Kissoshin Rayuwa Imam Alhassan (a) 15
Published: 9th, February 2025 GMT
15-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa Shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na shahid Aya. Murtadha muttahhari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen, Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan (s) Jikan manzon All..(s) sannan limami na 2 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) kuma da na farko ga Fitima(s) diyar manzon All..(s). A cikin shirimmu da ya gabata mun yi magana dangane da yadda manzon All..(s) yayi wafati, ya bar wannan duniya, da kuma wasu abubuwan da suka faru kafin wafatinsa.
Daga cikin abubuwan da suka fari har da musibar ranar Alhamsi, da yadda wasu sahabban manzon All..(s) suka sabawa umurnin na a kawo masa takarda ya rubutawa masu wani abu idan sun rike shi ba zasu taba bat aba har abada. Amma wasu sahabban manzon All..(s) suka saba masa, suka ma maida masa martani da cewa ‘alkur’ani ya ishemu’ saboda dama sun san ba abinda zai rubuta fiye da wannan. Don ya sha fada masu kan cewa zai bar abubuwan biyu a cikinsu “littafin All..da iyalan gidansa. Sannan sun san cewa shugaban iyalan gidansa shi ne Aliyu dan Abitalib, (a). Su kuma ba a shirye suke su bi Aliyun dan Abitalib (a) dan shekara 30 a duniya ba, don su manya manyan sahabban wasu sun kai shekaru 60 a duniya.
Banda haka basa son Annabi (s) kuma cikamakin annabawa ya fito daga banu Hashin sannan shuwagabnnin musulmi ko Khalifofi gaba daya har duniya ta nade, su fito daga yayansa(a). Sannan sauran gidajen larabawa, musamman Banu Umayya ba su da kome cikin shugabancin. Wannan ya sa suka kuduri anniyar cewa ba zasu bar iyalan gidan manzon All..(s) su karbi shugabanci a bayansa manzon All..(s) ba.
Don haka bayan wafatinsa, kamar yadda manzon All..(s) ya umurci Aliyu dan Abitalib (a), ya kasance tare da shi har sai ya rufe shi a cikin kabarinsa. Sannan abinda Aliyu (a) yayi Kenan, shi ya yi masa wanka sannan shi fara yi sallah shi kadai sannan musulmi suka zo gungu-gungu suna shiga dakin suna masa(s) sallah. Maza da mata, manya da yara duk sun masa sallah(s).
Daga nan sai Imam Ali (a) tashi za isa shi a kabarinsa, sai mughira a gangan ya yada zubinsa a cikin kabarin, saim ce cewa Aliyu (a) zobe na, sai Imam Ali (a) ya umuci dansa Imam Alhassan ya shiga ya dauko masa zobensa. Sai Imam Hassan ya shiga ya dauko masa zobensa.
A nan mughira yana son Imam Ali (a) ya barshi ya shiga cikin kabarin manzon All..(s) don yayi alfakhari da shi a cikin sahabban manzon All..(s). Amma sai Imam (a) ya gane, manufarsa, sai yace wa dansa Imam Hassan (s) ya dauko mana. Don haka shi ne na karshe wanda ya kasance kusa da manzon All..(s).
Daga nan sai Imam Ali (a) ya sa shi a kabarinsa sannan ya zauna kusa da kabarin yana kuka yana kuma wasu addu’o’ii, yana nuna bakinciki da rabuwa da manzon All..(s).
Manzon All..(s) ya yi wafati ne yana dan shekara 63 a duniya, sannan Imam Hassan (a) yana dan shekara 7 a duniya. Don a wannan shekaru, ko yara wadanda ba tsarkakku ba ma, suna kuma fahintar al-amuran da suke faruwa a kewaye da su.
Don haka Imam Hassan (a) ya fahinci yadda manzon All..(s) ya umurci sahabbansa manya-manya su tafi yaki tare da jagorancin Usama dan zaidu amma suka ki, sannan ya ga yadda kakansa manzon All..(s) ya umurcesu su kawo masa, takarda ya rubuta masu abinda idan sun rike sub a zasu bata ba har’abada. Amma suka yi ta jayayya a tsakaninsu a gabansa, daga karshe suka ce masa ‘alkur’ani ya ishemu,
Don haka yana sane da wadannan gaba daya. Kuma zamu yi Magana a kansu a zamanin Khalifa na daya da khalifa na biyu. Don haka ya ga irin yadda suka yi makirci don haka mahaifinsa zama khalifa a bayan kakansa.
Bayan da ruhin manzon All..Ya koma aljanna fidausi, ta kuma rabu da musibin duniya, sai musibun suka fara fadawa al-ummarsa daga bayan daya, suna bin juna.
Mutansa sun fara sababi a tsakaninsu kan wanda zai shugabancesu, sun bar wanda All..da manzonsa suka zabammasu, don su ma su dandana shugabancin, duk cewa basu cancanci haka ba.
Daga ciki akwai Sa’adu dan Ubada ya tara mutanen Ansar a sakifa, yana son ayi masa bai’a a matsayin khalifan manzon All..(s). bayan labarinwafatinsa ya isa a gareshi.
A cikin wannan halin ne sai labari ya iski Abubakar da Umar da Abu ubaida dan Jarrah kan cewa Ansar suna taro don zaben khalifa, kuma shi ne Sa’ad dan Ubada, daga nan sai suka yi sauri suka kai kansu sakifa, inda suka shiga jayayya da Ansar kan cewa, kan cewa su muhajirun ne suka cancanta don manzon All..(s) daga cikinsu, bayan jayayya mai yawa daga ciki har da zage-zage sai Aka yiwa Abubakar dan Abukuhafah bai’ar ba zata.
Daga nan suka sai sa’adu wanda bai da lafiya a lokacin yana kwance ko a taronne, yayi fushi, ya ce a maida shi gida. Sai sauran kuma sun shiga gari suna fadawa duk wanda suka gamu da shi ka yi bai’a wannan shine khalifan manzon All..(s).
Abinda ya faru din nan yayi dai dai da inda All..yake fada a cikin alkur’ani mai girma. Inda yake cewa
{Muhammadu bai kasance ba, fa ce manzon, hakika manzanni sun shede gabaninsa, shin idan ya mutu ko aka kashe shi, zaku juya daga duga-duganku, to wanda ya juya kan duga-dugansa, bai cutar da All..da kome ba, kuma da sannu All..zai sakawa wadanda suka gode masa}.
Wace masifa ce ta fi wannan musibar, na kaucewa hanyar da manzon All..(s) ya bar al-ummarsa a kanta? Wace musiba ne tafi All…da manzonsa su fada maku wannan tafarkin ne zai kaiku ya kuma tabbatar da ku kan gaskiya har abada amma sai ku zabi wata daban? Musiba kam kada ta fi wannan.
Kuma wani Karin abin mamaki a cikin wannan al-amarin shi ne, sun yi haka ne a dai-dai lokacinda gawar manzon All..(s) mai tsarki tana nan ba’a yi mata wanka ba, ba’a kuma yi mata sallah ba. Kuma manzon All..(s) ya umurci Aliyu (a) kada ya gushe tare da shi bayan wafatinsa, sai ya sa shi a kabarinsa. Don haka a dai dai lokacinda mai hakkin ya shagalto da wani aiki mafi muhimmanci, sai suka dauki wannan damar suka kwace-iko daga hannunsa, kafin ya kammala aikin jana’izar manzon All..(s), sun gama kullawa kansu shugabanci.sabanin abinda manzon All..(s).
Wasu malaman Tarihi sun bayyana cewa Khalifa na farko Abubakar da Khalifa na biyu, Umar da wasu wadanda suke tare da su, sun shalatu na neman al-amuran shugabancin ya tabbata garesu, don haka basu sami damar sallar gawa mai tsarki na manzon All..(s).
Khuduba ta .
{…har saida All..ya dauki ran manzonsa (s), wasu mutane suka juya baya da duga-dukansu, } Khuduba ta 150.
Don haka dole zamu gudanar da bincike ko da kadan ne, saboda yana da nasaba a rayuwar Imam Alhassan (a) kai tsaye. Don kauda shugabanci daga iyalan gidan manzon All..(s) yana da mummunan tasirinsa ga al-ummar musulmi kai tsaye, ku yana da kuma nasaba da makomar duniyar gaba daya, wannan al-amarin ya sauta tarihin addinin musulunci. Da iyalan gidan manzon All..(s) su ne suka karbi jagoranci tun bayan wafatin manzon All..(s), da kuwa tarihin musulunci bai kasance bakin tarihi kamar yadda ya kasance a halin yanzu ba. Da kuwa addinin musulunci ya mamaye duniya tun da dadewa, da babu yake-yaken masu kona danye da busashe da suka faru a cikin wannan al-ummar. Da tarihin duniya bas hi ne tarihinta a yanzu ba.
Da limami na 12 bai shiga gaiba ba da, da…..abubuwa da dama basu kasance kamar yadda suka kasance ba.
Daga cikin munanan abubuwan da suka faru saboda kauda iko daga hannun iyalan gidan manzon All..(s) bayan wafatinsa, sun hada da kodayin da -Tulaka-makiya Islam, wadanda suka yaki manzon All..(s) na tsawon shekaru kimani 20, sai da ya sami nasara a kansu a shekara ta 8 bayan hijira sai sun ce mun mika wuya, amma amini bai shiga zukatansu ba.
A lokacinda manzon All.. ya kwace makka daga hannun Abusufayan, sai aka zo da Abusufyan a gaban manzon All..(s) sai ya ce masa lokaci bai yi na ka shaida babu abin bauta da gaskiya sai All..sai yace na shaida tunda ka sami nasara a kammu, sai yace masa shin lokaci bai yi ba, ka shaida ni Muhammad manzon All..ne, sai yace . a nan kam akwai wani abu a cikin zuciyata, sai aka ce ko ka shaida ko a sare wuyarka, sai yace na shaida. Da haka Abu Sufyan da mutanen makka suka musulunci, sannan ya tarasu a Kaaba bayan ya tsarkake shi daga gumakanta, sai yace masu me kuke tsammanin za iyi da ku sai suka ce, dan uwa dan danuwammu, sai yace : ta tafi ta sake ku.
Wadannan suka musulunta a wannan halin ne, bayan wafatin manzon All..sun sami iko har suka tilastawa Imam Alhassan jikan manzon All..mika masu Mulki saboda bai da mataimaka.
Daga nan kuma aka fara musiba babba, a kan al-ummar musulmi musamman Mabiya iyalan gidan manzon All..(s) har yau, shekara 1400 bayan hijira. An kashe na kashewa an daura na daurewa an nisantar da na nisantarwa.
Tulakaa sun sami Mulki, sun kuma yi mafi munin abinda mutum zai yiwa wani a kan iyalan gidan manzon All..(s). sun yiwa mabiyansu haka. Kuma har yanzu al-amarin na ci gaba har zuwa lokacinda All..ya zo da al-amarinsa.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: iyalan gidan manzon All wadanda suka masu sauraro
এছাড়াও পড়ুন:
Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [18]
1. Gibɗa a cikin Addini:
Wannan ya ƙunshi yin gasa a ibada kamar sallah, ko azumi, ko karatun Alƙur’ani, da sadaka, ko mutum ya so ya zama hamshaƙin mai kuɗi da zai rinƙa taimaka wa addini da bayin Allah. Ko kuma mutum ya nemi ya zama malami ko jagora a addini don ya koyar da mutane.
2. Gibɗa a cikin Duniya:
Wannan shi ne mutum ya so samun ilimi irin na wasu don ya amfanar da kansa da al’umma. Ko kuma son ya zama attajiri ko ɗan kasuwa ko mai wata sana’a da zai rinƙa ba wa mutane horo saboda ya ga wani yana yi shi ma ya so ya ƙware ya taimaka domin samun lada a wurin Allah. Haka nan son samun shugabanci mai kyau domin jagorantar al’umma bisa gaskiya.
Manzon Allah (SAW) ya nuna irin wannanhassadarba laifi ba ce, inda ya ce: “Babu hassada sai a cikin abubuwa biyu: mutumin da Allah Ya ba shi ilimi, sai ya yi aiki da shi yana koyar da mutane, da kuma mutumin da Allah Ya ba shi dukiya, sai ya kashe ta a cikin hanyar da ta dace.” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.
Bambanci Tsakanin Hassada da Gibɗa:
Idan mutum ya ga wani yana da ilimi, sannan ya so ya zama kamar shi ba tare da yana son ilimin wancan ya gushe ba, to wannan ita ce gibɗa. Idan kuma mutum yana jin haushin wani saboda Allah Ya ba shi wata ni’ima, yana kuma son ni’imar ta gushe daga gare shi, to wannan ita ce hassada wacce aka haramta.
Illon Mutum Ya Zama Maras Gibɗa:
Idan mutum bai da hali na gibɗa, to hakan zai haifar masa da:
• Rashin ƙwazo da son ci gaba a rayuwa.
• Rashin yin koyi da na-gari a al’umma.
• Watsi da neman ilimi da kwarewa a sana’a ko addini.
• Rashin gasa a ayyukan ibada, wanda zai iya sa mutum ya ja baya a addini.
Yadda Mutum Zai Zama Mai Gibɗa:
Idan mutjm yana son ya sami ta gari, to dole ne ya zamanto ya:
• Nemi arzƙi ta hanyar halal da nagartaccen ilimi mai amfani.
• Aiki tuƙuru don samun ci gaba, ba tare da cutar da wani ba.
• Yin addu’a don Allah Ya ba shi irin ni’ima da wasu ke da ita.
• Kauracewa hassada da kiyayya a zuciya.
Kallon wasu a matsayin abin koyi, ba makiya ba.
Allah Ya datar da mu. Amin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp