HausaTv:
2025-03-26@08:51:00 GMT

Kissoshin Rayuwa Imam Alhassan(a) 13

Published: 9th, February 2025 GMT

13- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa Shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na shahid Aya. Murtadha muttahhari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen ,Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.

Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan (s) Jikan manzon All..(s) sannan limami na 2 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) kuma da na farko ga  Fitima(s) diyar manzon All..(s). a cikin shirimmu da ya gabata mun fara magana dangane da manzon All./.(s) ya farashi shiri don tabbatar da cewa iko ya koma da Aliyu dan Abitlaib (a) bayan wafatinsa, sai ya hada rundunar Usaman dainZaidu, wani yaro daga cikin sahabbansa(a) wanda ked an shehara 17 a duniya sannan ya sanya dukkan manya manyan sahabbansa wadanda suka suka hada da Abubakar da Umar da Usman da Abu ubaida dan jarra da wasu da dama cikin ansar, wadanda kuma ya fahinci cewa suna da kodayin shugabanci a bayansa, duk ya hadasu karkashin jagorancin Usama dan Zaidu.

Ya daura daura tut aba bawa Usama, ya ce masa ya je ya yaki kafirai a kasar da aka kashe babansa, wato zaidu dan Haritha. Sai Usama ya karbi tutan, sannan ya je wajen madina a wani wuri wanda ake kira jurf ya kafa sansanin sojojinsa, ya na jiran su fito amma suka ki fitowa, saboda suna sukar Jagorancin Usama dan Zaidu a kansu.

Amma sai manzon All..(s) sake fitowa duk da cewa yana cikin tsananin rashin lafiya, ya sake masu magana inda yace masu Usama dan Zaidu ya cancanci Khalifanci, haka ma babansa ya cancanci khalifanci, ammam sun soki jagoranci sa a lokacim ma.

Sannan ya la’ani wadanda suka ki zuwa tare da Usama dan Zaidu. Wannan dai shi  ne rundunar da manzon All..(s) ta karshen a rayuwarsa.

Kuma mun san yadda al-amarin ya kasance a lokacin. Don bayan sun ki tafiya sai suna zuwa gidansa suna son samun labarin mutuwarsa.

Don haka a ranar Alhamis ta karshe a rayuwarsa tun taru a gidansa, suna bankwana da shi sai yace masu ;Ku bani abin rubutu in rubuta masu abin idan kun yi riko da shi ba zaku bata bat aba har’abada.

Sai suka yi jayayya a tskaninsu wasu suna cewa a kawo wasu kuma suna newa kada a kawo don bai san abinda yake fad aba, a nan ne sai ransa ya baci, sai yace masu bai kamata ku yi jayayya a gaban annabi ba. Ku fita daga cikin daki na, sai suka fita. Ba tare da bata lokaci ba.

Wannan hadisin kamar yadda ya zo cikin Bukhari, ya zo da shi, , Ibn Abbass yana kiransa da “Musiban ranar Alhamis” musaibar ranar al-hamis wacce ta haka manzon All..(s) rubuta abinda idan mutane sun yi riko da shi ba zasu bat aba har abada, sai yayi kuka har ya jike gemansa.

Wannan yana cewa abinda zai rubutan yana da muhimmabci, kuma yana da dangantaka da makomar al-ummar musulmi. Sai kawai manzon All..(s) bai rubuta wannan abibda ba, amma ya fadi shi a wani wuri wanda ya fi dakinsa na wafati, wato kwanaki 70 kafin wafatinsa. Dan haka idan ya nanata shi a kan gadon wafatinsa, (s), karfafa abinda ya fada a duk tsawon lokacin aikinsa na hajji da kuma ranar Ghadir Kghom ne.

Sannan don sun san abinda zai rubutane ya sa suka ce masa, littafin All..ya ishemu, wato ba ruwansu da iyalan gidan manzon All… (s).

Daga nan kuma mu sawwara yadda diyarsa Zahra (s) ta ji a lokacin wafatinsa, tana kusa da shi kafin mutuwa da zo masa, sai tana cewa: Kai ton bakin cikina da bakin cikinka ya manzon All.(s)/ sai ya dube ta idanunta na ciki da hawaye, sai ya ce mata babu bakin ciki ga babakin da yau.

A lokacinda rashin lafiya ta yi tsanani ga manzon All.., sai hankalin Zahra (s) ya kara tashi, sai manzon All..(s) ya na son ya sawwaka mata bakin cikin da take ciki, sai ya ajiyeta a kusa da shi sai, ya asirta magana a gareta, sai ta yi kuka, sai ya sake asirta mata magana, sai ta yi murmushi, sai wannan al-amirin ya bawa A’isha ummul muminina, mamayi sai da ta fito daga wajensa, sai A’isha ta ce mata, nag a cewa a yau kin fi farinciki a kan bakin ciki, menene ya fada maki kika yi kuka sannan ya sake fada maki kiya yi murmushi,?.

