Iran Ta Kira Taron Gaggawa Na Ministocin OIC, Kan Shirin Trump Na Kwace Gaza
Published: 9th, February 2025 GMT
Iran ta bukaci taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta OIC, game da shirin shugaba Donald Trump na Amurka na kwace Gaza da kuma korar al’ummar Zirin.
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa haramtaccen shirin” na shugaban kasar Amurka kan Gaza ya gamu da kakkausan ra’ayi daga kasashe daban-daban, inda ya yi kira da a gudanar da taron gaggawa na ministocin kungiyar ta OIC domin tattaunawa da yanke shawara kan wannan batu.
A wata tattaunawa daban daban ta wayar tarho da wasu takwarorinsa a yammacin jiya Asabar ministan harkokin wajen na Iran Sayyid Abbas Araghchi da takwaransa na kasar Masar Badr Abdel-Aty, Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da shirin hadin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila na tilastawa mutanen Gaza gudun hijira a yankin da aka yi wa kawanya.
Mista Araghchi ya ce dole ne dukkan al’ummar musulmi su tashi tsaye wajen dakile wannan makirci.
Araghchi yakuma tattauna da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi OIC Hussein Ibrahim Taha ta wayar tarho.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya yi kira da a gudanar da wani taro na musamman na kungiyar domin daukar kwararan matakai masu inganci na kare hakkin Falasdinawa.
Ya kuma bayyana babban nauyin da ke wuyan kasashen musulmi na tallafawa Falasdinawa da ake zalunta, musamman hakkinsu na cin gashin kansu.
“Shirin tilastawa Falasdinawa kaura daga Gaza ba wa kawai babban laifi ba ne da ke da alaka da ‘kisan kare dangi,’ barazana ne ga tsaron yankin da kuma duniya baki daya,” in ji shi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Ta Jaddada Aniyar Aiwatar Da Sakamakon Taron FOCAC Na Beijing
Kazalika, mahalarta taron sun jaddada muhimmancin inganta samar da ayyukan yi, da karfafa tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar ’yan Najeriya, ta hanyar kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp