Gwamnatin Kano ta dakatar wani fim mai suna Zarmalulu
Published: 9th, February 2025 GMT
Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim da take zargin ya saɓa ka’ida tare da gayyatar dukkannin wanda suka fito a cikinsa domin sauraron ba’asi.
Hukumar tace fina-finai da dab’i ta Kano ce ta dakatar da fim ɗin mai suna Zarmalulu bayan ƙorafin da aka miƙa mata.
Taron Qur’ani: Tsakanin magoya baya da masu kushe Me ya sa ake musayar yawu tsakanin APC da PDP?Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a ranar Asabar, ta ce ana zargin waɗanda suka shirya fim ɗin sun sanya masa suna na baɗala.
“Biyo bayan ƙorafin da Hukumar ta karɓa daga wasu masu kishin Jihar Kano akan wannan fim ɗin, Shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha ya bayyana damuwarsa kan lamarin tare da dakatar da fim ɗin.
“Haka kuma, Abba El-Mustapha ya gayyaci dukkannin wanda suka fito a shirin domin jin ba’asi na yin amfani da ita wannan kalma.”
Bayanai sun ce fim ɗin mai suna “Zarmalulu” ana zarginsa da rashin ma’ana sannan an yi masa laƙabi da wani suna mai kama da na baɗala.
Hukumar ta buƙaci duk waɗanda suka yi ruwa da tsaki a fim ɗin da su bayyana a gaban kwamatin bincike da ta kafa.
Hukumar tace fina-finan na da hurumin dakatar da dukkannin wani fim da bata gamsu da yadda aka shirya shi ba tare da ladaftar da duk wani da ta samu da yin abinda bai kamata a cikin kowane fim ba ko kuma a wajen fim ɗin matsawar ɗan Masana’antar Kannywood ne.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hukumar Tace Fina Finai Jihar Kano kannywood Zarmalulu
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe mutum 10 a wani sabon hari a Filato
Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon harin da wasu mahara suka kai wa al’ummar Ruwi da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos, a Jihar Filato.
Maharan sun kai harin ne a daren ranar Alhamis, inda suka buɗe wuta kan mutanen da suka halarci wata jana’iza da misalin ƙarfe 9:30 na dare.
’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a ZamfaraWani mazaunin yankin ya ce: “Mummunan hari ne. Sun zo kwatsam suka fara harbi. Muna roƙon hukumomin tsaro da su ɗauki mataki don kare al’ummarmu.”
Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da faruwar harin, amma ba ta bayyana adadin waɗanda suka rasu ba.
Kakakin rundunar, DSP Alabo Alfred, ya ce, “Kwamishinan ‘yan sanda ya tura ƙarin jami’an tsaro da kayan aiki don wanzar da zaman lafiya.
“Za mu tabbatar da cewa waɗanda suka aikata wannan aika-aika sun fuskanci hukunci.”
Gwamnatin Jihar Filato ta yi Allah-wadai da harin.
Kwamishiniyar Yaɗa Labarai ta jihar, Joyce Ramnap, ta tabbatar wa jama’a cewa ana ɗaukar matakan kawo ƙarshen irin waɗannan hare-hare.
“Gwamnati ba za ta lamunci kashe rayukan ‘yan ƙasa ba. An umarci hukumomin tsaro da su kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da tabbatar da cewa sun fuskanci hukunci.”