HausaTv:
2025-03-26@09:02:30 GMT

Kissoshin Rayuwa Imam Alhassan (a) 14

Published: 9th, February 2025 GMT

14– Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa Shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na shahid Aya. Murtadha muttahhari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen ,Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.

Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan (s) Jikan manzon All..(s) sannan limami na 2 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) kuma da na farko ga  Fitima(s) diyar manzon All..(s). A cikin shirimmu da ya gabata mun fara Magana dangane da wasu abubuwan masu muhimmanci wadanda suka faru kafin wafatin manzon All..(s), wadanda suka hada, kan cewa manzon All..(s) ya tada rundunar Usama dan Zaidu dan shekara 17 a duniya, zuwa yaki da rumawa ta gabas, amma manya manya manyan sahabban manzon all..(s) sun ki fita zuwa ga yakin, sun suki manzon All..(s) kan shugabantar da Usama a kansu. Ya fito ya sake kodaitar da su, kan su fita, amma sun ki fita.

Don haka, manzon All..(s) ya yi wani kokari na tabbatar da abinda ya fada masu a wurare da dama, kan cewa su rike Alkur’ani da kuma iyalan gidansa a bayansa sai suka, ya gamu da turjiya daga wasu daga cikin sahabbansa.

Abinda ya faru shi kamar yadda ya zo a hadisin ‘nusibar ranar Alhamis, wanda Ibn Abbas ya ruwato yana cewa: Manzon All..(s) ya ce a bashi abin rubutu don ya rubuta masu abinda idan sun rike ba zasu taba bata ba har’abada.

Bayan haka sai Umar ya ce: littafin All..ya icemu, kuma cuta ta rinjaye shi. Bayan haka, sai suka tada hayaniya, a gabansu, wasu su ce ako masa wasu kuma suke kada a kawo masu.

Wannan sai da ya kai ga, ya ce masu su tashi su fita, don bai kamata yin jayeyye a gaban annabi ba.

Wannan musibar ranar Alhamis ta girma a kan duk wanda ya hankalta a cikin musulmi. Saboda an hana musulmi kaiwa ga abinda zai kiyayesu daga bata har abada.

Duk da cewa ba wannan ne manzon All..(s) yake yin Magana dangane da iyalan gidansa ba. Mun karanta a baya, hadisai da dama dangane da haka. Ya yi masu Magana a kansa, a duk inda ya yi khuduba a tsakninsu, a aikin hajjin bankwana, sannan bayan aikin Hajji a Ghadir Khum, ya fadawa wasu dai-daiku ya kuma fadawa wasu da dama kan cewa zai bar masu aikur’ani mai girma,  da kuma iyalan gidana a bayansa. Wanda ya yi riko da su ba zai bata ba har ranar kiyama.

Don haka mafi yawan sahabban da suke madina sun ana wannan masayi yar, amma a dai-dai wafatin manzon All..(s) sai wata jama’a ta fito tana jayayya da shi, ya fada su fada a gabansa. Ya bada umurni sai suke ba’aza yi ba.

Daga nan ya sakankancewa kan abinda All..ya kadda zai jarrabi al-ummarsa a bayansa sai ya auku, babu makawa.

A rajiyatu yaumul Khamis, wadansa suka da wannan manufar ta kwace iko daga Aliyu dan Abitalib (a), sun manta da ayoyin All..da dama dangane da matsayin manzon All..(s).

{ Mutuminku bai bata ba bai kuma kaucewa hanya ba. Kuma baya Magana bisa son zuciyarsa, wahayi ne wai ake sauko mana} Annajmi , sun manta da inda All..T yake cewa:

{Lalle ne shi da gaske, maganar wani manzon  ne mai girma a wajen  Allah. Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al’arshi. Wanda ake yi wa biyayya  ne a can, amintacce. Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.}  Atakweet (ko Izashamsu kuwwirat)19-22 da sauransi.

A rannan sun manta da wadan nan ayoyi alkur’ani mai girma kamar ba’a yi sub a, wadanda suke nuna girman manzon All..a wajen All.. sannan a wajen muminai.

Rayuwar duniya tarude su, ta kuma sun bata daga hanyar gaskiya, tun lokacinda manzon All..(s) yana numfashi, jim kadan a dauke ransa.

A lokacinda kusantar manzon All..(s) ga All..ma daukakin sarki, sai ya aiko mala’ikam mutuwa ya sauko, don ya dauko ransa mai tsarki zuwa zuwa Aljanna makoma.

Sai mala’ila ya sauki ya kuma nemi izinin shiga wajen manzon All..(s). Sai Zahra (s) ta fada mashi cewa ai yasuma saboda tsananin rashin lafiya. Bayan wani lokaci ya sake neman izinin shiga. Sai manzon All..(s) ya farfado daga sumarsa, Sai ya fadawa diyarsa Fatimah(s). Kin sanshi? Sai Tace: Babu ya manzon All..(s).

Lalle shi ne, mai raya kaburbura, shi ne mai rusa gidaje, kuma mai raba taro. Sai kara nutuwarta ta zubar da hawaye, sai tana fada a hankali (Kaito na ga mutuwar cikamin annabawa ya musiba ta, ,,, don rabuwada mafi alkhairin tsarkakakku, kaiton asara na don yankewar wahyi daga sama..)

Sai manzon All..(s) ya ji tausayinta, sai ya ce mata: Kada ki yi kuka don kace wacce zata fara haduwa da ni daga cikin iyalan gidana…)

Sai manzon All..(s) ya yi izini wa mala’ikan mutuwaya shigi wajensa. A lokacinda ya tsaya a wajensa, sai yace masa:

(Ya manzon All..(s), Lalle All..ya aiko ne a wajenka, ya umurce ni,  in yi biyayya a gareka, a cikin duk abinda ka umurce ni, idan ka amince ni da daukan ranka, in dauka, idan kuma ka umurceni in barta zan barta,.. sai manzon All…(s) ya ce: Ka yi aiki ya kai mala’ikan mutuwa).. Sai yace: da wannan aka murce ni in yi biyayya a gareka.

A nan sai Mala’ika Jibrulu ya shigo, sai yace: All..Ahmad Lalle All..yana shaukin saukin haduwa da kai. A lokacinda wadanda suke cikin daki sun fahinci cewa manzon All..(s) zai bar duna a lokacin, sai bakinciki ya shigesu, damuwa ta kawo masu har wuya. 

Sai Imam Hassan da Hussain(a) suka shigo suka jefa kansu kan manzon All..(s) suna kuka suna kuma yin guzuri na karshe daga wajensa, sai amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (s) yana son sauke sai yace masu: Kabarsu su ji dadi da ni, inji dadi da su. Lalle zasu gamu da wahala a bayana… ).

Sai ya juya zuwa ga wadanda suke kewaye da shi yana cewa: Hakika ba bar littafin All..a tsakaninku, da zuriyyata Ahlubaiti na, wanda ya yi watsi da littafin All..kamar wanda yayi watsi da sunnata, wanda ya yi watsi da sunnata kamar wanda yayi watsi da zurriyata , lalle ba zasu rabu da juna ba har su hadu da ni a Rabkin alkhauthar.

Daga nan sai ya kira wasiyyinsa Amirulmuminina (a) sai ya ce masa. Ka Sanya kaina a kan kirginka, hakika al-amarin All..ya zo. Idan raina ya fita, ka kama ta ka shafa fuskanka da ita, sannan ka juya ni zuwa al-kibla, sannan ka kula da al-amari na, 

 Ka sance wanda yayi mani salla da farko, sannan kada ka gushe tare da ni har sai ka sanyani a cikin kabari na. ka nemi taimakon All..mai girma da daukaka.

Sai Amirulmuminina (a) y ariki kan manzon All..(s). ya Sanya shi a kan  kirginsa, sannan ya mike hannunsa na dama, …sai manzon All..(s) ya yi izini wa mala’ikan mutuwa ya dauki ruhinsa mai tsarki. Manzon All..(s) yana jin zafin mutuwa, da dandanonsa, sai ransa ya fita, sai Ali (a) ya shafi fuskansa da shi a lokancisa ta fisa.

Sai ya bada labarin wafatinsa ga wadanda suke cikin dakin, ya bayyana wafatinsa.

Hakika an nade tutocin adalci a duniya a cikin duniyar bakin ciki, haka ma fitillun kamala da kuma daukaka. Dan’adam bai taba yin rashi irin wannan ba, sannan bai taba rasa wata asara fiye da shi ba.

Musamman iyalan gidansa, Musamman Zahra (s), ta jefa kanta a kan gawarsa tana cewa: Kai ton babana, aljanna firdauci masaukinta, ..

Da haka labarin ya yadu a Madina, wasu suna kuka, wasu sun taru suna magana a mansa, wasu sun kidimeh ko sun dimauce a lokacinda suka ji labarin wafatinsa (a).

Sai wasu kuma suna kokarin kwaceiko daga hannun Aliyu dan Abitalib (a).

Dangane da wafatinsa(a), Mai Kanzul ummal ya karbo hadisi daga Aba ghadafan cewa ya tambayi Ibn Abbas kan cewa :Shin a lokacinda manzon All..(s) ya rasu kansa yana kan kirjin wa? Ya rasu kansa yana kan kirgin Aliyu,. Sai nace Urwatu dan Zubai yana cewa dagaA’isha manzon All..ya rasu kansa yana tsakayin kirjina da cinyata, sai yace: kana da hankali kuwa, wallahi ya yi wafati kansa yana kan kitjin Ali (a), kuma shi ne ya yi masa wanka. Ibnu maja ma ya kawo wannan hadisin.

