Watanni 2 Da Sauke Baffa Bichi, An Nada Umar Farouk Mukamin Sakataren Gwamnatin Kano
Published: 9th, February 2025 GMT
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Kano.
Nadin na kunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a yammacin ranar Asabar 08, ga Febarairun 2025.
Dalilan Da Suka Sa Gwamnan Kano Sallamar SSG Da Wasu Kwamishinoni 5 Gwamnan Kano Ya Karyata Jita-jitar Rikicinsa Da Sakataren Gwamnatin JiharNadin Na Ibrahim zai fara aiki ne daga ranar Litinin mai zuwa 10, ga Febarairun 2025.
Sanarwar nadin ta bayyana cewa an zabi, Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar saboda shafe sama da shekaru talatin ya na aikin gwamnati da tarin kwarewar aiki da yake da ita a hukumomi da ma’aikatu daban-daban na gwamnati da ya yi aiki, don cimma muradin gwamnati mai ci na ciyar da jihar Kano gaba.
Nadin na Umar Farouk Ibrahim, na zuwa ne watanni biyu bayan sauke tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Dr. Baffa Abdullahi Bichi daga muƙaminsa a sakamakon dalilan rashin lafiya, kamar yadda sanarwar sauke shi ta bayyana haka a baya. Sai dai duk da haka wasu na ganin kamar akwai wasu dalilai na siyasa saɓanin wanda aka bayyana na sauke Baffa Bichin.
কীওয়ার্ড: Gwamnan Kano Sakataren Gwamnatin Kano Umar Farouk Ibrahim Sakataren Gwamnatin Gwamnatin Kano
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da Harin Jihar Filato
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan harin da aka kai Jihar Filato wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40.
A cikin wata sanarwa, Shugaban kasa ya la’anci wannan tashin hankali tare da mika ta’aziyyarsa ga Gwamna Caleb Mutfwang, Gwamnatin Jihar, da al’ummar Filato.
Sanarwar da Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan Harkokin Yada Labarai Mista Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, ta bukaci Gwamnan da ya nuna cikakken ikonsa wajen warware rikicin da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin soyayya da hadin kai a maimakon bambancin addini da kabila.
Ya bukaci shugabannin al’umma, da na addinai, da ma na siyasa a ciki da wajen jihar, da su hada kai domin kawo karshen ramuwar gayya da rikice-rikicen da suka jima suna addabar al’umma.
“Ya zaman wajibi a kawo karshen rikicin da ke faruwa tsakanin al’umma a Jihar Filato wanda ya samo asali daga rashin fahimta tsakanin kabilu da addinai daban-daban.” In ji Shugaba Tinubu.
“Na umarci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan wannan rikici, da gano wadanda ke da hannu a shirya wadannan ayyukan tashin hankali. Ba za mu amince da wannan barna da hare-haren ramuwar gayya ba. Ya isa haka.
Ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ba Gwamna Mutfwang da Gwamnatin Jihar Filato goyon baya wajen karfafa tattaunawa, inganta zaman tare, da tabbatar da adalci don magance wannan rikici har abada.
Daga Bello Wakili