Mata Mu Tsaya Da Kafafunmu Kar Mu Tsaya Sai An Bamu – Khadeejah Abdullahi
Published: 9th, February 2025 GMT
A’a ba ni da aure amma in sha Allah ina sa ran yi.
Malama Khadija kina da wata sana’a ne ko kuma karatu kike yi?
Eh ina da Diploma a Cibil Law, sai Degree a Islamic Studies,.kuma ni cikakkiyar ‘yar kasuwa ce,.na Fara sana’a a 2016
Wane irin kasuwanci kike yi ma ana dame-dame kike sayarwa?
Mhm, gaskiya ina kasuwanci da yawa kamar sarrafa dinki, kayan dandano da goge-goge da sarrafa dukiya
Me ya ja hankalinki da har kike sha’awar wannan sana’ar?
Ni dai gaskiya ban yadda da rayuwa akan dogaro da wani ba, rayuwata ita ce, kuma na fi yarda da in samu abu na kaina ba sai na je roko ba ko kuma sai na jira an bani saboda ni ba na son wulakanci kuma na yi amfani da baiwar da Allah ya ba ni ta sana’a.
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?
Ina ga kowace sana’a da nata kalubalen na wahala, a da can baya wurin samun kwastomomi, asarar kudade, ga rashin samun zama, wasu za su ce za su ba da adbance daga baya su ciko amma sam ba su yi.
Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika cimma?
Gaskiya Alhamdulillah, ba abin da zan ce sai godiya ga Allah. Ban taba tunanin a cikin karamin lokaci zan samu kwantiragi din da na samu a yanzu ba a fannin property management. Kuma ta haka na samu damar haduwa da mutanen da ban yi tsammani zan hadu da su ba kai har da wurare daban-daban.
Wane abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?
Ba abin da na fi so kamar in ga an yaba min aikin da na yi shi ya sa na ke ba da dukka ma’ana lokaci, kudadena don ganin na ba da sakamako mai kyau fiye da yadda ake zato. Kuma Alhamdulillah ayyukana suna kyau da taimakon ma’aikatana.
Dame kike so mutane su rika tunawa dake?
Na yi gidauniya a baya YOTD inda na taimaka wa marasa lafiya na samo musu kudin magani, a yanzu ma na canza wa gidauniyar suna ta koma Bisit the sick saboda na maida hankali kan marasa lafiya sosai.
Wace irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?
Addu’ar samun miji da ‘ya’ya nagari da rabuwa da iyaye lafiya
Wane irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
Gaskiya ina samun goyon baya sosai daga iyayena, ‘yan uwa da kuma wanda zan aura a da ya tsaya sosai wajen ganin komai ya tafi daidai
Kawaye fa?
Hahahaha, ai ni ta kowa ce duk inda na shiga ina blending da wuri amma kawaye na sosai ba su da yawa don ni dai sana’a ce kawata amma ina da kawaye biyu zuwa uku haka.
Me kika fi so cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Ni ba mai son kwalliya sosai bace wato na fi son sanya kaya masu sauki wanda ba zai takura min ba kuma ni na ni son atamfa kuma masoyiyar turare ce ni.
A karshe wace irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
Mata mu tsaya da kafafunmu, kar mu jira sai an ba mu kuma roko ba kyau, ka jira an baka yau, gobe an baka jibi ai ba za a bayar ba. Ko auna ka fiya tambaya. Kuma yandu yawanci naza sun fi son auren mai sana’a ko kuma mai yin aiki don kar ki zame musu larura, kuma wasu mazan ganin cewa kina kokarin neman naki zai sa su tallafa miki.
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Yi Wa ‘Yan Majalisar Ƙasa Kiranye
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Mulkin dimokuraɗiyya kamar yadda Hausawa ke cewa ‘yancin ɗan adam.
A lokacin da ta ba ka damar tsayawa don a zaɓe ka kan wani muƙamin, kazalika ta ba ka damar zaɓen wanda kake so ya shugabance ka kuma ya wakilce ka.
Wani abun da dimokuraɗiyyar ta bai wa al’umma dama a kai kuma shi ne na yin kiranye ga wakilan da suka zaɓa musamman idan waɗannan wakilan basa biya musu buƙatun da suka tura su a kai.
Tuni dai al’ummar Kogi ta Tsakiya suka fara kaɗa ƙuri’un kiranye ga Sanata Natasha da suka aike ga Majalisar Dattawa bisa dalilai nasu na ƙashin kan su.
NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen GwamnaShirin Najeriya A Yau na wannan rana zai tattauna ne kan matakai da sharuɗan da ake cikawa don yin kiranye ga ‘yan majalisa.
Domin sauke shirin, latsa nan