‘Yan Asalin Nijeriya Da Ke Buga Wa Kasashen Turai Wasa
Published: 9th, February 2025 GMT
Ga wasu manyan ‘yan kwallo da tauraronsu ke haskawa a duniya, wadanda asalin ‘yan Nijeriya ne, wato ko dai iyayensu baki daya ko wani daga cikin iyayen ‘yan Nijeriya ne.
Jamal Musiala (Jamus)
Matashin dan wasa Jamal Musiala, wanda aka haifa a ranar 26 ga Fabrairun shekarar 2003, fitaccen dan kwallon kasar Jamus ne da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta Jamus din kuma yana cikin matasan ‘yan kwallon da suke tashe a duniya a yanzu saboda ba za ka lissafa matasan ‘yan wasa guda biyar ba a duniya ba tare da ka saka sunansa ba.
Matashi Musiala ya wakilci kasar Ingila a kwallon matakin yara, kafin ya koma Jamus da buga wasa sannan kuma ya lashe kofuna da dama irin su gasar Bundesliga guda hudu da sauran kofuna, sannan ya samu kyaututtuka da dama tun daga lokacin da kungiyar Bayer Munchen ta fara saka shi a wasa tun yana dan shekara 17 a duniya.
Karim Adeyemi
Karim-Dabid Adeyemi wanda aka haifa a ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2002, dan wasan Jamus ne da kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund. An haifi dan wasan a birnin Munich, wanda mahaifinsa asalin dan Nijeriya ne, amma mahaifiyarsa ‘yar Romaniya ne kuma a kwanakin baya danwasan da ke buga wasa a Dortmund da ke Jamus ya kusa komawa kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta kasar Italiya kafin daga baya cinikin ya rushe bayan yaki amincewa da tafiya.
A baya-bayan nan Karim Adeyemi ya bude wata gidauniya a Nijeriya kuma ya bude gidauniyar ne a birnin Ibadan da ke Jiyar Oyo a kudu maso yammacin kasar nan, inda ya ce gidauniyar za ta mayar da hankali kan koyar da wasanni da ilimi, sannan a lokacin da ya ziyarci Nijeriya, Adeyemi ya shaida wa manema labarai cewa nan gaba yana tunanin komawa buga wasa a gasar Premier ta Ingila.
Michael Olise
Shima matashin dan wasan an haife shi ne a ranar 12 ga Disamban 2001, dan kwallo da a yanzu yake wakiltar Faransa kuma yake buga wasa a kungiyar Bayern Munich ta kasar Jamus. Olise wanda ya koma Jamus da buga wasa daga kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace asalin mahaifinsa dan Nijeriya ne, amma mahaifiyarsa ‘yar Aljeriya ce mazauniyar Faransa. Kuma yanzu haka yana daya daga cikin matasan ‘yan wasan da tauraruwarsu take haskawa a nahiyar Turai.
Noni Madueke
Shi dai asalin sunansa shi ne Chukwunonso Tristan “Noni” Madueke, kuma an haife shi ne a ranar 10 ga Maris a shekarar 2002 kuma yanzu yana wakiltar kasar Ingila ne, sannan yana buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta Ingila kuma shima asalin mahaifinsa dan Nijeriya, amma shi a Ingila aka haife shi, sannan itama mahaifiyarsa ‘yar asalin kasar Ingila ce.
Bukayo Saka
Bukayo Saka fitaccen dan kwallo ne da a yanzu yake jan zarensa a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke Ingila kuma danwasan wanda asalin sunansa Bukayo Ayoyinka Temidayo Saka, iyayensa Adenike da Yomi Saka duka ‘yan Nijeriya ne kuma a baya ya sha bayyana cewa yana alfahari da kasancewarsa dan Nijeriya, kuma ya kan ziyarci kasar nan a wasu lokutan.
Ethan Chidiebere Nwaneri
Ethan Chidiebere Nwaneri wanda aka haifa a ranar 21 ga watan Maris na 2007, matashin danwasa ne da a yanzu yake tashe a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, kuma an haife shi ne a arewacin Landan, amma iyayensa ‘yan Nijeriya ne, sannan ya wakilci tawagar ‘yanwasan kasa da shekara 16 da 17 da 19 sai dai har yanzu ba wakilci babbar tawagar Ingila ba, wanda hakan ya sa za a iya gayyatarsa Nijeriya.
Joshua Orobosa Zirkzee
Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bologna dake kasar Italiya, Joshua Orobosa Zirkzee wanda aka haifa a ranar 22 ga Mayun 2001, dan kwallo ne da yake wakiltar kasar Netherlands, kuma yake buga wasa a yanzu a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta Ingila sanann an haife shi ne a birnin Schiedam, sai dai shi mahaifiyarsa ce ‘yar Nijeriya, amma mahaifinsa dan Netherland ne.
কীওয়ার্ড: a kungiyar kwallon kafa ta wanda aka haifa a ranar yan Nijeriya ne dan Nijeriya buga wasa a
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗanyen Mai Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Ƙaru A Watan Janairun 2025 –OPEC
Sun ci gaba da cewa, tattalin arzikin ya karu zuwa kaso 3.5, a zango na uku a 2024, daga kaso 3.2 a zango na biyu a 2024.
A cewarsu, Nijeriya ta samu wannan nasarar ce, saboda tsaurara tsare-tsaren hada-hadar kudade, inda kuma fannin da bai shafi Man Futur na kasar ba, ya bayar da gagarumar gudunmawa, tare da samar da tsare-tsaren sakuka yin hada-hadar kasuwanci a kasar.
Sun kara da cewa, fannin Mai ya ci gaba da bayar da gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, musamman duba da yadda Matatar Man Fetur ta dangote ke samar da yawan Man a kasar, inda hakan ya kuma daidaita samar da Man da kuma rabar da shi, a cikin farashi mai rahusa.
Sai dai, shekaru da dama da suka gabata yawan samun satar dayen Mai da fasa butun Man da wasu batagari ke yi a kasar, sun janyo koma baya, ga fannin bunkasa tattalin arzikin kasar, wanda hakan, ke ci gaba da zama abin damuwa ga Gwamnatin kasar.
Ko a ranar 2 ga watan Yulin 2024, Kamfanin Albarkatun Man Fetur na kasa NNPC, ya kaddamar da dokar ta baci akan bangaren samar da danyen Mai na kasar.
A cewar Kamfanin, ya yi hakan ne, bisa nufin kara samar da wadataccen danyen Man a kasar da kara yawan ake adanawa.
Kazalika, Gwamnatin Tarayya ta amince da a kashe dala miliyan 21 domin aikin tura Mai daga gidajen mai Mai da ke daukacin yankin Neja Delta, musamman don a samu sukunin sanya ido kan yadda ake samar da danyen Mai da kuma rabar dashi.