OIC Ta Yi Allawadai Da Furucin Shugaban Kasar Amurka Akan Gaza
Published: 9th, February 2025 GMT
Kungiyar kasashen musulmi ( OIC) ta fitar da bayani da aciki ta yi tir da maganganun shugaban kasar Amurka Donald Trump akan fitar da mutanen Gaza.
Kungiyar ta OIC ta bayyana cewa; maganganun na shugaban kasar Amurka suna a matsayin goyon bayan ‘yan mamaya, masu mulkin mallaka domin kwace kasar Falasdinawa da hakan yake a matsayin take dokokin kasa da kasa da kudurorin MDD da su ka hada da kwamitin tsaro na wannan Majalisar mai lamba;2334.
Haka nan kuma bayanin na kungiyar kasashen musulmin ya ce, abinda Trump ya furta zai iya hana zaman lafiya wanzuwa a cikin wannan yankin.
Wani sashe na kungiyar kasashen musulmin ya bayyana kin amincewa da duk wani yunkuri na sauya tsarin iyaka da mutane a Falasdinu, tare da yin kira da a tsagaita wutar yaki mai dorewa.
Haka nan kuma kungiyar ta OIC ta nuna cikakken goyon bayanta ga hukumar Agaji ta Falasdinawa ta “UNRWA” wacce Isra’ila da Amurka su ka haramtawa kansu aiki da ita.
Kungiyar ta kuma nuna cikakken goyon bayanta ga al’ummar Falasdinu da kuma fadi tashin da suke yi na samun ‘yanci a karkashin kungiyar PLO.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Wang Yi: Kasar Sin Na Da Kwarin Gwiwa Kan Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a jiya cewa, kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da kasashen Japan da Koriya ta Kudu, kuma tana da kwarin gwiwa kan hakan.
Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar taron firaministan kasar Japan Shigeru Ishiba a birnin Tokyo tare da ministocin harkokin wajen kasashen Japan da Koriya ta Kudu. Yana mai cewa, an fara hadin gwiwa tsakanin Sin da Japan da Koriya ta Kudu da wuri, inda aka samu sakamako da dama, kuma tana da babban tasiri, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta fahimtar juna da hadin gwiwar moriyar juna a tsakaninsu.
Wakilin Musamman Na Xi Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugabar Namibiya Fadin Yankin Da Ke Fama Da Zaizayar Kasa Na Kasar Sin Ya Ragu A 2024Kazalika, dangantakar Sin da Japan da Koriya ta Kudu tana kara bunkasa, za a kara tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Bugu da kari, hadin gwiwarsu na kara zurfafa, kasashen yankin za su kara kaimi wajen tunkarar kalubale daban daban daga waje.
Wang ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Japan da Koriya ta Kudu, wajen kafa sahihiyar ra’ayi game da tarihin yakin duniya na biyu, da kiyaye tsarin bangarori daban daban, da kiyaye muhimmiyar rawar da MDD ke takawa a tsarin kasa da kasa, da ci gaba da inganta hadin gwiwa, da ba da gudummawa ga samun zaman lafiya da wadata a shiyyar da duniya baki daya. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp