Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano
Published: 9th, February 2025 GMT
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Kano.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yammacin ranar Asabar.
Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja Ya yi wa kansa keji don daina shan sigariSanarwar ta ce naɗin sabon Sakataren Gwamnatin zai fara aiki ne a hukumance daga ranar Litinin mai zuwa 10, ga Fabarairun 2025.
Sanarwar ta ce an naɗa sabon Sakataren Gwamnatin wanda ya shafe sama da shekaru talatin yana aikin gwamnati la’akari da ƙwarewar aiki da yake da ita a hukumomi da ma’aikatu daban-daban na wajen ganin an cimma muradin gwamnati mai ci na ciyar da Jihar Kano gaba.
Naɗin na Umar Farouk Ibrahim na zuwa ne watanni biyu bayan sauke tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Dokta Baffa Abdullahi Bichi daga muƙamin a sakamakon dalilan rashin lafiya, kamar yadda sanarwar sauke shi ta bayyana haka a baya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sakataren Gwamnatin Kano Umar Farouq Ibrahim sabon Sakataren Gwamnatin Gwamnatin Kano
এছাড়াও পড়ুন:
Fursunoni 12 Sun Tsere Daga Gidan Yari A Jihar Kogi
Gwamnatin jihar ta yi kira ga al’umma da su ba da hadin kai ga jami’an tsaro ta hanyar bayar da bayanai da za su taimaka wajen kamo sauran fursunonin da suka tsere.
Haka kuma, an buƙaci dangin waɗanda suka tsere da su mika kansu ga hukuma domin guje wa hukunci mai tsanani.
Wannan ba shi ne karo na farko da ake samun irin wannan matsala ba, domin a baya an samu fursunoni sun tsere daga gidajen yari daban-daban a Nijeriya.
Hakan na nuni da buƙatar ƙara tsaurara matakan tsaro a gidajen gyaran hali domin hana faruwar irin haka a gaba.
A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da bincike tare da ƙoƙarin kamo sauran fursunonin da suka tsere domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp