Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja
Published: 8th, February 2025 GMT
Kasuwannin hatsi a Jihar Neja suna fama da matsalar faduwar farashi amfanin gona, sakamakon shigo da hatsi daga kasashen makwabta kamar Chadi da Ghana da Jamhuriyar Benin da Burkina Faso.
Wannan yanayi ya haifar da yawan kaya, wanda ke shafar manoma da ‘yan kasuwa da masu samar da kayayyaki a yankin.
Manoman da suka tara hatsi don cin riba sun shiga damuwa saboda shaguna da kasuwanni sun cika da buhunhunan hatsi, amma babu masaya.
Wasu daga cikin manoma da ’yan kasuwa sun bayyana wa wakilinmu cewa, wannan yanayi ya rikitar da harkar kasuwanci, inda suke fama da karancin riba saboda farashin hatsi da sauran kayan gona irin su wake da waken soya da dawa da masara da gero na ci gaba da sauka warwas.
Wannan matsalar ta samo asali ne daga yadda wasu kamfanonin sarrafa abinci a Nijeriya ke siyan hatsi daga kasashen makwabta saboda farashi mai rahusa.
Amfanin gona ya yi kyau a wadannan kasashe, manoman suna da damar siyar da hatsinsu ga kamfanoni a Nijeriya a farashin da ya fi araha.
Wani dan kasuwa daga Minna ya koka da cewa, “mun yi tsammanin farashi zai tashi, muka tara hatsi don mu siyar a farashi mai tsada daga baya.
Sai dai shigowar hatsi daga kasashen waje kwatsam ya sa ba za mu iya siyar da kayayyakinmu ba tare da asara ba.”
Masu tara hatsi sun bayyana damuwarsu kan wannan sauyin farashi, inda wasu suka ce shagunan da suka cika da hatsi ba sa samun masu siye.
Idan wannan hali ya ci gaba, ‘yan kasuwa da dama da ke fatan samun riba daga tara hatsi na iya gamuwa da babbar asara.
A gefe guda, masu saye suna jin dadi saboda saukar farashin, amma manoma na korafin cewa wannan raguwar farashi barazana ce ga rayuwarsu da sana’arsu.
Shugaban Kungiyar Manoma da Masu Samar da Hatsi ta Nijeriya, reshen Karamar Hukumar Shiroro, Hassan Ango Abdullahi, ya tabbatar da wannan hali yayin wata tattaunawa a kasuwar Gwada.
Ya ce, “kamfanoni sun fi son siyan hatsi daga Chadi da Ghana da sauran kasashen waje saboda farashinsu yana da sauki.
“Misali, mun sayi wake da waken soya kan farashin Naira 103,000 da Naira 105,000 a kan kowane buhu mai nauyin kilo 100 lokacin girbi, amma yanzu farashin ya sauka zuwa Naira 80,000.
“Masu tara hatsi da suka saya a farashi mai tsada suna cikin wahala yanzu.”
Ya kara da cewa “Shekarar da ta gabata, kamfanoni suna ta siyan masara daga hannunmu, amma wannan shekarar sun daina siyan kayayyaki daga Nijeriya gaba ɗaya saboda sun fi samun rahusa daga kasashen makwabta.
“Muna da buhunan masara masu yawa a ajiye, amma babu masu saye.”
Abdullahi ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da su tallafa wa manoma ta hanyar samar da kayan aikin gona masu saukin farashi, irin su taki da sinadaran kashe kwari da injunan noma, domin bunkasa harkar noma.
Ya ce, idan gwamnati ta tallafa wa manoma, farashin abinci zai ci gaba da yin kasa, kuma kowa zai amfana.
Ya kuma bukaci Gwamnatin Jihar Neja da ta samar da wuraren siyar da taki a kowane yanki domin saukaka wa manoma daga karkara.
Ya ce, “ba daidai ba ne manoma daga karkara su yi doguwar tafiya zuwa Minna don sayan taki.
“Ya kamata a samar da wuraren sayar da taki a kowace mazaba.”
A daya bangaren, wasu ba su yarda cewa wannan matsalar raguwar farashi ta yi illa ba.
Sani Usman, Sakataren Kungiyar Manoma da Masu Samar da Hatsi ta Amana, reshen Karamar Hukumar Shiroro, ya ce, “manoma ba sa samun asara. Ko da taki yana kan farashin Naira 40,000 kowane buhu, masara ana sayar da ita a kan Naira 52,000, yayin da waken soya yake kan Naira 80,000.
“Idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, lokacin da masara take kan Naira 30,000 a kan kowane buhu.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Neja Ƙetare
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Bauchi Ta Ɗage Hawan Daushe Na Sallar Bana
Sai dai, bisa ladabi da girmamawa ga masarautu, Gwamna Bala Muhammad ya amince da roƙon ɗage Hawan Daushe.
Duk da haka, gwamnatin ta nuna damuwarta kan yadda ba a tuntuɓe ta ba kafin yanke wannan shawara.
Ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da aiki tare da sarakuna domin kyautata zamantakewa da ci gaban jihar.
Ga mutanen da wannan ɗagewa ta shafa, gwamnati ta fahimci damuwarsu, amma ta yi alƙawarin ɗaukar matakan da suka dace a nan gaba don kauce wa irin wannan matsala.
Gwamnan ya yi fatan jama’a za su yi bikin Sallah cikin lumana da farin ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp