HausaTv:
2025-04-26@22:51:31 GMT

Kissoshin Rayuwa Imam Hassan (s) 12

Published: 9th, February 2025 GMT

12-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa Shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na shahid Aya. Murtadha muttahhari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen ,Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.

Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan (s) limami na 2 daga cikin limamai masu tsare daga iyalan gidan manzon All..(s) kuma dan Fitima(s) diyar manzon All..(s) na farko.

Kuma a cikin shirimmu da ya gabata mun yi maganar yadda manzon All..(s) bayan kwanaki kadan da komawa Madina sai All..ya umurceshi da ya ji makabartan Bakiyya, ya nema masu gafara, don haka a cikin dare ya kira daya daga cikin yentattun bayinsa wanda ake kira Abu Maubihah inda ya fada masa cewa an umurce ni in nemawwa mutanen makabartan bakiyya gafara daga wajen All ..T kuma ina son ka rakani.

A lokacinda suka isar makabartan sai ya fadawa Abu Maubihah kan cewa an bani zami na mubudan taskokin duniya har abada, sannan aljanna, ko kuma haduwa da All..,amma na zami haduwa da All..,

Daga karshe ya zami haduwa da All..T. Sannan bayan kwanaki kadan, sai fara rashin lafiyarsa ta karshe, a nane sai yayi tunanin yadda iko zai koma ga Aliyu dan Abitalib (a) bayansa da sauki. Sai ya tada rundunar Usama dan Zaidu, ta tara dukkan manya-manyan sahabbansa daga cikin muhajirun da ansar, ya dora Usama dan shekara 17 a kansu.

A ciki ya umurci shi da yaje kasar Ruma ta gabas inda aka kashe babansa, ya yi kafirai.

Ya nuna masa dukkan dabarbarun yaki. Sannan ya bashi tutar, sai Usama yake wani wuri a bayan madina wanda ake kira Jurf. Sai yace masa. Amma suka ki fitowa su same shi, wasu ma suka fara sukan shugabancin Usama dan Zaidu, a lokacinda labari ya zo masa wasu sunki fita, sannan suna sukan shugabancin Usama a nan ma sai ya sake fita ya kuma yi masu Magana ya sake jaddada cewa, usman a ya canacanci shugabanci, haka ma babansa kafin shi. Duk da cewa a lokacin ma sun ki amincewa da jagorancin bababansa.

Mun kawo fara kawo maku abinda zamu iya dauka a cikin wannan hadisin, na cewa dabarar da manzon All..(s) yayi na nisantar da masu kodayin Mulki a bayansa ba zai kai ga nasarab, sannan su ma sun fahinci haka, shi ya sa suka sabawa manzon All..(s). Bayan haka.

Mun ji cewa a cikin manya-manyan sahabban da ya Sanya a cikin rundunar Usama akwai, Abubakar, da Umar da Abu ubaida dan jarrah da Usman da sauransu.

Sanna yaki sanya su kan rundunar ne don kada, wani daga cikinsu ya yi amfani da wannan damar don biyar bukatuna sa na kaiwa da shugabanci a bayansa.

Don haka ya tushe masu hanya, sannan ya la’ani duk wanda ya ki tafiya da rundunar Usama.

Banda haka wata dubarar da manzon All..(s) ya yi na shugabantar da Usama dan Zaidu  kan wadannan manya-manyan sahabban, shi ne ya nuna masu cewa, shugabanci cancanta ne ba yawan shekaru ba. Kuma All..ya na bawa shugabanci ga wanda ya ga dama, kuma zai bashi ilmi da kuma karfin da yake bukata don cancantar shugabancin.

Don haka manzon All..(s) ya bar wannan duniyar, manya-manyan sahabban manzon All..(s) su na karkashin shugabancin Usama dan Zaidu wanda bai fi shekaru 17 a diniya ba.

Don haka me zai hana Aliyu dan Abitalib wanda ya Usama shekaru, wato dan shekara 30 a duniya a lokacin, zama khalifan manzon All..(s) a bayansa(s)?.

A wani hadisi manzon All..(s) ya na cewa: wanda ya gabatar da kansa a cikin musulmi al-hali ya san da cewa akwai wanda ya fi cancanta da aikin to hakika ya kha’inci All..da manzonsa dakuma muminai (s).

A wani hadisin, yana cewa: All..yana kudaitarwa, sosai kan, wajen zaben mafi korewar mutane,  wanda ya kasance mafi cancanta ga wani matsayi. Lalle su sanya maslahar al-umma ne abin lura wajen zaben wanda ya cancanta. Su kasance amintattu a cikin abinda suke karba daga hannun mutane. A cikin cikin kuma kudaden da suke kasewa don abubuwan ji dadin rayuwar mutane. Sannan su tafiyar da al-amuran mutanen a cikin adalci kadai.  

Wannan kada ya kasance da yawan shekaru, sai dai ya kasance tare da kwarewa da kuma sanin makamar aiki, da sanin abubuwan da mutane suke bukata.

Don haka manzon All..(s) a cikin shugabantar da Usama Dan Zaidu ya kakkabo wasu daga cikin wadanda suke takara da Amirulmuminina (a) kan shugabancin al-ummar musulmi.

Ya karya zukatansu, daga neman wannan mukamin, ya kuma kashe guiwarsu daga ynkuri don neman wannan matsayin. Ya nisantar da su nesa ba kusa ba daga wannan burin nasu. Sannan suma sun fahinci haka a wajen manzon All…(s) kan hakan.

Baku ga cewa, Umar yana cewa Usama! Manzon All.. zai yi wafati kana shugabana?  Basu gushe ba suna suna jan kafa, sun ci gaba da sabawa manzon All..(s) har sai da ya yi wafata. (s).

Wannan kadan Kenan na abinda za’a iya fahinta na shugabatar da Usama dan shekara kimani 17 kan shaihunan kurasihawa da kuma wasu shuwagabannin ansar wadanda suka kodayin shugabancin al-ummar musulmi bayan wafatin sa (s).

Har’ila yau wannan ya tabbatar mana akwai makirci babban da aka kulla don hana Imam Ali (s) zama a kan kujerar da shi kadai ya dace da ita bayan manzon All..(s).

Zazzabi ta yi tsanani ga manzon All..(s), a lokacin matansa suka kusa da shi, a duk sanda suka sa hannunsu a kansa suna jin zafin jikinsa.

Sun sanya ruwan sanyi kusa da shi, a duk sanna ya sa hannunsa cikinsa sai ya taba ruwan ya shafi kansa da hannunsa.

Sai mutane suna ta kai kawo suna bankwana da shi, sai da suka taru a gidan sai yana fada masu: Ya ku mutane, an kusa a dauki raina, daukewa mai sauki, a tafi da ni. Hakikin na gabatar da maganganu, don sauke uzuri da ke kaina a kanku. Sai dai lalle ni ina barin Littafin All..mai girma da daukaka da kuma zurriyata Ahlubaiti na.  Sai ya kana hannun Aliyu(a) ya daga ta. : Sai yace: Ga Aliyu nan tare da Alkur’ani , kuma kur’ani yana tare da Ali ba zasu rabu ba, har sai sun riskeni a tabki.

Abinda yakamata al-umma ta yi shi ne ta bi umurnin manzon All..ta bi abinda ya fada mata ta bi Amirulmuminina (s), ta mika mata shugabanci, don shi ne kawai zai tafiyar da al-amarinsu kan koyarwar Alkur’ani mai girma. Ya kuma yi hukunci da hukuncin All..

Ta ta yi haka kuwa da ta tsira daga dukkan tawaya, kuma fitinu ba zasu same ta ba haka ma dukkan hatsurra ba zasu sameta ba. Da kuwa musulunci zai taka matakansa kai tsaye tare da daukaka ya kuma sami iko da duniya gaba daya. Ya cika shi da adalci.

Har’ila yau kafin rasuwarsa manzon All..(s) ya daura rawaninsa, sai ya je masallaci ya hau mimbarinsa, sai yace masu, Lalle Ubangijina ya hukunta ya kuma rantse kan cewa ba zai yafe zulunci azzalumi ba, don haka ina hadaku da All…duk wani mutum wanda yake da wani abu da na yi masa sai ya tashi ya fada don yayi kisasi, a yi kisasa a gidan duniya yafi mani da kisasa a Lahira. A gaban mala’iku da annabawa…}.

Sai kowa ya kasa Magana, manzon All..(s) yana nuna masu kan cewa zalunci ko wace irice mutum ya warware shi a lduniya ya fi masa a yi masa adalci a lahira.

An dade ba wanda yayi Magana sai wani mutum daga karshen masallacin mai suna Sawadat dan Qais, sai yace ai manzon All..(s) ya taba dokansa cikinsa wani lokaci don haka yana son kisasi.

Sai manzon All..(s) yace masa ya zo . sannan ya aiki Bilala ya kawo bulala a gida, da ya kawo sai mutana suna gani me mutumin nan za iyi da manzon All..(s) a cikin wannan halin da yake na rashin rafiya.

Sai Sawada ya zo kusa yana karkarwa., saboda haibar manzon All.. sai y ace: Ya manzon All..ka kyaye mani cikink, sai ya ce ya manzon All..(s) kayi mani izini in Sanya bakina a kan cikinka, sai yace masa ee. Sai ya Sanya bakinsa a kan cikin manzon  All… idanunsa yana zubar da hawaye. Sai yana cewa  ina neman tsari daga wuta albarkan wurin kisashi daga manzon All..(s), a ranar lahira.

Sai manzon All..(s) ya ce masa, zaka yi kissasi ne ko kai yi afwa, ya swadatah sai y ace Afwa ya manzon All..(s). 

Sai manzon All..(s) yad aga hannayensa masu albarka yana uddu’a yana cewa: Ya Ubangiji ! ka gafartawa Sawadatah saboda afwan da yayi wa annabinka Muhammadu.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu . wassalamu Alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: manya manyan masu sauraro

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Kakaba Takunkumi Kan Kasarta Ya Sabawa Hikimar Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Ita

Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta bayyana cewa; Kakaba takunkumi kan kasarta ya sabawa ikirarin Amurka na yin shawarwari da ita

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane masu alaka da bangaren makamashi, man fetur da iskar gas da kuma wasu mutane da dama masu fafutuka a shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na lumana takunkumi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Baqa’i ya bayyana manufar takunkuman da Amurka ta kakabawa al’ummar Iran da cewa; A fili take nuna kyama ga masu yanke shawaran Amurka kan al’ummar Iran da kuma nuna rashin mutunta doka da hakkin dan Adam ne.

Ya kara da cewa: Dogaro da tsarin gwamnatocin Amurka da suka shude kan takunkumin tattalin arziki a kan kasashe masu tasowa, a matsayin makamin tsoratarwa da matsin lamba na siyasa, wani lamari ne da ya saba wa muhimman ka’idojin Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma dokokin kasa da kasa, kuma yana yin zagon kasa ga ginshikin doka da ka’idojin ciniki cikin ‘yanci, kuma yana haifar da keta hakkin bil’adama na asali na al’ummomin da takunkumin ya shafa, musamman ‘yancin ci gaba. Wannan hali sau da yawa yana zama laifi ga ɗan adam.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran ta Bayyana cewa: TattaunawarMuscat Wata Dama Ce Ta Samun Zaman Lafiya Kan Batutuwan Masu Sarkakiya
  • Gwamnan Babban Bankin Sin: Harajin Amurka Ya Jefa Kasuwanni Da Kasashe Masu Tasowa Cikin Hadari
  • Nazari Kan Amfanin Noman Kanumfari
  • Sayyid Fadhlullahi Ya Jaddada Muhimmanci Samar Da Makamai Ciki Har Da Kare Kasa Daga Dan Mamaya
  • Duniyarmu A Yau: Shiri Kasashen Yamma Na Kashe Dukkan Falasdinwa A Gaza
  • Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (4)
  • Ƙarin ’yan Najeriya za su fuskanci talauci nan da 2027 — Bankin Duniya
  • Jagora: Tafarkin Imaman Ahlul Bayti ( A.S) Na Gwgawarmaya Ne Da Jajurcewa
  • Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Kakaba Takunkumi Kan Kasarta Ya Sabawa Hikimar Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Ita
  • Ya isa haka: Tinubu ya umarci shugabannin tsaro su kawo ƙarshen kashe-kashe