatin yahudawan sahyoniya ke aikatawa a Gaza da kuma harin da Amurka ta kai kan kasar Yaman na bukatar daukar matakin gaggawa da hadin gwiwa daga kasashen yankin da kum akasashen musulmi, domin dakatar da wannan ta’addanci da ke  ci gaba da kawo rashin tsaro a duk fadin yankin gabas ta tsakiya.

A nasa bangaren, Ministan kasar UAE Abdullah bin Zayed ya bayyana matukar damuwarsa kan tabarbarewar al’amura a yankin, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin damuwa matuka.

Ya jaddada bukatar ci gaba da tuntubar juna tsakanin kasashen yankin domin hana ci gaba da tabarbarewar zaman lafiya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun zafafa kai hare-hare ta sama da kuma ta kasa a zirin Gaza tun daga ranar Talata, inda suke  kai hari kan wuraren zaman jama’a da hakan ya hada da wuraren da aka tsugunnar da dubban mutane da suka rasa muhallansu da kuma gidaje, gami da asibitoci, tare da hana duk wasu ayyuka na jin kai ko ceton jama’a ko kai daukin gaggawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Masanin Amurka: Matakan Kariyar Cinikayya Da Amurka Ke Aiwatarwa Babban Kuskure Ne
  • Fiye Da Dalibai 4,200 Suka Amfana Da Tallafin Ilimi Na Sanata Solomon Adeola
  • Hikimar Gwamnatin Jihar Jigawa Na Kaddamar Da Shirin Gina Rijiyoyin Burtsatsan Noman Rani
  •  “Yan Ta’adda Sun Kai Hari Akan Masu Salla A Jamhuriyar Nijar
  • Ranar Mata Ta Duniya: NPA Ta Mayar Da Hankali Wajen Kare ‘Yancin Mata –Dantsoho
  • Trump Ya Bayyana Dalilin Rufe Gidan Rediyon Muryar Amurka
  • Iran da UAE sun kirayi Isra’ila da Amurka da su kawo karshen hare-harensu a Gaza da Yemen
  • Cibiya Mai Fafutukar Kare Hakkokin Falasdinawa “Global 195” Ta Shelanta Farautar Sojojin HKI Da Su KaTafka Laifukan Yaki
  • Taƙaddama: An kama wanda ya daɓa wa matarsa ​​wuƙa ta mutu
  • Gaggan Masu Garkuwa Da Mutane 10 Da Kayan Aikinsu Sun Shiga Hannu A Kano