Sai tace ba zan bayyana asirin manzon Al..(s). (wato idan da yana son ta ji, da ya daga muryarsa don kawa yaji, amma tunda ita kadai ya fadawa, a asiri ne, baya son kowa yaji sai ita Fatimah (s).

Amma ance bayan fatisansa (s) ta sake tambayarta, sai ta ce mata da farko ya ce, Malaki ya bijiromani al-kur’ani har sau biyu a wannan shekara, don bana gini fashe, mutuwata ta kusa, shi ne nai kuka, da ya sake magana ta biyu a asirce iata ma, sai yace mani,’ke ce na farko daga cikin iyalan gidana  wacce zata fara riskata. A nan sai na yi murmushi.

A wani hadisin yana ce mata, (ke ce na farko daga iyalan gidana, wanda zai hadu da ni, madallah da ni a matsayin magabaci, shin baki yarda ki kasance, shugaban matan Al-ummah ta ba….).

Bayan da Fatima (s) ta ji kan cewa mahaifinta ya kusan wafati, sai koma gida, ta je ta dauko yayanta Alhassan da Alhussain sai ta zo dasu wajen manzon All..(s). Tace masa… ya babana, ga wadannan yayanka biyu, ba gadarmasu wani abi daga (halayenka) wabi abu daga halayen. Manzon All…(s) ya gadar masu wani abu daga halayensa, sai ya ce mata: Amma Alhassan, na bashi haibata ta da jagorancinna, Amma Alhussain kuma na bashi jaruntata da kyautata.

Kamar yadda kuka gani ko wannensu ya gabar masa wani bangare na shifofinsa da kuma halayenta masu kyau.

An rawaito cewa Imam Hassan (s) halittar ta yi kama da manzon Al…(s) fiye da Imam Hussain, haka ma idan an ganshi, za’a ganshi ta haibar shuwagabanni irin ta annabawa da manzanni, haka ma Imam Hussain, jaruntance ta bayyana a ranar Karbala inda sojojin Yazidu la’anene ya kimani dubu 30 suka zagaya shi tare da magoya bayansa yan kadan, sun fuskancesu kuma suka yi shahada gaba dayansu.

An ruwaito cewa manzon All..(s) kafin rasuwarsa ya na da dinari  7, sai ya ji tsoron kada wafati ta zo masa suna tare da su, sai ya bada umurni a bada su sadaka kafin haka.

Amma sai suka shagaltu da shi har sai da ya farfado sai ya sake tamya danage da su. Ya ce masu: Me kukayi da kudadennan? Sai suka ce suna hannummu mun shagaltu da kaine, sai yace su kawo su, sai karba ya sa su a hannunsa, sai yace: Me Muhammadu zai tana a wajen Ubangijinsa ida ya same shi tare da wadannan.

Sai ya bada umurni aka rarrabasu cikin mabutaka.

Daga nan sai abinda malaman Ibn Abba ( r) yake kira musibar ranar Alhamis. Kafin haka All..T ya sanarda manzonsa (s) kan cewa, zai jarrabi al-ummarsa a bayansa, kuma musibu kamar daren duhu zasu fada masu, wanda kuma za iyi tsawo sai wadanda All..ya kubutar da shi daga wadannan musibu don yawansu da kuma tsawonsu.

Sannan yak arar tabbatar da  cewa iyalan gidansa zasu gamu da matsaloli a cikin al-ummarsa a bayansa.

Don haka bai bar yin kokari ba, don ganin ya kubuar da su daga musibun da suke gabansu.

A nan sai yayi tuna ya rubuta masu takarda wacce ba zasu taba bata ba har ba har abada idan suka yi riko da shi.

A wannan halin ne sai yace masu: Ku bani abin rubutu in don rubuta maku wani abu , wanda idan kun rike shi ba zaku taba bata ba har’abada: ana cikin wannan halin, wasu suna kokarin su gaggauta su kawo masu wasu suna cewa ku bari. Can sai wani daga can nesa ya ce masa. Lisfin All…ya ishemu. A nan sai ya sha mamakin yadda wani yake da jur’ar da zai fada masa haka, a cikin Jami’a don haka mutane da dama abin ya basu mamaki, ya kuma bayyana cewa akwai wani al-amari babba a bayansa (a).

Sannan fadin da yayi hasbuna kitaballahi, ya nuna cewa sun san abinza zai rubuta, sannan suka zabi abinda suke so daga cikin abubuwan da zai rubuta masu, sun ku a yi watsi da dayar.

Don haka Umar dankhaddabi ne ya fadi hakan. Kuma baa bin mamaki idan ya fadi hakan, don wanda ya karanta tarihin ya san rawar da ya taka wajen nisantar da iyalan gidan mazon All..daga shugabancin al-ummar musulmi a lokacin.

Banda haka, wato bayan Kalmar ‘littafin All..ya ishe’ sun ci gaba da jayayya a tsakaninsu a gaban manzon All..(s), sai matan manzon All..(s) wadanda suke bayan hijabi suke! “bakwajin abinda manzon All..(s) ya ke fada ? )  sai Umar yace:: Ku yi shiri, ku na nan kamar abokan Yusuf, idan ya yi lafiya ku zubar da hawaye idan kuma ya sami lafiya sai ku hau kan wuyarsa.).

Sai manzon All..(s). yace : Ku barsu sun fi ku alkhairi. Amma duk da haka an sami wasu wadanda suka tashi zasu aiwatar da umurnin manzon All..(s). sai wani daga cikinsu ya tashi yah ana shi, sai yace mata kada yayi (…don mutumin yana fadin abinda bai sani ba….) .

To daga nan kowa ya san cewa, masifa ta fada a kan al-ummar manzon All..(s), kuma musiba daga ta fi wannan musiya.

Dan Abbas( a), duk sanda ya karanta wannan labari sai ya yi kuka har hawayensa su jika gemunsa. Saboda bakin cikin abinda ya faru, saboda sabawa umurnin manzon All..(s).

Wannan halin ya samarda hayaniya a dakin da manzon All..(s) yake jinya. Sai yace mas uku tashi ku fita, bai kamata ku yi jayayya a gaban wani annabi ba. Sai kuma anan suka fita, sun kuma fahinci abinda yake fada. Ba kuma ranshin lafiya ya rinjayeshi kamar yadda suka fada a lokacinda yace su kawo masa littafin ya rabuta masu abinda ba zasu bata har abada ba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: ba har abada wadanda suka

এছাড়াও পড়ুন:

SDP: Ba Mu Yi Wa Kowa Alƙawarin Takarar Shugaban Ƙasa Ba

“SDP jam’iyya ce mai zaman kanta, kuma za mu ci gaba da bin tsarukanmu da dokokinmu wajen zaɓen ‘yan takara,” in ji shi.

“Za Mu Fi Mayar da Hankali Kan Ci Gaban Jama’a”

Shugaban jam’iyyar ya bayyana damuwa kan halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, musamman matsalar tsadar rayuwa da rashin tsaro.

Ya ce SDP ba za ta zama mafakar wasu ‘yan siyasa masu neman mulki ba tare da wani ingantaccen shiri ba.

“Dole mu duba halin da ƙasa ke ciki. Tsadar rayuwa na ci gaba da ƙaruwa, mutane na fama da wahala, amma ana cewa tattalin arziki yana inganta. Dole ne a fuskanci gaskiya, a yi aiki don ci gaban jama’a, ba kawai neman mulki ba,” in ji Gabam.

SDP Na Ci Gaba da Ƙarfafa Tsarukanta

Ya ce jam’iyyar na shirin fitar da manufofi masu amfani ga al’umma, inda za ta ba da dama ga matasa da mata wajen shiga siyasa da kuma samar da sabbin shugabanni masu nagarta.

Wannan furuci na shugabannin SDP na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin cewa wasu manyan ‘yan siyasa na shirin shiga jam’iyyar don samun damar takarar shugaban ƙasa.

Duk da haka, jam’iyyar ta bayyana cewa ba za ta sauya tsarinta domin kowanne mutum ba, kuma za ta bi ƙa’ida wajen fitar da ‘yan takara a zaɓen 2027.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Masu neman yi wa Natasha kiranye ba su cika ƙa’ida ba — INEC
  • Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe
  • Yansanda A Kasar Turkiyya Suna Ci Gaba Da Fafatawa Da Yan Adawa A Birnin Istambul
  • NUJ Ta Bada Tallafin Azumi Ga Iyalan Mambobinta Da Suka Rasu A Jihar Kebbi
  • SDP: Ba Mu Yi Wa Kowa Alƙawarin Takarar Shugaban Ƙasa Ba
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [17]
  •  Jam’iyyar “Turkish National Party” Ta Tsaid Imam Uglu A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa
  •  Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon Ya Yi Gargadi Akan Masu Tunanin Kulla Alakar Kasar Da HKI
  • Matasa sun kashe yaron da suka yi garkuwa da shi a Bauchi
  • Yadda garin Zip ya nutse a Kogin Binuwai