Masu Garkuwa Sun Nemi Fansar Miliyan 250 Kafin Su Saki Tsohon Shugaban NYSC, Janar Tsiga
Published: 8th, February 2025 GMT
Mai magana da yawun rundunar ‘ƴansandan jihar, Abubakar Sadiq ya ce; tuni jami’ansu sun je unguwar da gidan yake amma kafin su karasa tuni ‘ƴan bindigar sun tafi da Janar Tsigan.
Sai dai ya bayyana cewar jami’an tsaro suna aiki ba dare ba rana tare da haɗin guiwa da masu ruwa da tsaki domin kamo ‘yan bindigar.
A wani ci gaban kuma, rundunar ‘ƴansandan jihar ta Katsina ta kama wasu mutane 45 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.
কীওয়ার্ড: Yansanda Garkuwa Janar Tsiga
এছাড়াও পড়ুন:
Duk Da Dokar ‘Yancin Samar Da Abinci: Yara Miliyan 11 Na Fama Da Ƙaranci Abinci A Nijeriya
Rahoton ya bayyana rashin wadataccen abinci mai gina jiki, da wahalhalun tattalin arziki na iya zama ummul-haba’isin muhimman abubuwan da ke haifar da rashin abinci ga yara.
A cikin 2024 kadai, Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce ta yi wa yara sama da 300,000 maganin tamowa, doriyar kashi 25 cikin 100 daga 2023.
Daga cikin wadannan kaso, 75,000 na bukatar kulawar rashin lafiya mai tsanani, yayin da 250,000 aka basu kulawa ta hanyar shirye-shiryen sama musu lafiya a fadin jihohi bakwai: Borno, Bauchi, Katsina, Kano, Sokoto, Zamfara, da Kebbi.
Wakilin kungiyar ta MSF na kasa Dr Simba Tirima ya shaida wa LEADERSHIP cewa kungiyar agajin ta lura da yadda ake samun karuwar masu dauke da cutar, wanda ya zarce shekarun baya a duk cibiyoyin kula da lafiyarsu.
“Rashin abinci mai gina jiki na kara ta’azzara, tare da samun karin yara a wuraren da ake kula da su,” in ji Dr Tirima.
Lamarin dai ya samo asali ne sakamakon abubuwa da dama da suka hada da hauhawar farashin kayan abinci, rashin tsaro da ke shafar ayyukan noma, da kuma bala’in da ya shafi yanayi kamar ambaliyar ruwa, wadanda suka haddasa asarar amfanin gona.
“Idan ba tare da samar da isasshen abinci domin magance hakan ba, za mu sha gwagwarmaya wajen shawo kan magance halin da yara masu fama da tamowa ke ciki yadda ya kamata, wanda zai iya haifar da asarar rayuka,” a gargadin da Dr Tirima ya yi.
MSF ta ce ta fara tara kayan abinci kafin lokacin rashin abinci mai gina jiki ya riske ta musamman a Jihar Bauchi, wanda ke aiki da wurin jinyar mutane a dakunan da ke dauke gadaje 250 da kuma cibiyoyin ciyar da marasa lafiya guda uku.
Duk da haka, kungiyar ta ci gaba da nuna damuwa cewa raguwar kudade ga sauran hukumomin jin kai na iya kara dagula karfin gudanar daaikin,
A don haka, ta yi kira ga gwamnati da ta sa baki cikin gaggawa don magance lamarin, tare da nuna bukatar karfafa ayyukan kiwon lafiya a Wuraren Kula da Lafiya a Matakin Farko, karin kudade don shirye-shiryen samar da abinci mai gina jiki, tare da fadada yakin rigakafin.
“Dole ne hukumomi da abokan hulda su dauki babban mataki don magance matsalar karancin abinci mai gina jiki,” in ji Dokta Tirima.
Tare da karuwar matsalolin rashin abinci mai gina jiki, MSF na fargabar cewa za’a iya samun mummunar matsala a 2025.
kungiyar ta yi gargadin idan ba a dauki matakin gaggawa ba, Arewacin Nijeriya na iya fuskantar matsalar karancin abinci mai gina jiki, wanda hakan na iya haifar da karuwar mace-macen yara.