Imam Ali (a) ya tashi ya fara aikin yi masa wanda da sauran ayyukan da ake wa mamaci. Da ya kammala sai yana cewa (kai mai tsarki ne a raye da kuma bayan mutuwarka). Ko kafin haka.

A lokacinda ya kammala sai ya ajiyeshi a kang ado, farkon wanda yayi masa sallah shi ne All..mai girma da daukaka. Sannan Jibirilu da mika’ila da Asrafil. Sannan sauran mala’iku. Kungiya kungiya, sannan Aliyu ne y afara masa sallah a kasa. Sanan sauran suran musulmi suna zuwa su yi masa salla. Sannan su yi masa kallo na karshe.

A wani hadisin an bayyana cewa bayan da Imam Ali(s) ya sanyashi, kang ado. Sai yace masu kada kowa ya gabaci daya a cikinku, don shi limami ne gareku a raye ko bayan wafatinsa.

Don haka mutane suna zuwa gungu-gungu suna masa salla a cikin dakin. Basu da limami, Imam Ali (a) yana tsaye a gefen Janaza yana cewa:

Assalamu Alaika ayyuhan nabiyyu wa rahmatullahi wa barakatuhu. Allahumma Innaa nashadu annahu Ballah, ma unzila ilaihi, kuma yayi nasiha ga al-ummarsa, yayi jihadi a tafrkinka, har sai da All..ya daukka addininsa, kalmarsa ta cika, Ya Ubangiji ka sanyamu daga cikin wadanda suke bin abinda a kasaukar gareshi. Ka kuma tabbatar da mu a bayansa. Kuma ka hadamu da shi, ). Sai mutane kuma suna fada amin. Amin.

Bayan sun kammala sallar farilla sai Aliyu (s) yana, ya fara hakkar kabari.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: masu sauraro wadanda suka wadanda suke yi watsi da

এছাড়াও পড়ুন:

 Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon Ya Yi Gargadi Akan Masu Tunanin Kulla Alakar Kasar Da HKI

Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Barri ya jaddada cewa; HKI tana kokarin jefa Lebanon cikin tarkon kulla alaka da ita, yana mai jaddada cewa; Ko kadan Lebanon ba ta kama wannan hanyar ba.

Nabih Barri ya bayyana yadda wasu rahotanni daban-daban suke Magana akan cewa Amurka tana kai gwauro da mari, domin ganin an bude alaka kai tsaye a tsakanin Lebanon da HKI.

Shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon ya ce, ko kadan kasar Lebanon ba ta tunanin kulla alaka da HKI.

Haka nan kuma ya yi ishara da tsagaita wutar yaki wacce a kodayaushe HKI take ketawa, yana mai tabbatar da cewa Hizbullah tana riko da ita, don haka ya yi kira ga Amurka da sauran bangarorin da suke a cikin tsagaita wutar da su yi matsin lamba ga HKI domin ta yi aiki da ita.

Bugu da kari Nabih Barri ya ce; Sojojin kasar ta Lebanon sun gama shiryawa domin shiga cikin kudancin tafkin Laitani, amma matsalar da ake fuskanta ita ce yadda Isra’ila take kin janyewa daga wasu yankuna a cikin Lebanon.

Nabih Barri ya kuma jaddada cewa; Kungiyar Hizbullah tana aiki da tsagaita wutar yakin, kuma ba ta keta ta ba ko kadan.

Shugaban Majalisar Dokokin kasar ta Lebanon ya kara da cewa; Duk da cewa HKI tana keta tsagaita wutar yaki, amma ko sau daya Hizbullah ba ta harba ko harsashi daya ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [18]
  • Kantoman Ribas Ya Naɗa Farfesa Lucky Worika A Matsayin Sakataren Gwamnati
  • Yansanda A Kasar Turkiyya Suna Ci Gaba Da Fafatawa Da Yan Adawa A Birnin Istambul
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [17]
  •  Jam’iyyar “Turkish National Party” Ta Tsaid Imam Uglu A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa
  •  Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon Ya Yi Gargadi Akan Masu Tunanin Kulla Alakar Kasar Da HKI
  •  Arakci: Babu Wanda Zai Yi Tunanin Kawo Wa Iran Hari
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [16]
  • Yadda garin Zip ya nutse a Kogin Binuwai
  • Ko Raunin ‘Yan Wasa Zai Rage Wa Barcelona Karsashi A Kakar Bana?