Aminiya:
2025-02-21@14:57:51 GMT

Gobara ta ƙone motoci da shaguna a wajen sayar da gas a Neja

Published: 9th, February 2025 GMT

Wata gobara da ta tashi a wajen sayar da gas a Sabon Wuse da ke Ƙaramar Hukumar Tafa a Jihar Neja, ta yi sanadin ƙonewar motoci da shaguna da kuma kayan abinci.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar lokacin da wata tanka ke sauke gas a wajen sayar da gas.

Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu Me ya sa ake musayar yawu tsakanin APC da PDP?

Wutar ta ɗauki sa’o’i tana ci kafin isowar jami’an kashe gobara.

Wani mazaunin garin, Abdul Sabon-Wusa, ya ce bindigar ta girgiza yankin, inda mutane suka firgita suka fito daga gidajensu domin neman mafaka.

Wutar ta kuma bazu zuwa wani gidan mai, inda ta ƙone shaguna da motoci da aka ajiye.

“Muna godiya ga Allah ba a rasa rai ba, kuma ba a samu wanda ya jikkata ba.

“Idan hakan ta faru da rana lokacin da mutane ke kasuwancinsu, da wani babban iftila’in ne zai faru,” in ji shi.

Ya ce hayaƙin gobarar ya tashi sama sosai har ana iya ganinsa daga sassa daban-daban na garin, wanda ke nuna yadda wutar ta yi ƙamari.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gobara Wajen Sayar Gas

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Edo ta tanadi hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane

A yunƙurin daƙile ta’adar garkuwa da mutane, Majalisar Dokokin Jihar Edo, ta amince da dokar zartar da hukuncin kisa kan duk wanda aka kama da laifin.

Majalisar ta amince da ƙudirin ne wanda ta yi wa bita daki-daki yayin zaman da ta gudanar a ranar Talata.

USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Charity Aiguobarueghian ne ya jagoranci gabatar da ƙudirin wanda shugaban marasa rinjaye, Henry Okaka ya goyi baya.

A baya dai Majalisar Dokokin Edo ta ayyana hukuncin ɗaurin rai da rai ga duk wanda aka tabbatar wa laifin garkuwa da mutane tare da ƙwace duk wani abu da mallaka a dalilin aikata ta’adar ta garkuwa da neman kuɗin fansa.

Sai dai a yanzu majalisar dokoki ta sahale a tsananta matakin da za a riƙa ɗauka zuwa hukuncin kisa haɗi da ƙwace duk abin da aka mallaka ta hanyar aikata laifin.

Tuni dai Kakakin Majalisar, Blessing Agbebaku ya umarci Magatakardan majalisar da ya miƙa wa Gwamna Godwin Obasake ƙudirin domin amincewa.

Kazalika, majalisar ta amince da ƙudirin yi wa dokokin hukumomin samar da wutar lantarkin jihar gyaran fuska.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda Za A Kare Yara Daga Barazanar Intanet
  • Malamai Suna Takara Da ’Yan Siyasa Wajen Neman Mulki –Sule Lamido
  • Shirin Rigakafin Cututtuka Na UNICEF/GAVI Ya Sami Cikakken Hadin Kan Gwamnatin Jihar Jigawa
  • Gobara ta ƙone gidaje, dabobbi da kayan abinci a Kano
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa; Yahudawan Sahayoniyya Sun Kasa Murkushe Gwagwarmaya
  • ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2, sun sace manoma 10 a Neja
  • Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno
  • Majalisar Edo ta tanadi hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane
  • Mutane Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Wani Abu A Kasuwar Zamfara
  • Tara Daga N100,000 Kan Amfani Da Mitar Wutar Lantarki Ta Ɓarauniyar Hanya – NERC