A cikin dokar ‘yancin cin abinci, kundin tsarin mulkin Nijeriya ya amince da abinci a matsayin wani muhimmin hakki na dan’Adam kuma ya wajabta wa gwamnati ta samar da abinci, mai sauki, mai araha ga dukkan ‘yan Nijeriya.
Duk da haka, aiwatar da manufofin ya kasance mai rauni, kuma babu wata dabarar daukar tsawon lokaci don cimma manufofin doka.
Babban Daraktan Shirin Global Initiative for Food Security and Ecosystem Preservation (GIFSEP), Dr Michael Terunngwa David, ya lura cewa duk da cewa Dokar ta tabbata a gyare-gyaren tsarin mulki da aka sanya hannu a cikin Maris 2023, dokar ba ta da karfi kamar yadda ake aiwatar da ita, kuma aiwatar da ita yana da karfi kamar yadda wayar da kan jama’a ke kewaye da dokar.
“Samar da abincin fa ba wata alfarma bace; hakkin dan’Adam ne na asali. Amma duk da haka, miliyoyin ‘yan Nijeriya suna fama da yunwa, rashin abinci mai gina jiki, da rashin abinci. Dokar wata muhimmiyar manufa ce da ke magance wadannan kalubale ta hanyar tabbatar da samun abinci mai gina jiki, wadataccen abinci, da samunsa a araha ga kowa da kowa. Ya umurci gwamnati da ta dauki nauyin aiwatar da matakan da za su samar da abinci, wanda ya dace da kowane dan kasa.
Dokta David ya bayyana rashin tsaro a matsayin kalubale, inda ya ce rigingimu sun tilastawa manoma barin gonakinsu, lamarin da ya sa samar da abinci ke da wuya.
Misali, kashi 40 cikin 100 na gonakin Jihar Benuwe a yanzu ba a noma su saboda rashin tsaro.
A shekarar 2021, Nijeriya ta samar da ton miliyan 203 na abinci, amma duk da haka yunwa na ci gaba da wanzuwa saboda rashin tsarin rarrabawa da adanawa. Dakta David ya lura cewa adadin abincin da kasar ke bukata a kowace rana ga kowane mutum ya kai kilogiram 2.5.
Tare da mutane miliyan 230, al’umma na bukatar ton 575,000 na abinci a kowace rana ko kuma ton miliyan 210 a kowace shekara.
Har ila yau, Farfesa G. B. Ayoola, wanda ya kafa Gidauniyar Noma Da Kayan Aiki (FIF) kuma shugaban Voices for Food Security (VFS), ya nanata cewa lissafin gwamnati yana da mahimmanci don tabbatar da ganin Hakkin Abinci ya tsaya da kafarsa.
A cewarsa, a bisa tsari, dokar ta tilasta wa masu tsara manufofin mutunta hakkin abinci ta hanyar tabbatar da rashin kawo cikas ga manufofin, da suka hada da kare hakkin abinci daga ayyuka masu cutarwa daga kungiyoyin gwamnati da masu zaman kansu da kuma tabbatar da hakkin saar da abinci ta hanyar taimaka wa masu rauni kai tsaye.
Ya ce rashin kiyaye wadannan wajibai na iya haifar da sakamakon shari’a, duk da haka aiwatar da aiki yana da rauni.
Tsakanin watan Yuni da Agusta 2025, ana sa ran kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 30.6 a fadin jihohi 26 da Birnin Tarayya Abuja za su fuskanci karancin abinci, kamar yadda binciken Cadre Harmonisé (CH) na Fabrairu-Maris ya nuna.
Yayin da aka samu ragi daga miliyan 33.1 da aka yi hasashen a watan Nuwamba na 2024, masana sun yi gargadin cewa har yanzu miliyoyin mutane za su fuskanci wawakeken givin abinci sakamakon rikice-rikicen da ke haifar da rarrabuwar kawuna, bala’o’in yanayi, da matsin tattalin arziki.
Lamarin dai ya fi shafar yara da mata masu juna biyu, inda yara ‘yan kasa da shekaru biyar miliyan 5.4 da mata masu ciki da masu shayarwa 787,000 ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki. Wannan yana nuna karuwar kashi 23 cikin 100 daga alkaluman baya.
Wani abin ban tsoro kuma, yara miliyan 3.7 a yankin Arewa maso Gabas na fama da tamowa, suna kokawa da tashe-tashen hankula, da kuma karancin abinci, a cewar Hukumar Abinci da Aikin Noma ta FAO.
Jihohin da lamarin ya fi shafa sun hada da Yobe, Sokoto, Zamfara, da Katsina, inda matsalar rashin abinci mai gina jiki ta kai mataki na hudu a (matakin gaggawa) a wasu kananan Hukumomin. Maiduguri, Jere, Mobbar, Nganzai, da Mashi na daga cikin wuraren da ke fuskantar matsalar karancin abinci mai gina jiki, inda yara da mata 178,000 daga al’ummomin da lamarin ya shafa suka fi fuskantar hadari.
A halin da ake ciki, UNICEF ta yi kira da a dauki matakan da suka dace don kawo karshen karancin abinci na yara, ciki har da karfafa tsarin abinci don samar da abinci mai gina jiki mafi sauki kuma mai araha, fadada ayyukan abinci mai gina jiki don rigakafi da magance matsalar rashin abinci mai gina jiki da inganta shirye-shiryen kare rayuwar jama’a, gami da mika kudade da taimakon abinci ga iyalai masu rauni.
Asusun Kula da Abinci na Yara (CNF) shiri ne da UNICEF ke jagoranta da aka tsara don hanawa, ganowa, da kuma magance matsanancin karanci da rashin abinci mai gina jiki. Ana fatan yaran da ke fama da tamowa za su sami taimako ta hanyar CNF.
CNF, wanda aka kafa a bara tare da goyon bayan abokanan hadin gwiwa da yawa, hanya ce samar da kudi da ke karfafa zuba jari a cikin gida a cikin abinci mai gina jiki na yara.
UNICEF ta bukaci gwamnatoci, masu ba da taimako, da abokan huldar kudi da su kara tallafa wa CNF tare da ba da fifikon ayyukan da za a yi don magance matsalar karancin abinci mai gina jiki. Ya ce karuwar saka hannun jari a shirye-shiryen abinci mai gina jiki yana da matukar muhimmanci don tabbatar da ganin yara sun sami muhimman abubuwan gina jiki da suke bukata don girma da bunkasa.
Yayin da Nijeriya ke cikin kasashe 20 da suka fi fama da matsanancin karancin abinci, masu ruwa da tsaki sun jaddada cewa idan ba a dauki matakan gaggawa ba, lamarin na iya rikidewa zuwa wani bala’in jin kai.
Sai dai Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta Tarayya ta ce tana aiwatar da wasu tsare-tsare na ciyar da abinci tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki.
Darakta kuma shugabar sashen kula da abinci mai gina jiki a ma’aikatar, Misis Ladidi Bako-Aiyegbusi, ta jaddada bukatar inganta kasafin kudin abinci mai gina jiki, inda ta bayyana cewa zuba jari a fannin abinci mai gina jiki zai hana sama da miliyan 10 kamuwa da cutar gudawa da ciwon huhu, da kuma mutuwar yara kusan 220,000 a duk shekara a kasar, da muhimmiyar gudunmawa wajen rage mace-macen yara ‘yan kasa da shekaru 5 gaba daya.
A cewarta, zuba jari kan ayyukan samar da abinci mai gina jiki a duk fadin kasar na da yiwuwar ceto Dala miliyan 22 na kudaden kula da lafiya da suka shafi matsalar karancin abinci mai gina jiki.
Don haka an bukaci ‘yan majalisar da su tabbatar da cewa an ware wa abinci mai gina jiki kudi ga ma’aikatu da sassan da ke da sauran isar da shirye-shirye na musamman kan abinci mai gina jiki ta hanyar tabbatar da fitar da isassun kudi a kan lokaci, lura da yadda ake kashe kudin, da kuma tabbatar da an kashe kashe yadda ya kamata.
Ta kuma bukaci ‘yan majalisar da su tsara wata cikakkiyar muhawara ta shekara-shekara kan yanay
in abinci mai gina jiki a mazavunsu na tarayya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp