LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, an tabbatar da sallamar Ari a matsayin Kwamishinan zaɓen jihar Adamawa bayan da Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da buƙatar sallamarsa da shugaban ƙasa ya yi, biyo bayan zarginsa da aka yi da karya ƙa’idojin aiki da shigo da shakku yayin gudanar da aikin zaɓe da ayyana sakamakon zaɓe ba daidai ba, lamarin da har ya kai an gurfanar da shi a kotu.

 

Ari ya nuna damuwarsa kan yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe suka shafa wa idanunsu toka suka ƙi hango hujjojinsa da ya gabatar na kura-kuran da aka tafka a lokacin zaɓen.

 

Hudu wanda ya ɗauki Alkur’ani mai girma yayin hirar, ya rantse da Allah cewa, matakin da ya ɗauka a yayin ayyana sakamakon zaɓen ya yi ne da zuciya ɗaya kan gaskiya da kuma bisa dokokin gudanar da zaɓe.

 

Ari ya kuma ce INEC da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ba su ba shi damar kare kansa da ji daga gareshi ba, kuma shaidunsa da suke nuna cewa, Binani ce ta yi nasara an yi watsi da su ba tare da zurfin tunani ko nazarta ba.

 

Ya ce, hatta korarsa da shugaban ƙasa ya yi an yi ne kawai domin ɓata masa kima da mutunci.

 

Kan zargin da aka masa na cewa ya karɓi cin hancin biliyan 2 a wajen ‘yan siyasa domin kare ko yin abun da zai zama alfanu ga Binani, Ari ya ƙaryata. Ya sanar da cewa yanzu haka yana tuntuɓar iyalansa kan ko zai nemi haƙƙi a kotu kan zargi marar tushe da aka masa na amsar na goro, tare da cewa, “Nijeriya ƙasarmu ce dukka, ya rage namu mu kare ƙasar ko mu lalata ta.”

 

Da ya ke bayani kan zamansa a ofis, ya ce, ya samu nasarar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisu ba tare da wani ce-ce-ku-ce ba.

 

Ya yi iƙirarin cewa batutuwan da suka taso lokacin zaɓen gwamnan jihar da ‘yan majalisun jiha a rumfunan zaɓe 69 su ne suka janyo rikici da har ya kai ga korarsa.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Brice Ologui Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Gaban Da Kashi 90.35% A Jiya Lahadi

Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda kuma ya jagoranci juyin mulkin da aka yiwa Ali Bongo tsahon shugaban kasar ya lashe zaben da aka gudanar a jiya Lahadi tsakanin yan takara 7 har da shi.

Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News” ya bayyana cewa Oligui dan shekara 50 a duniya, shi ne babban dogarin sojoji masu tsare fadar shugaban kasar Gaban, a lokacinda ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin da yan gidan Bogo suka yi na shekaru kimani 50 a kasar.

Labarin ya kara da cewa kashi 2/3 na mutanen Gabon wadanda yawansu bai fi miliyon 2.3 ba suna cikin talauci a cikin kasa wacce take da arziki mai yawa.

Brice zai jagoranci kasar na tsawon shekaru 7 masu zuwa kuma yana iya sake shi takarar shugabancin kasa karo na biyu.

Yan takara 6 ne suka tsaya tare da Brice amma mai binsa bai sami fiye da kashi  3 % na kuri’un da aka kada ba sannan yawan fitowar mutane masu zabe ya kai kashi 70.4% wanda ya nuna cewa an sami sauyi babban a cikin harkokin siyasar kasar ta Gabaon.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Ce Za’a Gudanar Da Zagaye Na Gaba Tsakaninta Da Amurka Ne A Birnin Roma Na Kasar Italiya
  • Brice Ologui Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Gaban Da Kashi 90.35% A Jiya Lahadi
  • Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya
  • Badaƙalar Miyagun Ƙwayoyi: Kotun Amurka ta ba da umarnin fitar da bayanai kan binciken Tinubu
  • Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
  • Tsohon kocin Super Eagles Christian Chukwu ya rasu
  • Sin Ta Yi Allah-wadai Da Karin Harajin Amurka Ta Kuma Jaddada Goyon Bayanta Ga Ka’idojin WTO 
  • Abubuwa Da Yawa Na Faruwa Ba Tare Da Sanin Tinubu Ba – Tsohon Ma’aikacin Aso Rock
  • Kashe-kashen Filato: Jami’an tsaro na sassauta wa masu laifi —Tsohon gwamnan soji
  • Atiku ya jagoranci manyan ’yan siyasa sun ziyarci Buhari